44

667 65 1
                                    

NOT EDITED

Najib yana zuwa gida ya wuce dakinshi direct tareda rage kayan jikinshi ya shige bathroom ya sakarwa kanshi shower yana tunanin kalaman Jawahir, tabbas Jawahir ta haɗa mishi zafi dan baya tunani se iya zaban ta ya bar Sabreena, sannan baya tunanin ze iya zaban Sabreena ya bar Jawahir, bemaso yayi wannan tunanin dan kuwa bega ze iya hakura da daya daga cikinsu ba. Yana fitowa ya goge jikinshi tareda gyara gashin kanshi ya feshe jikinshi da turare yasa PJs dinshi ya kwanta kan gado tareda ciro waya ya bugawa Salim, ringing daya Salim ya dauka tareda cewa "mutumin ya akayi?", Najib ya sauke ajiyar zuciya yace "kana ina ne haka, yakeji surutu?", Salim yace "friend dina ya haɗawa girlfriend dinshi surprise birthday party", Najib na jin haka yace "shine se da daddare za'ayi?", Salim yace "dadina dakai akwai holy holy, anyways how far", Najib yasa hannu a gashin kanshi yana yamutsawa yace "Salim wallahi Jawahir ta haɗamin zafi, komai ya tafi normal hatta Sabreena ta amince even after knowing inason Jawahir, but case din Jawahir is different dan cewa tayi sedai in zaba ko ita ko Sabreena in ba haka ba ita ta hakura", Salim yace "toh kai yanzu me ka yanke?", Najib yace "ban yanke komai ba dan a gaskiya abinda Jawahir keso bame yiwuwa bane bazan iya zaba ba", Salim yayi shiru yana nazari kafin daga bisani yace "I think you should give her time, zata sauko nan gaba kadan", Najib ya girgiza kai kaman Salim na gabanshi yace "idan nace zanyi hakan zata kara nisanta kanta dani ne, gwara in dinga lallaɓa ta har Allah yasa tazo ta amince", Salim yace "shikenan bro Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi", Najib ya amsa da "amin" sannan sukayi sallama Najib ya ajiye wayar yana tunanin abinyi, ganin har dare ya raba bacci yaki zuwa yasa ya tashi ya dauro alwallah yazo yana nafila tareda neman zabin Allah cikin al'amuran shi, bashi ya samu bacci ba se gab da asuba wanda ko baccin awa daya beyi ba aka kira asalatu.



********************

Sabreena jin Jawahir shiru shiru bata shigo ba yasata zuwa Mamah dan tambayar ta inda Mamah tace mata tana visitors room dan haka taje tayi kwanciyar ta kawai, ranar cike da wasiwasi Sabreena tayi bacci dan se taga kaman ta musu shisshigi acikin rayuwarsu tinda ta tabbata da bata shigo rayuwarsu ba Najib baze ganta ba balle yace yanaso, inda wata zuciyar kuma ke ce mata ba komai ƙaddara ne, Allah ya ƙaddara seta shigo rayuwarsu din kuma se tayi soyayya da Najib shiyasa hakan ya faru, itama bangaren ta da kyar ta samu bacci ya dauke ta.

Washegari bayan Mamah ta idar da sallolin ta tayi laziminta ta gama seta mike ta wuce dakin da Jawahir ta kwana, knocking tayi inda Jawahir ta tambaya waye dan itama ta dade da tashi, jin Mamah ce ta tashi ta bude mata kofar tareda dawowa ta zauna kan gado tana jiran Mamah ta shigo, Mamah na shiga ta tura kofar ta rufe sannan taje ta zauna kusa da Jawahir tareda cewa "is something wrong with you, meyasa kika zabi kwana a nan?", Jawahir tace "ba komai Mamah", Mamah tayi murmushi tace "I don't believe you, kinsan cewar you can confide in me right", Jawahir ta kaɗa kai Mamah tace "then tell me, meke faruwa", cikin kwalla Jawahir ta kwashe yanda sukayi da Najib ta fada mata, riko hannun Jawahir Mamah  tayi sannan tace "Jawahir ai hada kishi da Sabreena ba wani abu bane, ba laifi bane, meyasa kikeso ki haramta halal, ku dukkanku ze iya auren ku, kuma inaso ki sani namiji mijin mace hudu ne, ko be auri Sabreena ba ze iya auro wata", da Jawahir tace "Mamah ni da zeyi haka ma da nafi kowa farin ciki dan wallahi gwara nayi kishi da wacce ban santa ba taba sanni ba da nayi kishi da wacce ta gama sanin komai nawa", gane inda Jawahir ta nufa yasa Mamah cewa "nidai bazan baki shawara kin kula Najib ba, inaso kuci gaba da mu'amalar ku yanda kukeyi ada sannan tsakaninki da Sabreena ma banaso komai ya canza kinji", Jawahir tace "karki damu Mamah, Sabreena batamin laifin komai ba, dan haka babu abinda se canja amma bazan miki alkawarin ci gaba da sakewa da Najib kamar da ba", murmushi Mamah tayi tace "har yau Jawahir kinanan da wannan stubbornness din da nasanki dashi", itama murmushin tayi sannan tace Mamah "pls inaso naje na karasa hutuna wurin Dada", da sauri Mamah tace "saboda Najib kikeso ki gudu, karki damu yau ze koma aiki dan haka base kin tafi ba", Jawahir tace "ba haka bane Mamah, kawai ina missing Dada ne, zan dawo ana saura sati mu koma school dan haka one week zanyi na dawo", Mamah bataso haka ba amma kuma bataso ta tauye wa 'yarta hakkin ta dan haka tace "shikenan, ki kula kinji", tace "I will Mamah, you are best", murmushi Mamah tayi ta ba Jawahir peck a goshi sannan ta fice daga dakin tanajin dadin yanda Jawahir ke nuna soyayya gareta yanzu ba kaman da ba da kwata kwata bata gaban Jawahir ɗin.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now