24

744 67 2
                                    

NOT EDITED

Kwata kwata Farida taki yarda ta hakura da lamarin Jawahir dan ko kadan bata son ganinta a kusa da ita, bata sha'awar mu'amala da ita dan haka bazata zauna ta nade hannu tana kallon Jawahir na abinda taga dama a wannan gidan ba, wannan dalilin yasa da yamma ganin Dada be dawo ba ta dauki waya ta haɗa conference call tsakaninta da Zulaika da Nafisa amma batasa Salma a ciki, duk wani abu da Baba ya fada mata shi ta maimaita musu sannan ta kara da cewar "nifa gaskiya bazan iya hakura ba dan wallahi yarinyar nan tana shiga gonata dayawa, wai kuji har kyautar mota ya mata dan kawai ta bukaci hakan wannan irin so yake mata, gaskiya so nake na kawar da ita daga ganinshi", Zulaika ce ta fara cewa "toh ke yanzu me kikeso muyi?", tace "ku nemamin mafita, Nafisa ina wannan malamin nan naki na Katsina?", Nafisa tace "yana nan", Farida tace "wurinshi zamuje", shiru Nafisa tayi na dan wani lokaci kafin tace "ogan naki ze barki ne?", Farida tace "dolenshi ma", Nafisa dake ganin karfin halin Farida tace "shikenan, duk sanda kika shirya ki bari na sani", da "toh" ta amsa musu sannan ta katse wayar tana cewa " 'yar iska, ba zaman dare ba, koh rubutu uwarki ke baki kikesha senasa kwana bakin titi yafi miki kwana gidan nan dan wallahi se kin gane bakida wayau tinda kince ke bakida kunya, fitsararra kawai".

********************

Washegari Monday tinda sassafe Jawahir ta tashi tayi wanka ta shirya ta fice daga gidan abinta dan a halin yanzu da Farida ke gidan bata cika son zama ba saboda gudun bacin rai, direct school dinsu ta nufa inda ta wuce hostel dinda Zahra tace mata take, kiranta tayi a waya dan ta fada mata room number dinta, ba wani sha wahalar ganewa ba saboda kasa take ba sama ba, su biyu ne a dakin Zahra na bunk din sama, kallon Jawahir Zahra tayi tace "yana ganki da sassafe bayan yau bana tunanin za'ayi wani lectures, kalla time ko 9 fah batayi ba", zama Jawahir tayi bayan ta gaida roommate din Zahra wacce ke shirin sannan tace "just felt like coming to school ne shi yasa,wannan karan you resumed early, kuma har kin samu roommate", Zahra tace "toh ba abinda nakeyi a gida, there's nothing fun to do, komai kayi idon mom da dade na kai shi yasa kawai na dawo, roommate kuma da kika gani tama rigani zuwa, dan nazo na tarar da ita", Jawahir ta ƙada kai sannan tace "nawa ne school fees dinmu wannan karon", fada mata Zahra tayi tareda duk wani details da take bukata har time table dinsu ta nuna mata wanda aka tura a class group yayinda ita kuma tayiwa Dada message ta watsapp harda kara riban da zata samu. Kwanciya tayi a bunk din Zahra tace "bacci nakeji", Zahra tace "yi baccinki, nima aiki zanyi dan ban gama settling ba, me zakici idan na gama" Jawahir na gyara kwanciya tace "duk abinda kika dafa", da haka Zahra ta barta tayi bacci ta cigaba da aikin gyara kayanta.

Koda Jawahir ta tashi Dada ya riga ya turo mata kudin dan yaga message din harda kari ya mata, tana gama cin abinci suka fita da Zahra zuwa cafe dan ta biya, an cika a cafe din dan haka suka nemi wuri daga gefe suka zauna suna hira duk da Jawahir ba wani maida hankali tayi kan hiran ba.


********************

Iya gajiya Sabreena ta gaji dan bata saba da wannan wahalar ba ga rana, yawo takeyi cikin school din ta rasa ma ta ina zata fara, seda ta fara zuwa admin block ta karbi admission letter dinta sannan ta fara registration, ganin process din ba sauki bane ta nemi wuri ta zauna bayan ta siya coke me sanyi da kore kishi, tayi dana sanin cewa Najib yayi zamanshi duk da ya nace seya rakota tace ya barshi, seda ta gama hutawa a lokacin har an kira sallah sannan ta tashi dan taje tayi sallah, da tambaya ta gane masallacin inda tayi alwallah a waje sannan ta shiga ciki, tana cikin sallah taji an zauna kusa da ita, sallame sallarta keda wuya Jawahir dake zaune gefe tace "kin idar?", juyowa Sabreena tayi tace "na idar", Jawahir tace "ara min hijabinki inyi sallah", kallon kayan jikin Jawahir Sabreena tayi, wando da top a jikinta se karamin veil data daura a kanta, cire hijabin dake jikinta tayi ta mikawa Jawahir wacce ta amsa tareda "Thank you" sannan ta mike ta tada nata sallan, koda ta idar bata wani tsaya dogon addu'a ba ta cire hijabin ta mikawa Sabreena tareda sake cewa "Thank you", sannan ta mike zata tafi Sabreena tayi saurin cewa "dan Allah ko zaki iya nuna department din Insurance", Jawahir "hanyar zanbi, muje", tafiya sukeyi Sabreena nata kallon Jawahir ganin kamannin ta da Mamah sosai, indai kasan Mamah kaga Jawahir kasan one way or the other sun hada wani abun da kamannin ya ɓaci harta tafiyansu da magana.

UWA TA GARI (EDITING)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin