49

703 58 0
                                    

A gaban gidansu Jarood tayi parking sannan ta fito ta kwankwasa gate din, ba jimawa aka bude mata ta shiga, a bakin kofa ta tsaya tana sallama mahaifiyar Jarood Hajiya Turai na zaune tana kallon news tace "waye? shigo", Jawahir ta karasa shiga ta tsugunna ta gaisheta tareda gaishe da Alhaji El Mu'az dake zaune kan wheelchair gefe daya ya zabga uban tagumi, cike da farin ciki tace "Jawahir kice kika zama haka, ai rabon dana ganki har na manta", Jawahir tayi dariya ta zauna kusa da ita tace "wallahi Hajiya karatu ne ya boye ni", tace "madallah Allah ya taimaka, nasan an kusa gamawa yanzu koh", tace "yanzu nake third year dina", Hajiya tace "da kin kare se aure", Jawahir tayi dariya tana rufe fuska.

Gaishe da Alhaji tayi ya amsa ta mishi ya jiki yace "da sauki", tareda dauke kai dan bayaso ana mishi ya jikin nan gani yake kaman kowa ya gama ganin weakness dinshi ba'a mishi kallon girman da ake mishi ada saboda yanzu bashi da komai, Hajiya Turai ce ta katse musu shirun da sukayi da cewa "bari na kira Jarood", tareda tashi ta shige ciki, bata dade ba suka dawo tareda Jarood dake kokarin sa riga dan yana jin Jawahir tazo ya tashi tareda rigarshi a hannu ya fito, a palor ya ganta yace "Jawahir hope all is well, naga bamu dade da rabuwa ba?", tace "nazo wurin ka", yace "ok, muje waje", ta mike tayiwa su Hajiya sallama gaba-daya sannan suka fice, a compound ta ciro cheque dinda Dada ya bata ta mika mishi ya amsa yana cewa "me wannan?", tace "bude ka gani", budewa yayi amma se ya kasa magana ganin cheque din 10million da suke nema ido rufe saboda kai Alhajin su kasar waje a mishi aiki, sedai baze iya amsar kudin daga hannun Jawahir ba dan wannan harkar karanta ce, maida mata cheque din yayi yace "I'm sorry bazan amsa ba", tace "Jarood why not, you need it", yace "You are right I need it amma bazan karbi makudan kudade haka daga wurin ki ba, don't worry zan samu koh a bank ne zanje na nema rance", tace "why bank bacin ga kudin nan a hannunka kaje ka karba, don't make this difficult, taimako nayi niyar yi karka ki karba please", yace "indai taimako na zakiyi toh ki ranta mun amma karki bani kyauta dan bazan karba ba, ki ranta min da kadan kadan zan biyaki har na gama", tace "ba matsala, you can pay back idan ka samu but for now have the money", ta mishi hakan ne dan ya karba bawai da gaske ranta mishin tayi ba ita kyauta ta bashi, da kyar ta samu ya karba ya mata godiya tareda alkawarin biyanta idan Allah ya bashi iko.



********************


Jarood ya nunawa iyayenshi kudin tareda fada musu yanda sukayi da Jawahir suka dinga sa mata albarka inda Alhaji da kanshi yace "yana dawowa kan kafafunshi ze biya ta kudin ta dan kuwa idan Allah ya bashi lafiya se ya maido duka abinda suka salwanta sakamakon fashin da aka musu danshi yafi zargin aiko su akayi, nan Jarood ya kira doctor dinsu wanda ze hadasu da me aikin ƙafan yace sun samu kudin, cikin sati daya sukayi duk wani abinda ya dace sukabi duk wani process daya dace subi jirgin su ya ɗaga daga nan gida Nigeria se Mexico dan nemawa Alhaji lafiya, (Allah yasa a dace).



*********************


Farida ce gaban malaminta tana cewa "malam ni na rasa abinda yasa aikin nan bayaci, kace zezo har yanzu bezo ba going to two months kenan ana abu daya gashi kudade na duk sun kare ba biyan bukata wai me kake ciki ne malam", Malam ya sauke ajiyar zuciya yace "bincike na ya nuna min aiki ne ya mishi yawa dan be dade da dawowa garin ba ma amma yanzu zan miki aikin da duk yawan aikinshi dole ya samu lokaci yazo gareki", tace "malam dan Allah ka taimaka, banso na gama idda bezo ya maida ni ba, gashi saura na wata daya da en kwanaki", yace "karki damu zezo", sannan ya janyo tray din gabanshi wanda kasa ne ciki yayi en rubuce rubucen shi yace "zamuyi sadaka, kuma Inshallah da anyi sadakar nan an gama aiki", tace "Allah dai yasa baza'a bukaci kudi dayawa dan duk kudade na sun kare", yayi wani makirin murmushi yace "wannan karon ba kudi ake bukata ba, aljani na yace maniyyi yake bukata", gabanta ya fadi tace "subhanallah, maniyyi kuma, ina nasan zan samo shi", ya kalleta yana lashe baki yace "abu me sauki, tarawa dake zanyi idan kika kawo se mu zuba maniyyin ki a wannan kwaryar shikenan an gama aiki", ta zuba mishi wata irin harara tace "meka dauke ni, kawura ko me, ina budurwa ma banyi zina ba se yanzu, duk iskanci na bana zina, kuma idan zanyi ma bazanyi da kazamin mutum irinka ba, duk ka jera Qur'anai a daki kaman wani na Allah ashe nan dan iska ne kai, tur da hali irin naka", ta mike zata wuce yace "ai dani dake ba banbanci idan na nemi na tara dake sai me, ba gwanda ni a kan ke da kike shige shigen malamai kina kauce hanyar Allah ba, yanzu kin zo kina wani tur da halina, ke ba'ayi tur da halinki ba kinayi da na wani", batada abinda zatace mishi dan gani take kaman tsayawa mishi magana bata lokaci ne, dan haka taja tsaki tayi ficewar ta tana Allah wadar da masu hali irin nashi, se yanzu take dana sanin zuwa wurin shi da takeyi har take karanto mishi matsalolin ta tana gani kaman ze iya mata magani, ta manta cewar Allah ne wanda ya kamata ta koma gareshi ko al'amuran ta zasu warware.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now