BIYAYYA BAYAN RAI

462 31 0
                                    

BIYAYYA BAYAN RAI 20-25

NAH

UMMUN ASMA'U(SA'ADATU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 20-25

Sosai Dr yayi farin ciki akan maganar da abokin MD yazo mashi da ita, dama abinda ya dade yana jiran ji daga garesa kenan, saboda bayaso shi ya fara masa magana kada yaga kamar yana tallar diyarsa ne.

Gyran murya yayi tare da kallon abokin Md yace ai wannan ba wani abu bane, dama yana sonta shine yakasa fada mani? Ai matsayinmu ya wuce haka, na daukesa tamkar dan uwana.

Babu abinda zance sai Allah yasa muna raye, kuma nayi matukar farin ciki da wannan magana, Alhamdulillahi Na'ima bata da wani wanda takeso domin tasan bana barinsu kulawa kowa sai sun gama karatu.

Kuma ni sheda ne domin tunda Na'ima tashiga makarantar nan ban taba ganin kowa yazo wajenta da sunan fira ba. Tunda yanzu suna a final year na bashi dama ya nemi so awajenta, kuma nasan Na'ima bazata kishi ba.

Allah ya zaba abinda yafi alkhairi. Sosai abokin MD yaji dadin abinda Dr, yace. Godiya yayi mashi sukayi sallama yatafi. Cike da farin ciki Dr yashiga dakin Umma dan ya fada mata labari mai dadi.

Yana shiga ya ssmeta har tayi bacci. Murmushi yayi yana fadin sarkin bacci, bara na kyaleki zuwa gobe mayi maganar. Bayan ya gama shirin bacci sako yashigo mashi ta wayarsa. Yana dubawa ya dafe kai.

Tsaki yayi yana fadin bana son irin haka, tun tuni sun san da tafiya bazasu fadama mutum da wuri ba, sai yanzu karfe 9 sannan zasu fada kuma ace anaso gobe atafi da safe. Wayarsa ce tayi kara.

Yana dagawa wanda yakira yace Dr kayi hakuri kaga sako late ko? Wallahi muma daga sama muka samu takardar kuma akace dole kaine zakaje shiyasa na turo maka yanzu. Dr yace ai ina nan na fara jin haushi kun aiko mani da sako very late.

Daga dayan bangaren yace kayi hakuri kila suma ahaka suka samu sakon. Dr yace shikenan babu damuwa, Allah yabkaimu goben. Yace amin. Yanzu zakaji alert sai ka dawo Allah ya kiyaye. Dr yace amin.

Tashi Dr yayi ya dauko jakarsa ya zuba kayansa kala biyu domin kwana biyu zeyi agarin Abuja.

Washe gari bayan yadawo sallar asuba yake fadama Umma maganar tafiyarsa. Cike da damuwa tace gaskiya wadannan mutanan sun cika shiga hakkin mutum, duka yaushe kadawo daga tafiya ai sai su tura wani ko.

Murmushi Dr yayi tare da kamo hannunta ganin yanda ta bata ranta. Zama yayi kusa da ita yana fadin kada ki damu, kinsan idan akace mutum yana rike gaskiya akan aikinsa kowa yanaso ya yaga ya hada alaka dashi.

Sanin kanki ne mutane da yawa suna son nashige masu gaba akan duk wani aiki daya taso. Kawai kitayami da addu'a wata rana dana aje aiki shikenan zan zauna tare daku. Murmushi tayi tana fadin Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya. Yace amin.

Bayan yagama shiryawa yatara yaransa sukayi addu'a kamar yanda ya saba idan zeyi tafiya, kallon Na'ima yayi yana fadin Na'ima ina fatan kin kusa kammala project dinki? Na'ima tace E Abba.

Jinjina kai yayi yana fadin da kyau, Allah ya bada sa'a, ki kara maida hankali banaso ki fadi ajarawarki ta karshe idan ba haka ba sai kin sake maimaita shekara daya. Kinga kece babba duk yanda kikayi haka nakasanki zasuyi.

Allah yayi maku albarka, ku kula da gida kwana biyu kawai zanyi insha Allah, banaso na samu labarin kunyi wani abu na rashin ji. Kiyi hakuri da kannanki. Na'ima tace insha Allah Abba.

Kudi ya ciro ya bama kowa. Godiya sukayi mashi suka gita rakashi, bayan sun dawo Dr ya kalli Umma yace idan nadawo akwai labari mai dadi. Murmushi tayi tace Allah ya maido mani da kai lafiya. Yace amin.

Haka yashiga mota tanadaga masa hannu shima yana dago mata har sai da ya fice sannan ta juya. Tana juyawa taga su Na'ima suna mata dariya. Hararsu tayi tana fadin sarakan sa ido me akayi? Na'ima tace Umma gani mukayi kamar bakiso Abba yatafi.

Murmushi tayi tace ai dole na damu, kema wata rana zaki fada mani irin haka. Dariya Na'ima tayi tashige ciki tana fadin zan baki labari mai dadi da Abba ya dawo.

