BIYAYYA BAYAN RAI

429 25 0
                                    

BIYAYYA BAYAN RAI 35-40

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

☘☘

UMMU ASMA'U (sa'adatu)🌸🌸


Dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi rahamanir rahim..

Page 35-40

Sai da Na'ima tayi nisa sosai, lokacin gari har ya gama haske sannan ta samu wani waje ta zauna, a hankali ta fara tuno irin gatan da Dr ya nuna mata, akwai lokacin da batada lfy tana fever sosai, ranar Dr baiyi bacci ba, shike rike da ita har gari ya waye, lokacin tana secondry School.
Runtse ido tayi tana tuna rayuwarsu kafin Abbansu ya rasu.

Ta dade ahaka tana tunani. Ajiyar zuciya tayi tana girgiza kai, a fili tana fadin  bazan iya ba, wallahi bazan iya guduwa na bar Ummana da Kannaina ba, idan na gudu kafin na kai inda zanje nayi hadari na mutu fa? Shikenan na mutu na bar mahaifiyata da bakin cikina.

Idan kuma Umma ta tashi ta gane na gudu idan zuciyarta ta buga ta mutu shikenan nayi sanadiyar mutuwar Mahaifiyata? Bakomai, bade ya rusa duk wani farin ciki na ba? Shikenan zan auresa.

Amma wallahi shima sai farin cikinsa  ya koma bakin ciki, zai aure ni saboda farin ciki to wallahi zai auri bakin ciki. Wayarta ta dauko tashiga rubuta ma Hafiz message tashiga fada masa abubuwan da suke faruwa.

Tana gamawa ta kara fashewa da kuka, ta dade ahaka kafin ta ta shi, ta wuce gida. Tana zuwa bakin gate ta iske 'yan gidan a waje da alama ita ake nema.

Bayan ta fito da gudu kannanta suka je suka rungumeta. Girgiza kai Umma tayi tabar wajen ta koma ciki. Jansu Na'ima tayi suka shiga ciki. A falo suka iske Umma, dukawa Na'ima tayi tana kuka.

Umma tace kukan me zakiyi mani kuma? Ba guduwa zakiyi ba waya baki shawara kika dawo? Cikin kuka Na'ima tace dan Allah Umma kiyi hakuri, wallahi laifin zuciyata ce dan Allah kiyafe mani.

Fahad yace Umma dan Allah ki yafe mata tunda ta dawo. Umma tace shikenan, naji dadi tunda har kika iya tunanin dawowa, kiyi hakuri Na'ima, wallahi da ace ba Wasiya Dr ya bar mani akan ki auri MD ba babu abinda zai sa na aura maki shi.

Insha Allah wata rana zakiyi farin ciki da Zabin Mahaifinki, nasan ayanzu zaki shiga damuwa, amma idan kika daure komai zai wuce. Kada ki boyema Hafiz, ki fada masa komai kada yace kin yaudaresa.

Na'ima tace wallahi bazan kara bata maki rai ba, na yarda zan auresa kiyafe mani Umma. Dafata tayi tace na yafe maki Na'ima, tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci. Allah yayi maki albarka.

Shigowar Hafiz kenan cikin gari,wayarsa tayi kara alamun sako yashigo. Dama tafiyar gaggawace ta kamashi zuwa kauye, gashi babu network acan shiyasa wayarsa bata shiga.

Yana dubawa yaga Na'ima ce. Murmushi yayi ya maida wayar aljihu yana fadin sai na kimtsa sannan zan karanta.

Bayan Na'ima tayi wanka taci abinci, suka koma falo ita da kaninta suna fira har Umman su, Na'ima daurewa dai ne take batason Umman su ta gane tana cikin damuwa ko kannenta da lokacin tausai suke bata. Umma ko sarai ta fahimce ta, amman batason ta nuna mata hakan, sun dade suna fira, zuwa karfe biyu, cousins din Dr suka zo da kudin neman aure da sadakin da yanuwan MD suka zo da shi, a cen gefen dangin Dr akayi tambayar auren.

Sun tsayarda rana, in Umma zainab ta kare wanka da wata daya,  Na'ima kuwa tunda suka shigo falon taja kannenta suka bar falon, tasan maganar MD ce ta kawo su, bayan sun wuce Umma ke mata bayanin abinda kenen tayi shiru, cikin jin nauyin Umman, tace duk abinda dangin mahaifinta suka tsara yayi, Umman ta kara yimata nasihar tayi ma haifinta BIYAYYA KO BAYAN RANSA, tasan zata ga ribar biyayyan.

