RB-28

6.1K 621 74
                                    

Khadija shine sunan da mahaifina ya saka min, sai ya yi min alkunya da Nawwara, duk da kasancewar ba ni ce ta farko ba, ƴaƴƴuna hudu maza duk basu tsayaba sai ni da nazo a ta biyar kuma mace.
  Bayan ni sai da mahaifiyata ta shekara biyar sannan ta haifi Habiba, a lokacin Mahaifina yana ta faɗi tashin rayuwa na nema mana abunda zamu ci.

Ba zan kira kaina da kyakkaywa ba, sai nasan ni ba mummuna ba ce, abunda kawai zan iya shaidar kaina da shi shine na ɗauko fari da kuma dogon hancin mahaifiyata kasancewarta fulani, gashin kan ba a magana na girata ma askewa nake balle kuma na gadon bayana dake ƙayatarda mai kallo.

Siye da siyarwar na fatoci, Sana'ar iyaye da kakkanina ce sana'ar wacce mahaifina ya buɗe ido ya samu kansa a cikinta har muma muka zo muka tarar anayi, kowa ya tashi a gidan ana buɗa masa shago ko kuma a haɗashi da wanda zai riƙa masa ja gaba kan sana'ar har ya kafa tashi.
Kusan zan iya cewa sana'ar bata karɓi mahaifinmu ba, tun lokacin da ya fara ba riba ba kuɗi, wani lokacin har kuɗin wani sai sun shiga ciki su ƙi fita, duk lokacin da mahaifinmu ya siyo fata da zimmar saidawa sai karaya ta sameshi wacce zata zama silar da ba zai iya maida kuɗin ba, yayyunsa da Yakumbo da kuma Hajiya Lamtana Allah ya jiƙanta sai suka ɗauki karan tsana suka ɗora ma Ramatu wato mahaifita, a ganinsu ita ce bata da ƙashin arziki, sukan ce wai can kamin ya aureta a lokacin da yake saurayinsa yana sa'arsa lafiya sai da ya aureta sannan komai yaso ya lalace.

A lokacin ina ƙarama amman abun yana min zafi sosai saboda yana damun mahaifiya sosai, har na riƙa kallonsu a matsayin maƙiyanmu wanda har yau shine a zuciyata, domin a lokacin a gaban idonmu suna faɗa wai uwarmu mai farar ƙafa ce wanda hakan suke tunanin ba komai bane ko kuma mu bamu kula ba alhalin yana mana zafi sai dai bamu isa mu nuna ba kasancewar gidan taro ne, ko tari kayi sai anji, Babban gida irin gidan nan ne da kakanni suke siye sai iyaye da jikoki su taru a gidan kowa ya keɓe wani ɓangare nasa ya kafa nasa iyalin.

Lokatuta da dama takan keɓe ita kaɗai ko kuma da mu tayi ta kuka tana roƙon Allah ya bawa mahaifina wani aikin duk da bashi da wani karantun zamani a wacan lokacin, muna haka wani maƙocinmu Malam Buba kuma abokin Baba da yake yawan zuwa Abuja ya faɗa ma Mahaifimu cewar wani attajirin mai kuɗi a garin Abuja yana neman mai masa gadi kuma ya ce baya buƙatar kowa sai bahaushe ɗan'uwansa, Malam Buba ya kasance yana masa gadin wani babban kamfanin siyer da kayan alatu ne dake can garin Abuja.

Muna zaune gida ranar wata talata, bayan mun gama cin kwaɗon ƙanzo, sai Baba ya shigo da far'arsa yana labarta mana abunda Malam Buba ya faɗa masa, Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta, a nan suka yanke shawarar ba zasu sanar da Yakumbo da Hajiya ba saboda sunsan ba zasu bari yaje ba, sai suka haɗa kai da Malam Buba ya faɗa musu Babanmu zaije Abuja ya kai fatune saboda ana bukatarsu a can, sun yi na'am suka masa addu'ah da fatan nasara, sai Baba ya karɓi fatun bashi da sunan idan yaje can zai aiko da kuɗin.

Ranar da zai tafi munyi kuka sosai ni da Inna har ma da wasu mutanen gidan saboda muna ganin kamar ba zai dawo ba, tafiya nisa kuma har garin Abuja garin da a wacan lokacin muke ɗaukarsa kamar wata ƙasar dabam.
  Bayan wata ɗaya da tafiyar mahaifinmu sai gashi ya dawo cikin shigar mutunci da kamala, sai dai ya ɗanyi rama kaɗan ya kuma yi haske, ya labarta mana komai yake muna nan cikin ranshi wannan tunanin ne ya hanashi ƙiba, har ma yake faɗa mana cewar mai gidansa ya ware masa wani ɓangare na gidansa ya bashi ya ce ya ɗauko iyalansa su dawo nan kuma ya zo mana da kuɗi mai yawa.

Ba ƙaramin yaƙi akayi ba kamin Hajiya ta yarda ta barmu aka tafi da mu, a nan ma sai da ya yi mata wata ƙaryar cewa ya canja sana'a yanzu yana siye da saida takalma ne na fatu har ma ya ce mata hayan gida ya kama a ƙauyen Abuja acan zai zauna da mu ya cigaba da sana'arsa.

Amaina huɗu a mota kamin mu sauka zaria, aka siya min abinci da ruwa na cika cikina ni da Habiba sannan muka cigaba da tafiyar, ko da muka shiga garin Abuja ina bachi, sai da motar ta tsaya sannan Inna ta tasheni muka koma can wani ɓangare na tashar, Baban mu ya ari wayar wani ya kira Alhaji ya sanar masa mun iso domin ba a shiga da wani abun haya a unguwar.
   Dare ya yi sosai har Baba ya yanke shawarar zuwa gurin abokinsa Malam Buba mu kwana a can sai ga ƴan komisho sun zo suna neman Malam Musa Kafinta, a nan suka haɗa mu da mutumen yanayin yadda Baba ya gaisa da shi sai ya tabbatar da cewar ya sanshi, ashe direban Alhajin ne.
   Ni da Inna duk da tsoro muka shiga motar saboda ganin Babbar motar kamar wannan wacce ni dai zan iya rantsuwa hannuna ma be taɓa kaiwa akanta, amman yau zan shigeta. Ina ta rabon ido har muka iso wata kyakkyawar unguwa. Idona be ƙara buɗewa har sai da muka iso cikin ƙaton gidan dake cike da ababen more rayuwa.

RAI BIYUWhere stories live. Discover now