RB-45

5.8K 745 141
                                    

MUSTAPHA POV.

Mustapha ya yi farincikin tararda Jibril da ya yi a dakin ko ba komai yasan Jibril ba zai jidadi ba, a farkon shigowarsa ya shigo da fargaba da kuma tunanin irin kallo da wulakancin da Nawwara zata masa, amman ganin Jibril ya sashi sakewa kamar daman can sun saba da Nawwara.
Murmushin fuskarsa ya fadada ya kunno kai cikin dakin tare da Jidda yana kallon Nawwara.

"Pretty ashe Babynmu babu lafiya, Wallahi ban sani ba sai jiya ya jikinsa"

Sai da Nawwara ta hadiye yawu sannan ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa.

"Da sauki"

Kana ta watsa ma Jidda harara. Kamar be san an hallici mutum a gurin ba haka ya bi ta kusa da Jibril ya karasa kusa da Noor ya dire ledodin da ke hannunsa.

"Cute Boy waya kade min kai"

Noor ya dade yana kallonsa kamin ya amsa masa bakinsa da nauyi.

"Nima ban san shi ba"

"Am sorry dear"

Ya fada yana zama kusa da shi tare da duba hannun sai kuma ya juyo ya kalli Nawwara.

"Pretty amman da sauki sosai ko?"

Nawwara kamar ba zata amsa shi sai dai ganin Jibril yasa ta karaso gurin tana fadin.

"Eh a hannu kawai ya kare"

"Wallahi ban sani ba sai dazun nan Jidda ke fada min"

Nawwara ta kalli Jidda sai Jidda ta dan zaro idon tana daga kafadarta.

"Ya matsa ne sai ya ganki kin san yadda yake damuwa"

"Sorry na zo ban fada miki ba"

"Ba komai"

Cewar Nawwara. Jibril ya rumtse ido ya sauke ajiyar zuciyar da ta mamaye masa kirji, sai ya juyo cikin facin rai ya ce.

"Ya kamata ku tafi yanzu, amman kai yaron nan i warning you karka sake shiga sabgar Nawwara ko ban fada maka ba"

Daga Nawwara har Mustapha da Jidda kallonsa suke.

"Waye wannan daman ka san shi ne?"

Jidda ta tambaya tana kallon Mustapha, sai Jibril ya yi cikinta kamar zai dake ta.

"Babu ruwanki a ciki"

Matsawa baya Jidda ta yi ganin yadda temper dinsa take, sai Mustapha ya taso daga inda yake zaune kusa da Noor yana murmushi ya karaso daf da Jibril ya soma gyara masa kwalar rigarsa.

"Ka kwantar da hankalinka Man, macece fa ba namiji ba kasan namijin da ya amsa sunansa namiji baya taba dukan mace, ko da yake kai ragon namiji ne, shiyasa kake duka kuma kake cin zarafin yarinyar nan marainiyar Allah, anya babu kai a cikin kashe mata mahaifi kuwa? Saboda na ga ka tsawwalla rayuwarsu ne da yawa ka siye gidansu... oops sorry na manta she's your ex...- "

Ya karashe maganar yana murmushi. Jibril ya daga hannu cike da hasala zai naushi bakinsa sai Mustapha ya rike hannunsa cikin zafin nama ya kai masa na shi naushin a baki har sai da Jibril ya yi baya baya ya rike bakin.

"1-1"

Mustapha ya fada yana murmushin keta. Sai Nawwara ta katsa musu tsawa.

"Miye haka? Ya zaku rika yin abu kamar kananan yara?"

Murmushi Jibril ya yi ya kallon Noor da duk tsoro ya gama mamayeshi ya ce

"Wasa ne fa kawai karki daga hankalinki, amman ki fada masa karya sake zuwa kusa da yaro na"

RAI BIYUWhere stories live. Discover now