RB -02

7.9K 802 40
                                    

   Bayan mun yi sallah isha'i Inna take labarta min irin dukan da ka yi ma Noor a makarantar islamiya yau saboda rashin biyan kuɗin sati biyar.

“Momy duba nan bulala ya kwanta min”

Ya faɗa yana nuna min hannunsa fafaren idanuwansa na cika da hawaye. Abun ka da farin mutun bulalar ta masa ja sosai kwanci jini ya kwanta a hannunsa. Hannunsa na kama ina murmushi.

“Ai lada kuke samu idan aka dake ku”

“Ni ba zan sake zuwa ba, Malam Usman azzalumi ne”

Ya faɗa yana taɓe pink lips ɗinsa. Sai na yi saurin rufe masa baki.

“Ba a zagin malami Noor kar na sake ji”

Habiba ta bige min hannu.

“Wallahi bar shi ya faɗa in ba zalumci ba miye na dukan ƙaramin yaro kamar Noor, ai dai yasan babu kuɗin ne da yanzu an bada, ji yadda ya bugar masa fatar hannu har ta yi ja, yaro ba a saba dukansa gida ba haka kawai wani ƙato zai dake shi”

Taja hannunsa suka fita waje ta shimfiɗa tsohuwar tabarma suka zauna, ni kan murmushi ne nawa, masifa ai Habiba ta iya ta har ta gaji musamman akan Noor duk wanda ya taɓa zai ga babu kyau.

Baba be shigo gida ba sai goma har da kwata a lokacin har Inna ta soma bachi, balle kuma Jamila da Sakina ba mota, daman su da anyi sallah isha'i suke bachi. Ni da Habiba ne kawai ba mu yi bachi ba, sai Noor da ke faman ƙirga taurariya, ina daga cikin ɗaki Baba yayi sallama, Habiba da Noor da ke waje suka amsa masa.
  Motsin rufe ƙofar gida da Baba ke ƙoƙarin ne ya tashi Inna daga ɗan guntun bachi da ta fara.

“Malam ka dawo?”

Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, shi kuma ya amsa mata fuskarsa da damuwa sosai.

“Na dawo amman ban samo komai ba”

“Ciyaman ɗin be dawo ba ne?”

Inna ta sake tambaya.

“Ya dawo amman be fito ba kuma be ce mu shigo ba, sai kawai aka rufe gate”

Kai na girgira kana ka ce

“Ai ba zaku samu ba, zai ce kullum kuna zuwa kuma masa maula a ƙofar gida, wata rana wulaƙancin ma sai ya fi haka, ni Wallahi Baba da ma zaka ji shawarata da ka daina zuwa gidan kowa roƙo yana zubar da mutunci da ƙimar mutum take”

“Zuwan ne ai ya zame mana dole tun ba babu wata sana'ar yi mai ƙarfi, tsaran icce ne ba kullum ake samu ba, jarin kuma mun cinye rayuwa ta yi tsada yanzu, dole sai mun haɗa da haka indai kana gida babu wanda zai ɗauko ya aiko maka. Ga ɗari na ranto gurin Malam Sahabi, da safe a karya”

Ya ciro naira ɗari a aljihunsa ya miƙawa Inna. Baba yana da gaskiya ba ko wane mai kuɗi bane mai zuciyar tausayi da taimako mafi yawansu kansu suka sani.

Unƙurawa na yi na tashi, na nufi ɗakinmu da muke kwana a ciki. Ganin haka yasa Habiba ta shigo da Noor sai ta koma ɗakinsu Inna ta taso da su Jamila da Sakina.

WASHE GARI...

Bayan na yi sallah asuba na zauna ina askar na safe da na saba yi a duk lokacin da na gama Sallah. Misalin ƙarfe bakwai da rabi Jamila taje ta siyo mana koko na naira ɗari, aka rarraba haka nan aka sha gayarsa ba tare da suga ba muka sha. A lokacin ne Sakina ta yi ma Noor shirin makaranta, ta kama hannunsa shi da Jamila tana cewa sai sun dawo. Har ya tafi sai ya sance hannunsa daga na Sakina yazo a guje yayi min kiss a goshi, sannan yayi min bye-bye yana dariya suka fice. Ban san inda ya samo wannan dabi'ar ba, ni dai nasan ban taɓa masa sumba idan zai je makaranta ba, ban kuma saba masa idan zai fita ba, amman shi yana yawan min a duk lokacin da zaije Makaranta.

Sallama muka ji ni da Habiba dake saka wandon makaranta.

“Daga ji Malam Hamisu ne, yabi ya takura mana akan kuɗin haya da be taka kara ya karya ba, baƙin Azzalumin banza mugu mtsss”

Ta ƙarasa tana jan tsaki. Na tada kai na kalleta.