MD kowa farin ciki baya misaltuwa, da ya tuna yanda shehu hassan ya fada masa sukayi da Dr, sosai kwananen yake cikin farin ciki.

Dr ya kusa shiga kaduna ummu zainab ta kira shi, tana tambayar sa ya hanya yace ya kusa shiga kaduna, tayi  masa Addu'an sauka lafiya sukayi sallama

Kadan Dr ya rage ya shiga kaduna, wata mota da ke bayansa driven yazo yayi overtaking motar Dr sai motar ta kwace wa driven ya tura motar Dr a jeji,  motar ta kubcewa Dr ta fara juyawa, sai da tayi juyi sosai ta daki wani katon ice ta tsaya, mutanen da ke wucewa ne suka tsaya  domin su taimaka Dr, da hanzari masu motar farko da sukayi tsaya suka nufi motar Dr, koda suka isa da kyar suka fito da shi jikin shi duk rauni ne da jini, daya daga cikin su yace su diba motar ko zasu samu information din shi, cen a karkashin sit, suka ga wayarsa da id cards din sa,  sun diba last call suka num ummu zainab, suka kira num ta, tana kitchen wayar ta dake gefenta ta fara kara a hankali ta dauki wayar gabanta na faduwa, daman tun safe take jin faduwar gaba, ganin num Dr sai ta dauka tana cewa ka shiga kadune, cen daya bangaren taji ance bashi ba, ummu zainab bakin ta na rawa tace waye, mutumin ya fadi mata, ya samu hadari ne a hanya, zasu wuce da shi asibitin shika, su hadu cen.

Ummu zainab tace innalilahi wa inna ilaihin rajiun, cikin rawar jiki ta wuce daki ta dauki hijab da keys din motar ta, ta fito falo lokacin hankalin ta yakai kan su fahad dake kallon tv, duk suka tashi suna tambayar ta lafiya, gudun kar suce zasu bita, tace masu a wajen aiki a ka kira ta yanzun zata dawo, lokacin Na'ima ta na makaranta, ta wuce cikin sauri tana ce  wa maigadin ya bude mata get, cikin mintuna ashirin ta isa shika teaching hospital, tun a  hanya take kiran num Dr mutanen da suka taimaka masa suke ce mata sun kusa, ta isa da mintuna suka isa, suna parking mota, ummu zainab ta isa, tana ganin halin da Dr yake ciki ta fasa kuka,  nurses ne suka zo da sauri da gadon daukar mara lafiya  aka dora Dr jini duk ya bata masa jiki kai tsaye emergency suka wuce da shi ummu zainab na kuka tana bin su.

A baki shiga emergency Dr ya bude idanunsa cikin zafin ciwo,  yace nurse su tsaya zaya yi magana da Ummu zainab, ta duka dai fuskan shi,  cikin tsananin juriya yake magana yace zainab kiyi hankuri da rayuwa duk yanda tazo maki, ki kula da yaranki, MD ya aiko man yana son ya neme auren Na'ima, zainab ko bayan raina ku aura ma sa Na'ima Muhammadu nasan zai rika ta da amana, ki fadima yan uwana su yaya sadiya su yafe min, nurse din da sauri suka wuce dashi ciki, don ceton rayuwar sa, wayyannen mutane da suka taimaka Dr su ne ke ta Ummu zaibab hankuri da ta daina kuka, Allah zai bashi lafiya su zasu wuce, ta yi masu godiya, ta kira sadiya da Aisha yayun Dr ta fada masu, ta kira yannen ta, ta fada masu, cikin tsananin tashin hankali ta kura ma kofar emegency ido tana Addu'a Allah ya tashi mijinta, likitoci ke ta shiga suna fita, bayan wani lokaci Aisha ta iso, Ummu zainab na gani ta, ta fada kanta tana kuka, Aisha ma kuka takeyi.

Babban likitan ne ya fito yana share zufa, da sauri suka nufe sa, suna tambayar Dr ya dago ya kalle su, ya jijiga kansa, yace sai kuyi  hankuri, Allah yayi masa cikawa, ya samu internal injury ne a kai, cikin karaji ummu zainab ta kurma ihu, ta fadi sume, Aisha ma tafasa kuka mai cin rai, a haka babbar yayar Dr sadiya da mijinta suka iso, da sauri a dauki ummu zuwa emergency, da taimakon likitocin ta bude idanuta sai take ganin kamar mafalki ne, ganinsu sadiya ya tabbatar mata ba mafalki take  yi ba, mijin sadiya ya cema likitan zasu iya wucewa da Ummu zainab gida , likitan yace eh zasu iya shock ne ta samu.

Matan ne suka wuce da ita gida, mijin Aisha da sadiya suka tsaya domin wucewa da gawar Dr gida, bayan sun karfi gawan ne suka wuce,  da kiran  dukkan dangi da abukan arziki suna fadi ma mutane, don hallarta jana'izar Dr.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now