BIYAYYA BAYAN RAI

452 31 0
                                    

BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸☘☘🌸🌸

NAH

🌸

UMMUN ASMA'U (SA'ADTU)

DEDICATED TO NABILAT ZANGO(LADY)

Bismilahi rahamanir rahim.

Page 30-35

Na'ima kuwa suna fitowa exams last paper su, project dai ya rage masu, take cewa maryam gaban ta take jin yana faduwa bata jindadin jikin ta su wuce gida, ta aje maryam ta dauki hanyar gidan su da ke zaria city, daman tun rasuwar mahaifiyarsu Dr bai bar ainihin gidan su ba, da baya ya sayi filin da ke kusa da gidan aka hade aka gyara gidan.

Tana shiga layin nasu ta hango mutane sun fara taru kofar gidan, cikin sauri ta isa kofar gidan, waje tayi parking, ta wuce ciki da sauri ganin mazan gwaggonin ta da da dangi mahaifiyar ta tasan ba lafiya, ta karsa cikin gidan, tana kiran umman su, jiyo kukan umman da kanninta yasa ta yi tsaye, autan umman ne ya zo ya rike ta, yana cewa yaya abban mu yayi hadari ya rasu, Na'ima ta fasa kara mai karfi ta fadi kasa, yaya sadiya sister Dr ce tazo ta ja ta zuwa cikin dakin mahaifiyarta, umma zainab naganin an jayo Na'ima ta kara fasa kuka, duk wanda ke gidan ya tausaya masu, kuka sukai mai cin rai, Umma zainab ta jayo wayar ta, ta shiga neman layin MD.

Yana tsakiyar aiki a office call din Umma zainab na shigowa, hakanen yaji gabansa ya fadi, da sanyi jiki ya dauki call din, yana cewa Assalamu Alaikum sai tace masa muhammadu yau mun rasa Dr, babu Dr, da karfi MD ya tashi, cikin tashin hankali yake cewa hello ta kashe wayar, da sauri ya dauki keys dinsa ya fito, masinjan na oga lafiya bai saurara masa ya wuce, ya kira abokin sa shehu hassan ya fadi masa, shehun yace su hadu su wuce zari'a.

Allah ne kurum ya kai su lafiya, saboda gudun da MD ke zubawa, shehun kan sa cikin tashin hankali yake yana tuna zuwan sa wajen Dr.

Koda suka isa ana shirin kai Dr makwancinsa, fahad naganin MD da gudu yazo ya fada masa yana kuka, MD kuka ya fashe da shi, mutanen da suka san alakar MD da Dr sun tausaya masu, shehu ya kira yan gidan su MD da nasu gidan duk ya fada masu, jamma'a da dama ne suka raka Dr makwancin sa, mutane da yawa suna fadin alhairin sa.

Bayan an dawo ne mazan suka shiga cikin gidan don yi masu gaisuwa, MD da yan gidan su da suka zo da yan gidansu shehun suka shiga, sun shiga wajen ummu zainab, MD kasa magana yayi sai kuka, Ummu zainab naganin sa tasa kuka, mutane ke ta basu hankuri cewa yanzu addu'ar su yake nema.

Haka aka cigaba da zaman makoki har akayi sadakan ukku, lokacin kowa yaga iyalain Dr zai tausaya masu, har Na'ima da mahaifiyar ta, duk sun rame, maryam gidan su Na'ima tavdawo tana bata baki, ita ma mutuwar ta shigeta.

MD hutu ya dauka office ya dawo zaria, gidansa dake GRA, ba yanda baiyi da Hindatu tazo taki, cikin yayi hidama sosai an aje abinci har abin sha.

Da akayi sadakan ukku ne, ranar da zai wuce ya shiga don yima ummu zainab sallama a falo ya taradda su da yan uwan Dr, Na'ima da maryam na gefe zaune, yayi masu sallama zai wuce, har ya mike Ummu zainab tace masa in an kwana biyu akwai maganar da takeso yazo zasuyi, ya insha Allahu in an kwana biyu za dawo ya masu sallama ya wuce.

Na'ima ta jinjina meyasa umman su keson ganin Mutumin nen ko yana bin mahaifin su kudin bata kawo komi a ranta ba, ummu zainab, cikin damuwa take ga rashin Dr ga wasiyar da ya bar mata, abinda ke damun ta, zuwan Hafis da mahaifan sa gaisuwa da sunen mane min Na'ima,
ina zata fara kuma ta fahimci Na'imar na son sa, ta yanke shawara zata tara dangin Dr ta fada masu abinda kenen.

