RB-08

5.7K 580 31
                                    

  Riƙani ta yi ta tayar ta maida can kusa da Inna ta zaunar tana bani haƙuri da kalaman da za su sanyayamin zuciya.

    Kuka muke ta yi ni da Habiba, yayinda Inna ta rafka uban tagumi tana kallon gawar Baba. Baba Dahiru ne yaja janena dake kan igiya ya rufa masa. Haka muka zauna har garin Allah ya waye babu wanda ya runtsa. Su Baba Dahiru ne suka yi alwala suka tafi masallaci yayinda mu muka yi namu sallah a gida, bayan na gama na ɗauko alƙur'ane ina karantawa, izuwa yanzu bana da buƙatar wani kuka bayan wanda na yi jiya ya haddasa min ciwon kai da kumburewar idanu,  ina jin yadda maƙota na nesa da na kusa ke ta shigowa suna jajantama Inna, wasu na san gulma ce ta kawo su tun da gari ma be gama wayewa ba amman har labarin ya zaga unguwarmu da ma unguwanin da ke kusa da mu.

Bayan fitowa Masallci sauran ƴan'uwan Babana suka shigo maza da mata cikin har da Yakumbo.  masu kuka na yi masu faɗa na yi, Baba Ayuba ne ya bada shawarar a ɗauki gawar Baba aje da ita police station a mayar musu, Baba Sulaiman kuma ya hana wai ba za a tagayar masa da gawar ɗan'uwa ba, idan aka yi haka ɗan'uwansa aka wulaƙanta. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa station ɗin ba tare da gawar Baba ba, a ɗakin mu aka saka shi sai aka rufe ɗakin duk muka kwaso muka dawo ɗakin Inna. Noor ya zo kusa da ni ya zauna, Jamila da Sakina kuma suka zauna gurin ƙofa suna ta aikin kuka kamar yadda Habiba ke yi. Ni kuma ɓa noce kaina ƙasa bana kuka kuma bana tunani kaina kamar fanko na ke jinsa, shigowar Jidda da Mahaifiyarta ce ta ɗaga hankalin kowa, saboda kuka da take kamar ita akayi ma mutuwar, sai gida ya ɗauki kuka muryarta muryar Habiba da Inna sai kuma Jamila da Sakina. Yakumbo ce ta katsa musu tsawa tana faɗa kan kuka da suke, musamman Inna da take ganin ita ya kamata ace ta rarrashe mu amman ita take kukan ma.

“Mamaci addu'a yake so ba kuka ba, bawan Allah nan fa yana cikin gidan nan amman kuna ta masa kuka, kuka ai ba zai dawo da shi ba, ba zai muku maganin komai ba, amman addu'a zata iya sanyaya muku zuciya kuma ta canja lamarinku, sannan shi kuma Allah ya karɓa yayi masa rahama.
Yanzu ke Hajara ke da ya kamata ace kin bawa yaran nan haƙuri, sai ki zauna kina kukan tare da su, Allah be yi wani dan wani ba, be yi Musa dan ku ba kuma be yi ku dan Musa ba, shi ya hallita abunda yasa masa rai yanzu kuma ya karɓi abunsa, gode masa ma ya kamata ku yi kuma ku yi haƙuri sai kuga Allah ya yi muku wata mafitar”

Ba laifi kalamanta sun yi tasiri gurin Inna da har tasa hannu ta share hawayenta tana ta kokuwar tsayar da kukanta, Habiba kan kunne uwar shegu ta yi sai abunda ya cigaba, kusa da ni Jidda ta dawo ta zauna ta kama hannuna ta riƙe sai hawaye take, ni kan kallonta kawai na ke ina jin kaina kamar babu komai a ciki.

Tun da suka ta fi basu dawo ba sai ƙarfe goma na safe har da ƴan mintuna, mutane da suka je tun hasken alfijir ba gama yayewa ba. Tare da tawagar ƴan sanda suka zo wanda hakan ya haddasa mana dandazo jama'a a ƙofar gida.

Dpo ne ya shiga da kansa ya duba gawar baba tare da wani ƙaramin ɗan sanda mai ɗaukar hoton jikin Baba, bayan ya gama dubawa ne ya dawo gurinmu, a bakin ƙofa ya tsaya yana ba mu haƙuri tare da faɗar za a ɗauki mataki da ya dace.

“Wacan ƴarsa ce?”

Ya tambaya ganin ni kaɗaice na kasa ɗago kai na kalleshi tun da ya soma maganar har ya gama. Inna A'i ta nuna Habiba da Jamila da kuma Sakina

“Eh da wannan da wacan da wacan, su kaɗai Allah ya bashi”

“Allah sarki ku yi haƙuri zamu ɗauki mataki, yanzu haka mun sa an kama ƴan sandan da suka yi wannan aika-aikar kuma za a gabatar da su a gaban kotu In'sha Allahu”

Ya ƙarasa yana ciro duba goma da uku ya miƙawa Jamila da ke kusa da shi, kana ya miƙe tsaye yana mana sallama.

“Mu za mu tafi Allah ya sanyaya zuciyarku”

Na yi zaton ya tafi hakan yasa na ɗago idona da ke cike da hawaye na kalli ƙofa, karaf idona sai cikin nasa, sauke na sa idon yayi ya wuce ƴan sanda na take masa baya. Na yi baƙin cikin haɗa ido da shi domin a yanzu ko mutuwa ban tsana kamar yadda na tsanesa ba, da saninsa aka yi ma mahaifina komai saboda ƴar'uwarsa har suka kashe shi. Bayan fitarsa Baba Sulaiman ya shigo yana mana bayanin yadda abun ya wakana lokacin da suka isa station ɗin.

RAI BIYUWhere stories live. Discover now