10

829 89 2
                                    

Suna zaune sukaji horn alaman ya karaso, cikè da zumudi Sabreena ta fita tana jira mahaifinta ya gama parking, yana fitowa ta karasa tareda rungume shi cikeda tsananin jin dadi tana cewa "Abba na, i missed you soo much", murmushi yayi kafin ya bata fuska yace "Sabreena nan garin fah ba Libya bane da zaki tashi kibi mutum ba tareda kin san meshi ba, stop trusting people so easily, this is Nigeria".

Shiru tayi yayin da Mamah dake kallonsu tace "a mata afuwa, it's not her fault, gani nayi ta dade zaune a airport tana jiran ka kuma da alaman akwai gajiya tattare da ita shiyasa nace tazo gidana dan ta samu ta huta kafin ka gama meeting din", se'a lokacin ya kula da Mamah, kallon ta ya tsaya yi yana yaba kyawun halitta irin nata a ranshi.

Seda Sabreena ta tabo shi tareda cewa "Abba", sannan ya fito daga duniyar tunanin da ya fada yayi murmushi yana cewa "shikenan ba damuwa, an yafe mata", sannan ya juya ga Sabreena yace "but don't try that again, u got me worried", rike kunnuwanta tayi alaman ban hakuri sannan ya juya wurin Mamah yace "nagode sosai da kika nuna kulawarki akan ta, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, mu yanzu zamu wuce", "ba komai ai yiwa kaine", cewar Mamah dake wasa da gefen mayafinta.

Kallon Sabreena yayi tayi saurin cewa "let me get my luggage", sannan tayi ciki, shikuma ya maida hankalin shi kan Mamah yace "amma bansan sunan ba", murmushi tayi tace "sunana Hindu", yace "nice name, nikuma sunana Harun", gyada kai kawai Mamah tayi, Sabreena ta fito janye da akwatin ta sukasa a mota sannan ta juya ta kalli Mamah tace "it was nice meeting you, ɗan zaman nan da nayi dake naji dadi sosai, se nake gani kaman da mommy na nake", murmushi Mamah tayi tana kallon expression din Sabreena da alama she's missing her Mom, dafata tayi tace "it was nice meeting you also, kuma u are always welcome here, duk sanda kikeso zaki iya zuwa, I will be glad to have you here".

Gyada kai Sabreena tayi tana hugging din Mamah sannan tayi breaking hug ta ciro wayarta ta mikawa Mamah tace "I will need your contact number", ba musu Mamah tasa mata sukayi sallama suka shiga mota, Abba yaja Sabreena na dagawa Mamah hannu.

Seda taga wucewar su sannan ta koma ciki dan ta dauka abinda zata dauka ta koma office. A cikin mota Sabreena ta kalli mahaifinta tace "Abba the lady is nice koh?", yace "uhm, she's nice", Sabreena ta gyara zama tana cewa "I like her", kallon Sabreena yayi sannan ya maida kallonshi ga titi bece komai ba se tunanin da ya fada.

WACECE SABREENA?

Sabreena Harun 'ƴa daya tilo ga Alhaji Harun da matarshi Asiya, Alhaji Harun dan Nigeria ne a jihar Borno, asalin fulanin Borno ne wanda ya taso, yayi karatun secondary dinshi a nan Borno din, a lokacin da ya gama ne ya samu scholarship zuwa Libya inda ya karanci dentistry, be dawo ba seda ya hada masters dinshi sannan ya dawo gida Nigeria ya fara aikinshi a babban asibitin gomnati a matsayin likitan hakori.

A lokacin da yake karatu a Libya ya hadu da Asiya mahaifiyar Sabreena itama tana karatu a nan school dinda yake, yayi senior dinta da two years a school din, sakamakon tutorial da yake ma ita da kawayenta soyayya ya shiga tsakani, dan haka koda ya dawo gida Nigeria seya fadawa iyayenshi akaje nema mishi aurenta, basu wahala ba aka bashi dukda kuwa tana karatu haka aka yanke mata karatu sukayi aurensu ya kawo ta Nigeria a nan kano din.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now