RB-15

4.7K 577 72
                                    

Habiba ce kwance tsakar gida amai na gefenta da alama yanzu ta gama shi, domin Inna ta ɗauki makwashi da tsintsiya ta je ɗebo ƙasa. Da sauri na ƙarasa kusa da ita jikina a mace na dafata.

“Sannu Habiba mi ke damunki”

“Wallahi kaina ne ke ta ciwo ban ma iya dawowa daga makaranta ba sai da malaminmu ya kawo ni, sai faman aman na ke, kuma bakina babu daɗi”

Samun kaina na yi da kuka marar sauti, hawaye na bin fuskata kamar babu gobe. Na samu kaina cikin wani irin tashin hankali wanda ban taɓa samun kaina a ciki ba.

“Ai zata samu sauƙi ina jin malaria ce bata sake ta ba”

Inna ta faɗa ganin ina kuka, sai faman rufe aman take.

“Allah yasa malaria ce, Allah yasa ta tabbata malaria ce ba ciki ba”

Maganar ta fito daga bakina kamar antseni. Hakan yasa Inna ta kalleni

“Nawwara, akwai abunda ya kamata na sani ne?”

Na yi saurin girgiza mata kaina hankalina a tashe.

“Babu babu komai”

Ta saki tsintsiyar hannunta, ta kalli Habiba da ta soma kuka daga inda take kwance.

“Akwai abunda kuke ɓoyewa ne?”

Na girgiza mata kai alamar a'a. Amman bata yarda ba. Ta soma ƙirga da hannunta.

“Tsaya dakata, Habiba tana da ciki kenan?”

Habiba ta yi saurin tashi zaune ta matsa gefena kamar zata shige jikina tana girgiwa Inna kai.

“A'a Inna”

Ta faɗa cikin kuka, kamar yadda nima na ke kuka. Sai ina ta kalleta idonta cike da hawaye ta nunata da yatsa.

“Kina da ciki Habiba, na lura da haka domin yanayinki ya canja gaba ɗaya, amman saboda karna munana zato a gareki yasa ban bari zuciyata ta ƙawata min wannan ba, ashe yaudara kuke ke da ƴar'uwarki, na shiga uku na lalace ina kika samo shi?”

Ta ɗora hannu saman kai ta nufi ɗaki tana kuka. Hakan yasa na cire Hijabin da ke jikina na aje a gurin tare da wayata na rufe mata baya. Safa da marwa na tarar tana yi a cikin ɗakin tana kuka, kamar jira take na shigo sai ta rufeni da maganganu marar daɗi.

“Kun cuce ni Nawwara, wannan ba tarbiyar gidan nan ba ce, ina kuka ɗaukota? Kun ƙara shafa mana baƙin fenti acewa mahaifinku ɓarawo ku kuma a kiraku ƴan iska, wayyo Allah na”

Ta faɗi tsakar ɗaki tana kusar kuka. Kusa da ita na ƙarasa na ɗafa ina kuka na ce

“Wallahi ba mu watsar ba Inna, ita ma yaudararta aka yi”

“Waya yaudareta? Faɗa min waya rusa mana ɗan farincikin da ya rage mana?”

A nan na feɗe mata daga biri har wutsiya akan abunda ya faru, sai dai ban labarta mata cewar Mustapha ne ya aikata mata haka ba, saboda bana tabbacin cikin nasa ne ko ba nasa ba ni dai abunda na sani ba shi kaɗai na ya yi lalata da ita ba, nasan kuma duk na faɗa mata cewar shi ne zata iya zuwa ta samu iyayensa wanda hakan na san ba zai mana daɗi ba, domin zasu iya ɗauka ko wane irin mataki a kan ɗan su ƙwalli ɗaya da suke ji da shi.

Can ƙasa-ƙasa na hango muryar Inna tana cewa.

“Habiba ta ci amanata kuma ta ci amanar kanta, ta zubarda ƙima da duk wani mutuncin da yake gidan nan, a yau na yi nadamar haihuwarta, baƙincikinta zai kasheni, ni ma nice na tafi ba mahaifinku ba, Allah be ƙaddara ya ga wannan abun kaico da wayyo a rayuwarsa ba sai ni, Habiba kin cuce mu...”

Duk wannan furucin da Inna take akan kunnuwan Habiba saboda tana jikin ƙofa tsaye ne, sai da Inna bata iya ganinta saboda ta bata baya ne. Muna haɗa ido da ita sai ta bar jikin ƙofar ta nufi ɗakinmu. Da sauri na tashi na bita saboda irin hawayen da na hango suna zuba a idonta.

Ko da na shiga na tarar tana ta saurin cire uniform ɗin jikinta ta saka wasu tufafin. Jin motsina yasa ta juyo da sauri ta kalleni.

“Nawwara guduwa zan yi, ba zan zama dalilin mutuwar Inna ba, ba zan rasa Baba kuma na rasa Inna ba-”

Ta juyo ta cigaba da haɗa kayanta. Ƙarasa na yi kusa da ita ya miƙar da ita tsaye na kama hannyenta da ke zafi sosai saboda zazzaɓi na riƙe gam, ina kuka kamar yadda itama take yi har ɗayanmu baya iya yiwa ɗan'uwansa magana.


GOOD NIGHT.... 🤧

RAI BIYUWhere stories live. Discover now