Washe gari, Umma zainab tace ma sadiya da Aisha yayu Dr akwai maganar da takeson suyi, sadiya tace yana da kyau in abinda ya shafi Dr ne su kira kanin mahaifiyarsu da kanin mahaifin su, tun da duk suna raye. Bayan duk sun halara ne ummu zainab tayi masu bayanin wasiya da Dr ya bar mata, kamin Allah yayi mashi cikawa, sunyi shiru na wani lokacin kamin kawu Abdullahi yayi gyaran murya yace muhammadu bazai zafa Na'ima abinda yasa zata cutu ba, saboda haka ya zama dole a cika masa kudirin sa, kuma yasan Na'imar bazata ki, abinda mahaifin ta ya zafa mata ba, yasan zatayi masa BIYAYYA BAYAN RAI, yace ma su sadiya ko akwai mai magana sukace suma suna bayan maganar danuwan su, ya juya wajen dayan kawun nasu shima yace hakan zaa yi, sun yake shawaran su sadiyan su kira Na'iman suyi mata bayanin abinda kenen, amman sunce zasu barsa har ayi sadakan arba'in dai hankalin Na'ima ya kara dawowa jikin ta.

MD kuwa bayan ya bar zaria yake tunanin ganin da Ummu zainab keson masa, bayan ya isa zaria ya kira shehu hassan yana masa bayani, shehun yace ya kwantar da hankalin sa, zai yuyu Dr ya fada mata ne. A haka sukayi sallama, kwanen biyu MD cikin tunani yayi su Allah yake kwana biyun yayi, bayan kwana biyu MD ya shirya zuwa Zarian, sayayya sosai yayi, tun kan abinci har sabulun wanka, ya isa gidan ana kiran laa'asr ya fitar da kayan ya bawa maigadin ya wuce masallaci, bayan ya dawo ne, ya shiga cikin gidan sun gaisa da ummun tare da kara yima ta gaisuwa, tayi masa godiyar kayan da ya kawo, tana cewa hidimar yayi yawa, yace ba komai albarka ta yake nema. Sunyi shiru na wani lokacin kamin ta kirasa muhammadu ya dago kansa tace Kamin Allah yayi wa Dr rasuwa, ya fadamin ka aiko masa kana son Na'ima da aure, tace ya bar wasiyyar ko bayan ransa a aura ma Na'ima, nayi ma dangin mahaifin ta bayani, sun aminta da wasiyyar sa, sunce haka zaayi, sai dai zasu ba da lokaci kamin suyi mata bayanin abin da kenen, ka bada lokaci kadan ka turo magabatanka don a tsayar da rana, tun da ta kammala karatun ta. MD da ji abin kamar a mafarki, yayi hamdala a ransa, cike da girmamawa yace umma kina ganin ba matsala gefen Na'iman, Umma tayi jim na wani lokacin kan tace bana tunanin haka saboda bana tunanin Na'ima ta tsallake ummunin Dr, yayi mata godiya sosai, sunyi sallama da Alkawalin in anyi sadakan Arba'in zai turo magabatan sa.

Bayan wasu kwanaki akayi sadakar arba'in Dr anyi addu'oin sosai, bayan ankare sadiya da Aisha suka kira Na'ima a dakin Dr, sun mata nasiha sosai kamin su fada mata wasiyyar da mahaifinta ya bari, Na'ima cikin tsananin tashin hankali ta mike tsaya, tace wallahi bazan yi ba, Abban mu bazai ce haka ba, ina wanda nake so ta fashe da kuka mai tsanani, Ummu zainab dake falo tana kai tana komowa tasan zaa rina, don ta lura ko kadan Na'ima bata son ko maganar MD, kamar su ummi da suka mayar da shi dan uwa.

Sadiya ta jawo Na'ima cikin sigar lalashi tace kiyi hankuri Na'ima Dr bazai tafa baki abinda yasan zai cutar dake, Na'ima kuwa sai kuka takeyi tana cewa bazata yi ba, karya ake ma mahaifin ta, Ummu zainab ta shigo cikin dakin ta zauna tace ma Na'ima tabbas abinda gwagwanin ki suka fada haka yake in mahaifinki ya barma wasiyya, Na'ima cikin kuka tace Abbana bazai min haka ba gaskiya ne ba, ummu zainab cikin bacin rai tace wazai maki karya in ko gwaggo in ki, to kiji da kyau aure da MD anyi ankare, don baki san ciwon kan ki bazakiyi wa mahaifinki BIYAYYA BAYAN RAI? Mi ya rage ku da shi wane irin gatane bai baku ba. Cikin bacin rai ta fita daki, Gwaggonin ta ne, suka ciga ba da bata magana ganin ta kiya su ma suka mike cikin bacin rai suka tabbatar mata sai sun cika wasiyyar kanin su.

Muje zuwa

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now