12

860 85 2
                                    

Cike da mamakin Jawahir Farida ta karasa aikinta, Jawahir kuwa koda Dada yaga ta fito tana gunguni yasan batayi abin arziki a kitchen din ba, girgiza kai yayi yaci gaba da kallon shi ba tareda yace komai ba, itama zama tayi tana ciro wayarta dake aljihun wandonta ta shiga Instagram tana duba feeds dinta.

Koda Farida ta gama jera komai tayi kan dinning sannan ta musu iso zuwa dinning din dan su karya, Jawahir kallon yanda Dadanta ke hira da Farida cike da raha kawai takeyi, se a lokacin ta fara tambayar kanta 'toh meyasa tun tasowar ta bata taba ganin yanama Mamah magana cikin sanyin murya haka ba, se fada koda yaushe?', kawar da tunanin tayi saboda batason abinda ze dinga tuna mata da Mamah.

Dada ne ya kalleta yace "my princess ya ba kya cin abincin?", daukon fork tayi ta soma ci tana cewa "ba komai, yanzu zanci", hada ido sukayi da Farida inda ta mata wani sly smile sannan ta maida hankalinta kan Dada sukaci gaba da hiransu, Jawahir ganin bazata jura tana zaune a wuri amma ace hankalin Dada na kan wata daban ba yasa ta mike tareda cewa "I'm full, zan shiga ciki na huta", basu hanata tafiya ba dan Dada yasan Jawahir ba gwanan cin abinci bace, barta dai da ci banza ci wofi amma bazata zauna taci abinci sosai me gina jiki ba.

Tana shigewa daki Farida ta kalli Dada sosai ta matsar da plate din abincinta gefe sannan tace "idan bazaka damu ba inaso na sallami masu aikin gidan nan", kallonta yayi da mamaki yace "meyasa?", ta kamo hannunsa tana murzawa a hankali tace "saboda idan ba haka nayi ba Jawahir bazata taba zama cikakkiyar mace ba, sedai ta saura a jerin muna mata dan kuwa I'm sorry to say amma Jawahir lacks a lot of things ta fannin kula da gida, a wannan zamanin ba ko wani namiji bane ze yarda ya zauna da macen da bata iya girki ba balle kula da muhalli, ni a ganina idan na sallame masu aiki se mu raba aikin ni da ita kaga a haka zata fara iya wa da kadan kadan harta saba".

Tunani ya shiga yi kuma yaga tabbas haka din shine daidai dan idan da masu aiki akace tayi wani abun ba lallai ne tayi ba dan zata dinga gani kaman ai da masu aiki me amfaninsu amma idan basa nan kila tayi consider tayi abinda aka satan, amma hakan baze taba yiwuwa ba harsai ya zaunar da ita Jawahir din sunyi magana sannan.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli Farida yace "gaskiya wannan shawarar taki shine daidai, kuma hakan zamuyi amma ki dan bata lokaci su gama exams dinsu tinda sun riga sun fara kuma next week zasu gama, kinga a lokacin tanada dama sosai tinda zasuyi hutu, inyaso masu aikin se'a sallamesu a matsayin an basu hutu kafin ita Jawahir din ta koma school, kinga kafin hutun ta ya kare ta koya wani abin ta fannin gyara gida dama girkin kanshi", murmushin samun nasara tayi tace "madallah, Allah ya mana jagora akan lamarin ta", da "ameen", ya amsa yanajin wani irin dadi a ranshi ganin yadda matar tashi ke kokarin ganin Jawahir ta zama 'ƴa itama kaman yadda sa'anninta suke a ko ina.

Sati daya kenan da Farida ta samu Dada ta mishi magana, yau Jawahir na dawowa daga last paper dinta taga alaman canji a gidan dan masu aikin da ke kula da gidan basa nan, gashi dakinta yadda ta tafi ta barshi haka tadawo ta tarar dashi ba abinda aka taba, pillow dinda ke kwance kasa ta dauke ta wurga kan gado sannan ta ajiye bag dinda ke hannunta ta fice tana kwalawa masu aikin kira amma taji shiru.

Dada dake kwance daki ya tashi ya fito inda itama Farida dake kitchen ta fito tana cewa "Jawahir lafiya kike kwala kira haka?", ba tareda ta mata wani kallon arziki ba tace "inasu Mariya, haka suka barmin daki ba gyara tsabar kazanta, yaushe muka fara wasa dasu da har zasu bar min daki tun safe ba'a gyara ba", kallonta kawai Farida keyi tana mamakin hali irin na Jawahir, wato ita damuwarta ya kasance duk abinda takeso tazo ta sameshi a haka, batasan wani abu waishi Uziri ba.

UWA TA GARI (EDITING)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt