26

669 78 5
                                    

Kaman yadda Farida tayi kudirin zuwa Katsina seda taje, koda ta fadawa Dada zata bikin kawarta Katsina be hanata ba harda bata gudunmawa takai, ita da Nafisa da Zulaika suka dau hanyar Katsina, sun samu ganin malamin da sukaje nema sedai ba biyan bukata dan shima cewa yayi ta hakura saboda Jawahir bazata bata saukar da kai ba kaman yadda Farida keso, Farida taji haushin wannan maganar dan haka ta bukaci a illata rayuwar ta indai wannan baze gagara ba, murmushi malamin yayi yace baze gagara ba dan already rayuwarta ma na kan hanyar bata so ta kwantar da hankalinta, wani garin magani ya bata yace ta zubawa Jawahir a abinsha indai har tasha toh an gama magana, duk da batasamu biyan bukata yadda takeso ba wannan dinma ya faranta mata rai, haka suka dawo gida inda Farida ke neman aikata kudirin ta na Allah wadar (Allah ka kiyashemu mugun hali).

*********************

Washegari da misalin karfe daya Jawahir ta shirya cikin riga da wando sannan ta dauko hijabin Islamiyyanta ta daura akai ta fice, bata dauki mota ba dan tasan cewar Najib zezo daukanta, koda ta taje Islamiyya Khadijah ta riga tazo nan suka zauna suna muraji'an karatun da aka musu last week har malaminsu ya shigo, bayan sun gama tilawa aka kara musu yace su dauko hadisin su yau hadisi zasuyi, Jawahir ta nutsu kasancewar tanason hadisi sosai, malamin ya fara da cewa "عن بهز بن حكيم عن أبيه عن جده ( معاوية بن حيدة )رضي الله عنه قلت : يا رسول الله من أَبَرُّ ؟ قال : ( أمك) قلت من أبر؟ قال : ( أمك ) قلت من أبر؟ قال : ( أمك ) قلت من أبر ؟ قال : (أباك ثم الأقرب فالأقرب )

Wato an karbo daga Bahaza dan Hakeem daga babanshi daga kuma kakanshi (ma'awiya bin hayda) Allah ya kara musu yarda yace : Ya Rasulullah wanene yafi cancanta ayima biyayya? se yace (mahaifiyarka), na sake tambayarshi na biyu wanene yafi cancanta ayima biyayya? se yace (mahaifiyarka), na uku na tambayeshi waye kuma yafi cancanta ayima biyayya? yace (mahaifiyarka), se na sake tambayarshi na hudu se yace (mahaifinka sannan wanda yafi kusada kai wanda yafi kusada kai). Wato seda yace ayima mahaifiya biyayya sau uku sannan yace mahaifi se kuma wanda yafi kusa da kai wanda yafi kusa da kai.

Wannan hadisi yana nuna mana cewar komai zakayi mahaifiya itace farko, kuyi mata biyayya, kubi maganar ta, saboda mahaifiya ba abin wasa bace, bari na baku wani tarihi, cewar malam "
Wani bawan Allah ne ya rasu akaje jana'izar shi kasa taki karbar shi, se akaje wurin Annabi Muhammad SAW akace "ya manzon Allah, ga wani bawa nan ya rasu amma kasa taki karbar shi", se manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace, "aje a samu iyalanshi aji ko yana aikata wani abu", se akaje aka samu iyalanshi amma sukace babu wani abu da yake aikatawa, se manzon Allah ya tambaya "shin mahaifiyar shi nada rai?", akace "eh Ya manzon Allah", yace "toh aje a tambayi mahaifiyarshi ko wani laifi ya taba mata", da aka tambayi mahaifiyarshi se tace ita babu abinda ya mata, se manzon Allah yace "a'a ta dai yi tunani babu abinda yake mata da har ranta kedan sosuwa", se tace "babu abinda yake min, amma tabbas akwai abinda yakeyi wanda yakesa raina sosuwa duk da ni bawai na daukeshi laifi bane amma idan yayi nakan ji ba dadi a raina, se raina ya sosu", se aka tambaye ta wani abu kenan, se tace "wato danta ya kasance idan ze siya abu, allal misali ze siya atampha toh se ya siyo guda biyu, ita daya matarshi daya amma fa na matarshi yanafin nata tsada, toh wannan abin yana sosa mata rai duk da bata taba furta mishi ba", se manzon Allah yace "toh idan ba kin yafe mishi wannan laifin ba kasa bazata taba karbar shi ba", shiru duka ajin sukayi suna jimamin wannan tarihi malam yacigaba da cewa " ga wani tarihi kuma na wani bawan Allah da mahaifiyarshi", " Wani bawan Allah ne yaje wurin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama goye da mahaifiyarshi a baya, se yace "ya manzon Allah, ga mahaifiyata, ta tsufa nike mata wanka, in bata abinci, in bata ruwa sannan in goyata inje duk inda zani da ita, shin ya manzon Allah na biyata? Se manzon Allah yace "nishi daya da tayi wurin haihuwarka baka biya ba tukuna".   "Dan haka nakeso ku kiyaye, iyaye mata ba abinda za'a dinga wasa dasu bane koh wulakanta wa ba", shirun da aji yayi ne yasa kowa kejin shesshekar da Jawahir keyi a inda take zaune, dago kai malamin yayi ya kalli inda Jawahir ke zaune yace "Jawahir lafiya kike kuka", girgiza kai tayi alaman ba komai, lura yayi cewar ba magana zatayi ba, dan haka yace "da akwai me tambaya?", duk aji sukace 'babu" yace "shikenan aje ayi sallah a dawo", mikewa duk sukayi suka fice banda Jawahir da ta kasa tashi daga inda take zaune.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now