Hafis kuwa, bayan ya natsue ne, ya dauko wayar don karanta sakon Na'imar cikin tashin hankali ya mike tsaye yace bazai yuyu ya rasa rayuwar sa ba, Na'ima ita  rayuwarsa, ya wuce dakin Ummansa cikin damuwa yace mata zai je zaria, tace masa lafiya cikin damuwa yayi mata bayanin Na'imar da yake bata labari, ta aiko masa cewa anyi mata miji aure zaa yi mata, Umman Hafis ta yi shiru cikin damuwa tace masa yayi hankuri, tunda har mahaifan yarinyar sun mata miji, ko yaje zaria meye amfanin zuwa, kuma yana da kyau, kayi ma mahaifanka BIYAYYA KO BAYAN RAN SU, ganin yabnda ya tadda hankalin sa, Umman tace yayi hankuri da safe  zasu je da mahaifinsa tare dashi, da kyar ya yarda goben su je. Bayan ya fita dakin Umman Hafis din tayi shiru tasan tabbas Hafis zai shiga damuwa don yasa yarinyar a ranshi,  zata yiwa mahaifinsa bayanin, in ya Amince suje zarian suji gaskiyar maganar.

A gefen MD kuwa duk da kudin auren da aka kai  gidan su Na'ima ya kasa samun natsuwa cikin zuciyarsa,  sai yake ganin riba me zai samu in ya auri yarinyar da bata son sa, ya sha daukan waya ya kira Ummu zainab ace wan yana son a bar maganar sai yaji ya kasa, Shehu hassan ya fada masa sai yayi hankuri komai zai wuce, yasan ko don Dr zai jure duk abinda zai je ya dawo, yayi ma alkawalin komai tsanani zai yi hankuri da Na'ima zai cigaba da addu'an Allah yasa taso shi kamar yanda yake sonta.

Hafis kuwa bayan Umman sa tayima mahaifinsa bayanin abinda ke faruwa, yace suje zarian ko don hankalin Hafis din ya kwanta, sun shirya zuwa zaria, da safe sammako sukayi, da wuri suka isa zarian, kai tsaye gidan su Na'imar suka wuce, ya kira num Na'imar bata shiga, daman tunda ta tura masa text ta kashe wayarta, har suka isa kofar gidan num bata zuwa, da fahad suka fara haduwa bayan sunyi parking, fahad yazo ya gaishe su, shine yayi ma Umman Hafis jagoran zuwa cikin gidan, cikin karamci Umma zainab ta tarbe ta, Umman hafis tayi mata bayanin tare suke da Hafis da mahaifinsa da dalilin zuwan su, Ummu zainab ta kira Fahad ya shigo da su Hafis din cikin falo, bayan sun gaisa an kawo masu abinci sunci Ummu zainab tayi masu bayanin wasiyyar da Dr ya bari har sadakin da aka kawo.

Tace masu tana son cika umurnin mahaifinta ne, bawai don bata son Hafis din bane, ko wace uwa tafi son takai yar'ta a inda take so, mahaifin mahaifin Hafis yayi ma Umma godiya sosai akan karamcin da aka yi masu,  daman aure mukaddari ne daga Allah, sunyi masu godiya sosai suka yi ma Umman sallama zasu koma kano, Hafis kuwa tun da suka fara magana yake zubar da hawaye, zuciyar sa na masa zafi, shikenen ya rasa Na'ima kenen, da kyar mahaifinsa ya jasa suka fita falon, Umma zainab kanta jikinta yayi sanyi, yaran sun bata tausayi.

Na'ima kuwa tana daki ta kasa fitowa sai kuka take yi, tsanen MD ya kara shiga zuciyar ta, ta sha alwashin sai yayi nadamar saninta rayuwarsa. Bayan sun fita falon ne, Hafis cikin kuka ya roki mahaifinsa da su barsa ya yi bankwana da Na'ima, Umman Hafis ce ta sake komawa cikin gidan tayima Umma zainab bayanin in zai yuyu Hafis yayi sallama da Na'ima, Umma zainab tace ba komai Ummi ta fada ma Na'imar a kofar fita wajen gidan Na'ima ta same su, ta gaida mahaifin Hafis, suka wuce mota suka barsu su gana, shiru sukayi suna kallon juna, Hafis ne ya daure yace wa Na'ima yana mata fatan alhairi, Na'imar kuka takeyi sosai ta kasa magana a haka Hafis ya juya ya wuce, Na'ima cikin kuka ta koma gida, duk kannen ta sun tausaya mata, Umma zainab daurewa take yi batason nuna ma yaran.

A gefen MD kuwa shirye shirye auren yake amman kasan zuciyarsa ya na tsoron abinda zaije ya dawo don ya hango kiyaryar sa a idon Na'ima, son ta kuwa kullun karuwa yake a ransa, a zaria zaa a kai Amarya kamin su wuce kaduna, kowa da gefensa ita da hindatu.

Muje zuwa.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now