BIYYAYA BAYAN RAI 1

2.2K 75 0
                                    

BIYYAYA BAYAN RAI
A

aa

NAH

UMMU A'SMAU (SA'ADATU)
 
DEDICATED TO NABEELERT ZANGO(LADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM

Page 1-5

Zaune take a bayan class  dinsu kasan wata bishiya ta kifa kanta saman kafafuwanta banda kuka babu abinda takeyi. Taya ummunsu zata kawo mata wani bakon al'amari lokacin da zuciyarta ta samu abokin rayuwa.

Kafin Abbansu ya rasu shi bai fada mata kudirinshi akanta ba? Me yasa ummansu takeso ta hadata da wani daban? Kodan taga yana da kudi gashi  yanzu ita daya take kula dasu? Idan har tana so nayi aure ai sai ta barni na auri zafina.

Saboda taga Abbanmu ya rasu shiyasa ta hado maganar aurena dashi? Mai yasa takeso dole sai nayi BIYAYYA BAYAN RAI? Gaskiya bazan iya wannan abun da take bukata ba.

Tabbas nasan ince zan cutu, gashi yana da mata har da yara, shikenen ni bazan yi rayuwata kamar yanda muka dade muna mafarkinta ba? Ni nasan da Abba yanaso ya hadani dashi bazai boye mani ba.

Saboda anga baya raye akeson afito da wata wasiya kuma a danganta ta dashi. Dago kanta tayi tana goge idonta da bayan hannunta wanda sukayi jawur saboda tsabar kuka.

Dole ce tasa tazo makaranta saboda tanaso ta hadu da muradin ranta, sai gashi abin haushi ma baizo ba, ta kira wayar shi akashe. Hakan ne yasa takasa zaman ajin tafito nan ko zata samu saukin zugin da takeji a zuciyarta.

Gashi lecturer dinsu ya shiga amman bata jin zata iya shiga aji ayanda idanuwanta suke, duk wanda ya kalleta yasan tasha kuka. Maida kanta tayi saman kafarta yayin da wata zuciyarta take saka mata kawai ta gudu tabar gidan.

Domin sai tana gidan ummansu zata iya aura mata mutumin da bata so, don a zuciyarta takasa yarda da maganar ummansu na cewar auren da takeso tayi wasiyyar Abbansu ce, kawai tana gani son zuciyar ummansu ne shiyasa tace haka.

Ta rasa dalilin umma nason ta hadata da wannen mutumin, bayan ummansu tana matukar son yaranta, suna rayuwar jin dadi mezai sa yanzu kuma canjin rayuwa ta dalilin wani aure can

Jinjina kai tayi tana fadin komai zai faru bazan taba bari na auri mutumin da zuciyata bata so ba. Babu wata BIYAYYAR DA ZANYI BAYAN RAI. Na gode Allah da  Abba baya raye, nasan idan yana raye ya yanke wannan hukunci bazan iya mashi musu ba.

Nasan idan nabar gidan navwani lokaci ummana zata sauko domin tana da saukin kai.murmushi tayi tana kara goge idonta lokacin data gama gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta yanke mata.

Dafata taji anyi, a firgice ta juyo, ajiyar zuciya ta saki ganin kawarta ce maryam juyawa tayi tana kara goge idonta saboda bata son kowa yasan halin da take ciki. abinda bata sani ba duk maganganun da tayi na karshe duk afili tayisu kuma maryam kawarta taji.

Murmushi tayi tana tun yaushe kikazo? Zama maryam din tayi fuskrta cike da damuwa saboda jin abubuwan da Na'ima take fada, gashi idanuwanta sun kumbura saboda kuka, ko bata fada mata ba tasan tasha kuka sosai.

Kallonta tayi tana fadin Allah yasa abubuwan da naji ba gaskiya bane? Haba Na'ima da hankalinki kike tunanin aikata abinda naji kina fada? To wai ma menene yake damunki? Ashe akwai abinda zaki boye mani? A tunani na babu  abinda zaki boye mani.