“Kowa a gurin ki Azzalumi Habiba, ina laifin mutumen yana ɗaga mana ƙafa dai-dai gwargwado ke kin san da wani gurin ne da yanzu an koremu, amman kowa ki riƙa kiransa da Azzalumin hakan be dace ba sam”

Kamar jira take sai tayi cikina da faɗa.

“Kowa Azzalumine Nawwara na faɗa, waya kula da halin da muke ciki har ya damu kowa dai kansa ya sani, na faɗa kowa na duniyar nan Azzalumi ne”

Tana kaiwa nan ta saka farin hijabinta ta ɗauki jakarta ta fice ina mata Allah ya shirya.
Bayan ta fita na tashi ya leƙa ɗakin Inna dan yi mata ina kwana.

“Lafiya ƙalau Nawwara Allah yasa dai kin sha kokon dan nasan halin fa”

“Na sha Inna, har sai da na raga”

Na faɗa ina dariya, sai ga Baba ya shigo.

“Baba ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Nawwara an tashi lafiya”

“Lafiya ƙalau, ya lafiyar jikin”

“Alhamdullilah, Hamisu ne ya zo na ce yayi haƙuri har zuwa satin sama, sai dai ya ce daga wannan ba zai ƙara ɗaga mana ƙafa ba”

Ya faɗa yana zama kusa da tsohon rediyonsa.

“Allah gamu gareka, ka iya mana”

Cewar Inna tana sauke ajiyar zuciya. Ni kuma na miƙe tsaye ina faɗin

“Bari naje na shirya na koma can na gani dan jiya sun ce min na dawo da safe”

Baba ya ce.

“Sun ce zaki samu aikin ne?”

“Inshallah zan samu, saboda gurin Babansu naje kuma yana da mutuncin sosai”

“Wai aikin me ne?”

Inna ta tambaya tana daga kwance.

“Sharar ti'ti ne kuma kullum ake biya”

Ta yi saurin tashi zaune.

“Wane irin sharar ti-ti kuma Nawwara? Wannan sam ba mutuncin ki ba ne, Wallahi zaginki za a fara daman sun saba”

“Dukan masu zaginmu Inna babu wanda ya taɓa ɗauko Naira ɗari ya bamu ya ce mu siye wani abu, kuma na muku alƙawarin kare mutuncinna, Hijab zan saka idan har na samu aikin nan”

“Ba irin wannan aikin ya dace da ke ba Nawwara, ni nafi kowa dacewa da na yi shi”

“Baba ka san kana da Asma ba zai yiyu ka yi irin wannan aikin ba, kuma na maka alƙawari da zarar ka samu wani aikin zan daina wannan”

Ya girgiza min.

“Ba zaki yi ba Nawwara, sai dai ba zan hana ki bincikar wani aikin na daban ba, shi ma kuma kamin na samu wani abun yi”

Na ɗaga masa kai cike da ladabi.

“Tau Baba zan koma Candy Restaurant ko Allah zai sa a dace, amman Baba dan Allah ban da turin baron nan da ka taɓa yi kasan yadda zuciyarka yake idan ka ɗauki abu mai nauyi, ni Wallahi bana son kana dakon nan”

Na faɗa kamar na yi kuka, dan har ga Allah nafi tsanar dako fiye da komai a duniyar nan. Baba yayi murmushi irin nasu na manya sannan ya ce

“Nawwara kenan, ni dai ina jan hankalinki kan tsare mutuncinki da kuma na mu gaba ɗaya, Nawwara ke rai biyu ce mai maka da rai dubu a gurin mu, dukan abunda zai zubar da mutuncin ɗan ki da ni Mahaifinki karki kuskura aikata shi, ki riƙa tuna ke uwace, kuma ɗiyar wani wacce idan kika yi abun assha za a zagi Ubanki, ɗan ki kuma ayi masa jawabi, ni dai na san irin tarbiyar da na baku Wallahi ko cikin maza dubu zaki shiga matuƙar baki watsar da tarbiyar gidan nan ba, nasan zaki fito lafiya.

Ni da kan ɗan ki rai biyu ne a gareki Nawwara, abu kaɗan kika aikata zai iya saka zuciyata ta buga, ɗan kuma zai tsanake ni ya riƙa nadamar da kika kasance uwarsa, saboda haka ki riƙe mutuncin ki, Allah ya muku albarka”

Ni da Inna muka amsa da Amin.
Haka yake min a duk lokacin da zan fita neman aiki ko wani abu makamancin wannan, waɗannan nasihohin suna tasiri a gareni matuƙa, sukan katangeni daga duk wani tayi da wasu suke min na siyar da mutuncina, ko kuma musanya mutuncina da takarɗun aiki.

Comment on every single line.

RAI BIYUWo Geschichten leben. Entdecke jetzt