BIYAYYA BAYAN RAI

452 29 0
                                    
🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU ASMA'U(SA'ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango leady

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 45-50

Na'ima ta dade kwance kamin bacci ya dauke ta, karfe hudu da rabi ta farka, sabon tashi da sukayi tun gidan su, tayi arwala ta fara nafiloli, MD ma lokacin ya tashi ya fara nafilolin sa, zuwa lokacin sallah subahin ya fito domin zuwa masallacin dake gaban gidan sa, ya wuce dakin Na'ima domin ya tadda sallah, yayi mamakin jin karatun qu'arani yana tashi ya yi mintuna yana saurarenta, ya gode Allah tabas ya samu irin matar da ya jima yana rokon Allah ya bashi. Ya wuce gefen Hindatu don yasan in ba tashinta akayi bazata tashi sallah ba, ya dade yana kwankwasa kofar gefen kamin mai yi mata aiki tazo ta bude, ya wuce dakin ta bacci abinta, sai da yaga ta shiga toillet ya wuce masallaci don yasan halin Hindatu zata iya komawa ta kwanta.

Bayan ankare sallah ya jima masallaci yana karatun qur'ani so da yawa mutanen unguwar har mamakin halinsa suke, kowa zai watse ya barsa masallaci bayan sallah subahin ba irin wasu masu kudin da ankare sallah zasu wuce, wasun ko sallah basa fitowa. Sai da gari ya waye ya fito masallaci, Shehu ne ya kira sa, yana tambayarsa hope komai daidai, MD yayi masa bayanin tun jiya bai ganta ta rufe dakin, ya kara fada masa yayi hankuri komai zai wuce, Shehu yace zuwa ajima zaa kawo masu break fast daga gidansa, kullun zaa kawo for a week don yasan Hindatu bazata basu abincin ba, MD yayi godiya sosai don yana tunanin yimata take away don yasan Hindatu.

Cikin gidan ya wuce gefen Na'ima kamshin turaren wuta ne ya tarbe sa, ko'ina tsaf da ganin yasan ta fito ne, kamar ya dibata sai yawu ce bedroom dinsa, wanka yayi ya shirya cikin wani hadadan material milky yayi kyau sai kamshi turare yake yi, yana fitowa falon yaji sallama maigadin yana fada masa ga driven gidan Alhaji Shehu an aiko, ya fita kofar gidan sun gaisa da driven ya amshi abincin cikin baban basket, falo ya wuce ya aje abincin a dining table.

Da faduwar gaba ya wuce bedroom din Na'ima yayi mamakin ganin kofar a bude, ya shiga da sallama tayi wanka ta shirya cikin kyakyan lace army green don kowane lokacin dark collar tafi sawa zamanta fara sosai, siket an bulawus ne sun amshi jikinta, shiru tayi masa taki amsa sallamar, ya sake sallama sanin hukunci sallama ta amsa masa ciki ciki, ya tsura mata ido yana kallon tayi masa kyau sosai, duk zamansa da Hindatu duk tayi kwaliyya fita zatayi, wani lokacin da daurin kirji take yini. Ganin bata ce masa kala ba, yace mata antashi lafiya still bace masa komai sai dane danen wayar ta take, yace akwai abinci a dining, still shiru ta masa,  ya yi seconds yana kallon kamin ya fita dakin, kichin ya wuce ya dauko plates da cups ya dawo falon, ya bude warmers din masa ce da miyar ganye, farfesun kaza da kunun tsamiya, yayi murmushi, yace Shehu kenen duk favorites din sa ne ya dibi abincin kadan yaci, hankalin sa na wajen Na'ima kamar ya koma ko ya dibi abincin ya kaimata, wata zuciyar na kwafarsa da ya kyaleta.

🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

☘☘

UMMU ASMA'U (SAA'DATU)

🌸🌸🌸

Dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 45-50

Na'ima ta dade kwance kamin bacci ya dauke ta, karfe hudu da rabi ta farka, sabon tashi da sukayi tun gidan su, tayi arwala ta fara nafiloli, MD ma lokacin ya tashi ya fara nafilolin sa, zuwa lokacin sallah subahin ya fito domin zuwa masallacin dake gaban gidan sa, ya wuce dakin Na'ima domin ya tadda sallah, yayi mamakin jin karatun qu'arani yana tashi ya yi mintuna yana saurarenta, ya gode Allah tabas ya samu irin matar da ya jima yana rokon Allah ya bashi. Ya wuce gefen Hindatu don yasan in ba tashinta akayi bazata tashi sallah ba, ya dade yana kwankwasa kofar gefen kamin mai yi mata aiki tazo ta bude, ya wuce dakin ta bacci abinta, sai da yaga ta shiga toillet ya wuce masallaci don yasan halin Hindatu zata iya komawa ta kwanta.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now