RB-42

5.9K 863 239
                                    

Sun samu kusan mintuna arba'in suna meeting din sannan daga karshe suka cimma matsaya daya akan kwangilar da kamfanin zai bawa kamfaninsu Jibril.  Hannu ya mikawa Jibril suka gaisa sannan ya fito, daman hankalinta yana can gurin Nawwara zuciyarsa na raya masa tana can tana fira da wannan mutumen na dazu.
 
Da ya fito sai ya samu Mutumen shi kadai yana ta aikinsa sai wasu mutun biyu da suka zauna a kujerar da ya bar Nawwara dazu, kamar ba zai tambaya a zatonsa tana can wani gurin ne ko kuma ta koma cikin mota.

“Mai gida matar da kuke tare ta fita wai dan ta ya yi hatsari”

Sai Jibril ya tsaya cak kana ya juyo ya kalleshi.

“Dan ta?”

Ya fada.

“Ee tun dazu ta tafi na ce bari a fada maka sai ta ce a a”

“Kasan matar da muke tare kuwa?”

“Ee wacce kuka shigo tare, ai ni na tarboku na santa wata fara doguwa ba sosai ba mai dan fadin fuska tana sanye da abaya green”

“Amman dan ta ka ji ta ce ko kanenta?”

“Dan ta dai ta ce indai ba rudewa ta yi ba, saboda waya aka kira aka fada mata”

“Kaji wani abu bayan wannan?”

“A a gaskiya hankalinta a tashe yake bata ce komai ba”

Da sauri Jibril ya fita daga harabar gurin direbansa na hangosa ya san a uzurce yake kuma ya san babu abunda ya tsana irin jira, tun kamin ya karaso ya janyo mota kuma ya bude masa. Har Jibril zai shiga sai kuma ya mika masa jakarsa da laptop dake hannunsa.

“Nawwara ta tafi”

“Ee naga ta fice da gudu tana kuka har wani na tambayarta a abunda ya faru bata dai kula shi ba”

Ya amsa masa yana saka Laptop din a mota, juyawa Jibril ya yi ya koma ciki gurin mutumen dazu.

“Please ko kaji inda zata je? Ko kuma inda hadarin ya faru?”

Mutumen da dan yi shiru sannan ya daga masa kai.

“Ee na ji ta ambaci Specialist Hospital gaskiya ina jin ko can aka kai yaron ko kuma can hadarin ya faru”

“Thank you”

Ya juyo da sauri ya nufi gurin motarsa, driver seat ya nufa ya ce direban ya fita ya hau achaba shi akwai inda zai je, @360 ya fisgi motar kamar zai tashi sama, wani irin vibration jininsa yake yana jin kamar ya runtse ido ya gansa a cikin asibitin.

“Dan ta...”

Yana ta maimaita hakan ya iso Abuja road sai ya dauke hanyar da zata sada shi da Specialist, gudu yake sosai kamar dan shi aka yi titi ko kuma ance masa babu ababen hawa sai nasa kadai.
  Lokacin da zai kunna kai a gate din Specialist din sai da ya yi kamar zai buge wani magidanci da ke kokarin fitowa.
  Ko fakin din kirki be yi ba ya fito yana ta waiwagen inda zai shiga, tsabar rude daman can sau daya ya taba shigo asibitin loacin da yake farkofarkon zuwa sokoto sika yi wata mata tiyata.

Da sauri ya nufi emergency wajen yan hatsari, har ciki ya karasa ya karasa inda Nurses suke ya muna masu id cart dinsa sannan ya soma tambayarsu ko an kawo wani.

“Eh an kawo mutun daya yanzu”

“Zai kai minti nawa?”

“Ten haka yanzu yanzu”

“Babba ne ko yaro?”

“Gaskiya dattijo ne”

“No wanda na ke nema karamin yaro ne yana tare da mamansa ina jin za ayi awa daya yanzu da kawo shi”

RAI BIYUWhere stories live. Discover now