RB-03

7K 665 21
                                    

     Bayan na baro ɗakin Inna na ɗibi ruwa a shiga ban ɗaki na yi wanka. Atamfata ta sallar bara na ɗauko na saka, akwai da son saka gyale duk da kasancewar Baba baya son haka, daman ba ko waɗanne uwane suke son ƴarsu ta saka gyale ba, sai dai nawa gyalen ba irin na barbarɗaɗɗin ƴan mata nan ne ba, me zai kai ni saka ƙaramin gyale bayan ina da ɗa kuma ba budurwa ba ce ni, duk da yake wani lokacin Jidda da Habiba har da mutanen waje kan faɗa min babu wanda zai kalleni ya ce ni bazawara ce har sai idan ni na faɗa, wani lokacin ko da na faɗa ba a yarda har sai idan waɗanda suka san ni ne. 

Ina da kyau jiki dai-dai gwargwado wannan yasa mutane basa yarda idan har na faɗa cewar ni Bazawara ce har da ɗa, wannan baya rasa nasaba da auren wuri da aka min, a lokacin da nake ganin kamar ban isa auren ba, auren da ya gurɓata min rayuwa ya canja ƙaddarata daga mai kyau zuwa mummuna.

Atamfata miyan goro ce mai ratsin ja, hakan yasa na saka jan gyale saboda atamfar ta ƙara fita, talkamin Habiba na ɗauka na saka masu launin ja. Fes na fito sam baza kalleni kace ina da wata damuwa a wannan lokacin ba, idan ba ka birkice atamfata gaka ta roba bace sai ka ɗauka ni ƴar wani shegen mai kuɗi ce, ba laifi ni kaina ina sarawa kaina indai babin kwaliyana ne na iƴa fito kamar matar minister.

“Inna zan tafi”

Na faɗa ina tsaye daga jikin ƙofa, kai na jingine da ƙofar ina kallon Baba da ke unƙurin tashi.

“Tau Allah ya kiyaye”

Inna ta faɗa, Baba kuma sai ya ce

“Ni ma bari na shiga kasuwa na ga abunda Allah zai yi”

Salamar Maniru muka ji wato almajirin Hajiya Murja, maƙociyarmu masu babban gida, matar babban soja wacce bata taimako sai idan da dalili. Ni da Inna muka haɗa baki gurin amsa masa, Baban kan ya amsa masa da.

“Bata nan taje makaranta”

Domin yasan Jamila take nema, takan aiko kiranta a duk lokacin da wani aiki ya sha gabanta, domin kawai ta taya ta aikin sai ta sammata wani abu daga abincin rana ko dare da aka yi a gidan.
  Bayan Maniru ya fita Baba ya haɗe fuskarsa saboda mu ɗauki zancensa da muhimmanci, ya saba mana a duk lokacin da yake hanin mu kan aikata wani abu ko kuma ba mu umarni.

“Bana son zuwan da Jamila take a gidan Manjo Faruku, kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi”

“Ni kaima bana son zuwanta a gidan domin yaron gidan nan ba shi da tarbiya, sannan yunwa babu abunda bata sawa musamman ga waɗannan da suke yara”

Na faɗa cike da jin zafin tuna irin satar da ta taɓa ɗorawa Sakina a kwanakin baya.
Inna dai bata ce komai ba bayan ajiyar zuciya da ta sauke.

“Na tafi nidai ayi min addu'ah”

“Tau Allah ya bada sa'a karki daɗe dai, kuma ki kula.da irin mutanen da zaki yi hulɗa da su”

Cewar Inna ni kuma na amsa da tau na kama hanya ina addu'ar fita daga gida wato.  _Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah._
_بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ_

Babu ko ƙwandala a hannuna ƙasa na kama hanya duk kuwa da kasancewar unguwar akwai ɗan nisa da ta mu. A bakin ti-ti na haɗu da Bilal wato abokina ko kuma na ce mutumen da muke mutunci da shi sosai har mutane suke raɗin-raɗin wai akwai soyayya a tsakanin mu.

“Nawancy”

“Bilal ya gida?”

“Lafiya ƙalau Wallahi Ina zaki je haka?”

Bana son faɗa masa ainahin inda zanje, ba kasafai nake son mutane su san ina zuwa aiki ba nafi son aji na samu aikin kawai, musamman Bilal da yake yawan nuna min baya son neman aikin da na ke.

RAI BIYUWhere stories live. Discover now