RB-37

6.2K 784 260
                                    

Ina fitowa daga banɗaki na zauna saman tabarma da na tashi sai Noor ya miƙon wayata da ke hannunsa.

“Momy gashi an kira na ɗauka amman ba ayi magana ba”

Ina karɓar wayar na duba sai na ga number Jibril number nan ce da ya saba kirana da ita.

“Ka yi magana?”

“Ee amman ban ce ance komai ba, sai na ce idan kin zo zan faɗa miki sai na kashe”

“Na shiga uku Noor miyasa ka yi magana?”

Hankalina ya tashi sosai zuciyata na ta raya min Jibril zai gane cewar Noor ɗansa ne.

“Momy ban ce komai ba”

Ya faɗa ganin yadda duk na bi na rikice, kai na gyaɗa masa naja shi zuwa saman ƙafafuna na zaunar da shi na rumgumeshi, muna haka wayar ta ƙara ringing ina dubawa na ga Number Jibril sai na kashe wayar gaba ɗaya, gabana sai faɗuwa yake, zuciyata na nuna min Jibril zai uya zuwa gidan nan a yanzu ko anjima saboda ɗansa.
Unƙurawa na yi na tashi sai ga Jidda ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, sai jikina ya ƙara yin sanyi har na ke ganin kamar ita ma tare take da Jibril.

“Noor tashi kaje ɗaki yi sauri”

Sai da ya gaisheta sannan ya tashi ya nufi ɗakin, ita kuma ta zauna kusa da ni tare da dafani.

“Ki kwantar da hankalinki ba zan cuceki ba, ba kuma za a haɗa baki da ni a cuceki ba”

“Idan har ni be cuceni ke zai cuce ki”

“Mustaphan da kika sani a baya ba shi ne a yanzu ba, Wallahi ya canja Nawwara kuma saboda ke ina ganin wannan kaɗai abun farincikine ace ta dalilinka wani ya shiryu”

Na gyara zamana ina kallonta da kyau.

“Bakin san waye Mustapha ba shiyasa kika wannan maganar, baki san iya ta'asar da ya yi ba shiyasa kike ganin kamar ya canja”

“Ya canja Nawwara ko ki yarda ko karki yarda Mustapha ya canja, ganin da kika mana tare yazo gurina ne saboda yana neman yafiyarki, yana son na taimaka masa na nema masa yafiyarki”

“Kin san abunda ya aikata min kuwa?”

“Shine mutumen da ya yi fyaɗe ya bata dubu ashirin ko? Ko ba wannan ba ne?”

Kallon mamaki na yi mata.

“Ya faɗa miki kenan?”

“Ya faɗa min komai saboda kawai yana neman yafiyarki, ki dubi girman Allah Nawwara ki yafe masa ko ya samu sassaucin rayuwa”

“Taya kika san tuban gaskiya ya yi? Maza suna yaudararmu Jidda saboda sun san mu mata muna raunin zuciya, sukan yi amfani da wannan damar su sake cutar da mu”

“Ba zai taɓa cutar da kr ba Nawwara, tun daga lokacin da kika taɓa marinsa ya ƙyaleki zuciyata ta raya min Mustapha son kin yake ko kuma son wani na ki, ya isa shaidar kirki cewar Mustapha tuban kirki ya yi tun da ya biyo ki har ƙofar gidanku ya nemi yafiyarki, idan har yana son cutar da ke ba zai taɓa neman yafiyarki ba, zai iya sakawa a ɗauko masa ke ya yi miki yadda ya ke so, zan iya dafa miki ƙur'ane cewar Mustapha tuban ƙwarai ya yi kuma ya yi nadama”

“Ba zan yafe masa ba da gangan mutun zai aikata abu sai kuma ya dawo neman yafiya, da ace be mata fyaɗe ba da bata samu ciki ba da duk be kaita ga halaka ba, da yanzu ƴar'uwata tana nan raye”

Na faɗa zuciyata na mugun ƙuna. Sai dai abunda ya fito daga bakin Jidda ya kusa ya ruɗar da ni ko kuma ma na ce haukatarda ni gaba ɗaya.

“Ashe jahila ce ke Nawwara, karatun addininki be amfaneki da komai ba, baki da imani ko kaɗan saboda baki yarda da ƙaddara ba, kuma bari na gyara miki kalamanki da ace yar'uwarki bata je ta kai kanta gunsa ba da be samu damar yi mata fyaɗen ba, kuma ko da Mustapha ko babu Mustapha dole Habiba zata mutu kuma dole sai wani ya yi mata fyaɗe kuma dole sai ta yi ciki saboda yana rubuce cikin kundin ƙaddararta, tirr da halinki Nawwara tirr zuciyar da bata yarda da ƙaddara marar kyau ba sai mai kyau, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke da Allah zai cewa faɗi ki mutun kuma ki faɗin ki mutu dan dolenki, zuciyarki bata da kyau Nawwara saboda babu imani babu tausayi a cikinta, bawan Allah nan ko shi da hannunsa ya kashe Habiba ya kamata ki yafe masa tun da har yace miki ya tuba, balle fyaɗen da idan aka bincika daga shi har ita suna da laifi-!”

RAI BIYUWhere stories live. Discover now