Yashe aka sa maki rana bamu sani ba? A cikin kalamanki na fahimci kamar auren dole zaayi maki ke kuma kike son ki bijerema ummanku. Haba Na'ima, da hankalin ki kike fadar guduwa kibar umma da kannanki? Kada kimanta duk wata diya mace mai hankali da tarbiya ta zauna agaban iyayenta shine gatan ta.

Wallahi matukar kika sa kafa kika bar gidanku da niyar guduwa duk inda kikaje kallon karuwa zasuyi maki,  babu wanda zaiyi maki kallon mutuniyar arziki, domin duk Da na halak agaban iyayenshi yake daraja.

Dago kai tayi tana kallon maryam hawaye suna cigaba da zubo mata. Hannu tasa ta goge idonta tana fadin bazaki fahimci abind nakeji bane.kinfi kowa sanin irin son da muke ma junanmu da kabir, taya ummu zata zo mani da maganar Alhajin da suke tare da Abbanmu kafin ya rasu wai Abba yabar  mata wasiyyar ko BAYAN RANSHI na aureshi.

Kawai gani nakeyi umma tanaso na aureshi ne shiyasa tace wasiyar Abba ce, koda ace wasiyarshi taya kike tunanin zan iya yin BIYAYYA BAYAN RAI? Ai tunda Abba ya rasu kawai abarni na auri wanda nakeso.

Tunda har ba shind ya fada mani da bakinshi ba kona auri wani Allah bazai kamani da laifin komai ba. Saboda haka guduwa zanyi, idan umma taga na gudu zata fasa abinda tayi niya daga baya sai na dawo nasan ummana tana saukin kai zata fahimceni

Murmushi maryam tayi tana fadin kina tunanin saboda Abba baya raye shikenen duk doka daya kafa kafin ya rasu zata daina aiki? Wallahi duk yaran da suka san abinda sukeyi  har su mutu bazasu taba watsi da duk wata huduba ta iyayensu ba koda basa raye.

Ai kyan 'ya'ya su kasance masu yima iyayensu BIYAYYA KO BAYAN RANSU NE. Idan har zaki iya yima mahaifinki BIYAYYA lokacin yana raye banga dalilin da zaisa ki kasa  mashi BIYAYYA BAYAN RANSHI BA.

Nide na fada maki iya gaskiyata, kiyi hankuri da zafin Abbanki, ummunki bazata taba fada maki karya ba, duk abinda zata fada tabbas wasiyyar da Abba ya bar mata ne, ribar mezataci idan tayi ma mamaci karya haba Na'ima kiyi tunani mana.

A tunaninki saboda kudin Alhaji umma takeson ki aureshi, kisan dai umma bata cikin talaucin da zata bayar da ke saboda kudi. Kawai tanaso  kisamu kwanciyar hankali ne, Allah kadai yasan Abinda Abba ya hango maki awajen Alhajin tunda kince Abba yasanshi sosai.

Shi kanshi Abba da yasan mutuwa zaiyi kafin ya rasu zai fada maki kudirinshi, kuma na tabbata lokacin da zai bakwa kusa da sai ya fada maki, tunda ummanki kawai take kusa dashi dole ita zai fada mawa.

Mikewa tayi tana girgiza kai tana fadin nagode da shawararki, amman kisani bazan iya cutar kaina ba, idan nayarda nice zan zauna ba wani ba.

shikenen haka rayuwata zata kare, ita ummu ai auren soyayya sukayi da abba, ke kanki wanda zaki aura zafin kine bana wani ba, shine ni kuma kike kokarin tursasani na auri wani can. Matukar ina raye babu wanda zan aura sai zabi na. Bazan taba amincewa da wata BIYAYAYA BAYAN RAI BA. Wucewa tayi tabarta zaune awajen ta nufi hanyar fita daga makarantar.

ASALIN LABARIN.

Kubiyoni zuwa next page don jin asalin labarin BIYAYYA BAYAN RAI.

Ummun As'mau(sa'adatu

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now