RB-46

6.7K 735 189
                                    

Zafin marin ya haddasa min ganin duhu a idanuwana, sai na kyabta idon sau biyar sannan na ga Inna dake tsaye tana hararata, Noor kuma ya fashe da kuka ya rike min kafafu da dayan hannunsa. Hawayene suka soma zuba a idanuwana ina dafe da kuncina, sai na juyo na kalli Jibril da shi ma idanuwansa ke cike da kwalla, juyawa ya yi ya bar dakin ba tare da ya ce komai ba, sai da yaja kofar dakin sannan Inna ta soma fadamin maganganu marar dadi.

“Ina miki kallon mai hankali ashe baki da hankali, abunda kika aikata a yanzu ya fi abunda Jibril ya yi ma Noor shekarun da suka wuce, miye abun burgewa a cikin fadar irin wannan maganar a gaban idon dansa? Wane irin kallo kike son dan sa ya masa? Kina tunanin burgeshi zaki yi? Ki haddasawa danki tsanar ubansa da kanki? Idan ke baki son shi karki shiga tsakanin uba da da, Wallahi da Noor zai girma a cikin talaucin da ya fi wannan kuma daga baya ya hadu da mahaifinsa dole ne sai ya masa biyayya saboda haka Allah ya ce.

Wace irin zuciya ce da ke Nawwara, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne? Wa kika fi? Idan ma ba zaki yafe masa ba ai ba sai kin shiga tsakaninsa da dansa, Wannan ba halinki ba ne Nawwara kuma ba halina ba ne ba kuma halin Babanki ba ne, ban san inda kika dauko wannan bakar zuciyar ba”

Tun da ta soma maganar na lumshe ido hawaye na cigaba da min zuba, sai na ji ta fisge Noor daga rikon da ya yi min ina bude ido ta nuna min hanyar fita.

“Fita ki bar dakin nan”

Na bude baki zan yi magana ta daga min hannu.

“Bana son jin wata magana daga bakinki ki fice kawai kije gida”

Juyawa na yi kafafuna da nauyi zuciyata kuma da rauni na fito daga dakin ina share hawayena. Kowa kallona yake ni kuma na ki na kalli kowa na fito ina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi bakin gate din asibitin.
   Miyasa kowa ya kasa fahimtata? Miyasa ni kadai na ke jin abunda na ke ji babu mai ji min zafi? Ni kadai na san irin wulakancin da na fuskanta a gidan Jibril amman yau Inna har ta tana marina saboda shi? Zama da mutane da kalubale shi yake canjawa mutum rayuwa Inna ta kasa fahimtar hakan.
 
Har na isa gida kuka nake, mai Napep din har tambaya ya yi wai ko an yi min mutuwa ne nidai ban amsa shi ba, da hawayen fuskata na shiga gida Sakina da Jamila suna zaune waje suna shan iskar hadari da ke kadawa, yanayin shogowata yasa Sakina ta taso ta sauri ta tari ne sai ta haska fuskata.

“Lafiya Anti Nawwara? Ko Noor ya mutu ne?”

Na girgiza mata kai alamar a'a, ina kallon yanayinta da ya yi min kama da na Habiba, banbancinsu da Habiba ce rumgumeni zata yi ta fashe da kuka ko da kuwa bata san abunda na ke wa kuka ba.

“Anti Nawwara miya faru?”

Ta tambaya tana jijjigani zuciyarta cike da fargabar abunda ya saka ni kuka.

“Na rasa komai Sakina, na rasa karatuna wanda shine gimshiken rayuwata saboda Jibril, na rasa mahaifina mai fahimtar kukana, na rasa yar'uwar da ke goyon bayana, yanzu kuma zan rasa Noor Inna kuma tana goyon bayan Jibril, ni kan miya ragemin a duniyar nan? Kowa baya fahimtata, babu mai jin yarena, ni kadai na ke kukana, damuwata ni kadai ta dama, ni kadai na ke jin zafina, duniya ta juya min baya ta kona min komai na farinciki, duk abunda na taba zafi yake min, mai amfanin kuma ta mayarda shi toka da na taba sai dai ya bi iska, na kasa gane bayana balle na fuskancin gaba, babu ranar tsayuwar hawayena”

Ta rika hannuna tana kuka kamar yadda Habiba take min.

“Allah yana tare da ke Anti Nawwara shi zai miki maganin komai”

Na gyada kaina alamar gamsu har na saukarda nauyayyen ajiyar zuciya. Sannan na share hawayena na nufi dakinmu.

“Habiba”

Ina shiga na ambaci sunanta kamar tana jina, sai kuma na kwanta saman katifa ina hawaye, wayar da ke hannuna ta yi kara alamar sako, ina dubawa na ga number Jibril.

RAI BIYUWhere stories live. Discover now