38

644 56 1
                                    

Zaune Jawahir take tana chatting da Najib a waya Sabreena ta shigo dakin, kallo daya tayiwa Jawahir ta dauke kai dan tasan da wanda ake chatting din, Najib ne kaɗai wanda Jawahir ke bata lokacinta ta zauna tana chatting dashi, bathroom Sabreena ta wuce tana kokarin hadiye kishin daya taso mata, alwallah tayi ta fito ta kalli Jawahir da se murmushi takeyi a zuciyarta tace "kome yake fada mata dake sata murmushi haka oho", shimfida sallaya tayi sannan tace "sister anfa kira sallah", Jawahir ta dago ta kalli Sabreena tareda mika mata waya tace "ungu nan yaya Najib ze miki magana", bata musa ba ta karba wayar tareda zama kan gado yayinda ita kuma Jawahir ta wuce bathroom.

Sallama ta mishi dan yasan itace sannan tace "Jawahir wai zakamin magana", shiru yayi yana kallon text din dan shi dai yasan bece a ba Sabreena waya ba, ganin shirun yayi yawa ta kuma type mishi "are you there", nan da nan ya mata reply da "Yes, dama na tambayi sister dinki abinda zan kawo muku idan zan dawo tace ita bata sani ba, shine nace bari na tambaye ki", shiru tayi tana kara karanta text din, wato ma Jawahir aka tambaya tinda batasan abinda zatace a kawo ba shine yace a bata wayar gata second option, takaici ne ya kamata sedai ta hadiye abinta sannan ta rubuta mishi "ka siyo duk abinda kaga ya dace, ni sallah zanyi yanzu", daga haka ta ajiye wayar ta tada sallarta dan har yanzu Jawahir bata fito ba, yana karanta abinda ta turomai yasan ranta ya ɓaci kuma he won't blame her, Jawahir ce da laifi ita da ta bata wayar ba tareda yace ta bata ba tinda idan yanason magana Sabreena ai yana da number dinta. Shima ajiye wayar yayi kan desk dinshi yana tunanin abinda ya dace yayi.

Jawahir na fitowa itama ta shimfida nata sallayar ta tafara sallar ta, bayan ta idar tayi addu'o'inta ta dawo ta zauna gefen Sabreena dake game a nata wayar fuskar ta ba annuri ko kadan dan kuwa ta fara gajiya da ganin yanda Najib yafi fifita Jawahir a kanta, a hankali Jawahir tace "sister meya ce miki?", ba tareda Sabreena ta kalleta ba tace "tambaya na yayi abinda ze siyo mana idan ya tashi dawowa", ganin yadda Sabreena tayi maganar cike da dacin rai yasa Jawahir cewa "kina jin haushi na koh?", da sauri Sabreena ta kalleta tace "sister saboda me zanji haushin ki?", "saboda ina son wanda kike so", cewar Jawahir tana kallon expression din Sabreena, gabadaya Sabreena rasa abin fada tayi dan batamasan me zata cewa Jawahir ba tinda ba karya tayi ba sedai ita kam batajin haushin ta, zata iya cewa tana jin kishi amma badai haushi ba, riko hannunta Jawahir tayi tace "don't worry it's ok to fall in love with him, after all bake kika sawa kanki soyayyar shi a zuciyar ki ba so I won't judge you, nima bani na sawa kaina ba sedai na girma da soyayyar Yaya Najib a raina, most of the time idan zezo nan gidan ina lura da yanda kike jin dadi, haka kuma idan yazo ina ganin yadda kike kallonshi", cikin sanyin murya Sabreena tace "how did you...", da sauri Jawahir ta katse ta da cewar "I'm not a fool to not notice, amma karki damu, duk da nasan inada mugun kishi bana kishin kasancewar ki da Najib wanda a kullum nakewa Allah godiya daya ciremin kishinki a raina dan in har ina kishin kasancewar ki da Najib bansan ina zansa raina ba", hawaye ne ya cika ma Sabreena ido tace "but he only loves you", Jawahir tayi murmushin karfin hali tace "waye yace miki haka, ke bakya ganin irin kallon da yake min shi yake miki?", girgiza kai Sabreena tayi dan ita kam bata taɓa lura ba Jawahir ta matse hannun Sabreena dake cikin nata sannan tace "sister inaso mu hada kai wurin ba yaya Najib farin ciki, nasan cewar sooner or later dole yace yanason daya daga cikinmu, what I want with you is duk wacce ya zaba dole dayar ta hakura tasawa zuciyarta dangana, idan har ke ya zaba toh kuwa ni zan hakura dashi", da sauri Sabreena ta girgiza kai tace "no, nikam bazanyi wannan sonkan ba, indai har zaki hakura toh nima na hakura yaje can ya nemi wata, ko kuma ya haɗamu mu biyun duka", dariya Jawahir tayi tana tashi daga zaunen da take tace "Sabreena do you think zanyi zaman kishi dake ne, that won't happen, koda zan zauna da kishiya ba zan zauna dake a matsayin kishiya ta ba", Sabreena na kallon tace "why", kai tsaye Jawahir tace "saboda inada kishi, ni kuma banason nayi kishi dake shiyasa kigaka ko yanzu ma ban damu ba", shiru Sabreena tayi dan ita dai al'amarin ya daure mata kai.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now