BIYAYYA BAYAN RAI

348 8 0
                                    

🌸🌸🌸☘🌸🌸🌸

BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸🌸☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU AS'MAU(SA'ADTU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LADY)

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 30-35.

Washe gari Na'ima tana daki tana kuka har 'yan uwan Abbanta suka tafi bata fito ba. Umma kuma taki shiga dakinta saboda tanajin haushin abinda tayi jiya, duk da tana tausayinta amma tana ganin meyasa bazatayi hakuri ta karbi zabin Mahaifinta ba.

Fahad ne yazo kusa da Umma yana fadin Umma dan Allah kiyi hakuri, wallahi bama jin dafin gidan gaba daya. Gashi babu Abba, ke kuma kina cikin damuwa. Ga Yaya Na'ima itama tana cikin damuwa.

Meze hana Umma ki bari ta auri wanda takeso tunda Abba baya raye, kuma shima besan akwai wanda takeso ba da baze zaba mata MD ba. Murmushi Umma tayi tace Fahad kai yaro ne, baza fahimci abinda muka hango ba.

Na'ima da wanda takeso class mate ne, taya kake tunanin aurensu zeyi karko bayan su duka yara ne? Amma idan ta auri Md zataji dadi saboda yasan gidansu, baze taba wulakanta taba.

Badan kudinsa yasa mukeson ta auresa ba. Saboda nagartasa yasa mukeso ta auresa. Ko bayanzu ba ni nasan Na'ima zatayi farin ciki da zabin mu. Tabbas nasan akwai ciwo rabuwa da masoyi amma kuma idan tayi hakuri zataci riba.

Fahad yace haka ne Umma. Amma dan Allah kidena fushi da ita, kinga zafin zai hade mata biyu. Umma tace shikenan Fahad, bara naje na sameta. Tashi tayi ta nufi dakin Na'ima.

Kwance take tana ta kokarin kiran wayar abun sonta amma taki shiga. Bude kofar dakin ne yasa ta aje wayar tare da tashi zaune. Umma ta gani a tsaye. Dukar da kai tayi tana fadin Umma ina kwana? Umma tace daban kwana ba ai bazaki ganni ba.

Wato daban shigo ba kinfi karfin kije ki gaisheni ko?? Bakin da suke gidan ma basu isa ki gaishe su sai kin nuna masu yanzu wuyanki yayi kwari, saboda babu Dr, yanzu ban isa dake ba.

Kinyi dai dai, duk abinda kikayi dai dai dake ne. Idan nima kika sa mani hawan jini aka wayi gari zuciyata ta buga kinga sai na bar maki duniyar ki auri wanda kike so. Kuka Na'ima tasa ta duka tana bama Umma hakuri.

Zama Umma tayi tare da rage murya tace haba Na'ima, kina tunanin zamu zaba maki abinda zai cutar da kene? Tunda har kika ga Dr ya zaba maki miji kinsan akwai abinda ya hango. Meyasa bazaki amshi zabinsa ba domin ki samu albarkarsa.

Cikin kuka Na'ima tace dan Allah Umma ki janye wannan maganar, wallahi bana son MD, akwai wanda nakeso. Umma idan ban auresa ba mutuwa zanyi muna son junanmu. Kuka me karfi tasa.

Murmushin takaici Umma tayi tace shikenan Na'ima tashi ki shirya kitafi makaranta kada ki makara idan kika dawo zamu karasa maganar. Amma inaso kisa aranki, matukar nice na haifeki bakida miji sai MD

Tashi tayi ta fita. Sosai Na'ima tasha kuka kafin tashiga wanka. Tana fitowa mai da turare kawai tasa tashirya ko karyawa batayi ba tayima Umma sallama ta fita zuciyarta tana mata zafi a haka ta nufi makaranta.

****** ******

CIGABAN LABARI

Na'ima tana barin wajen Maryam motar ta ta nufa ta bar makarantar zuciyarta tana cigaba da bata shawara akan taje ta hada kayanta tabar garin kawai, idan komai ya lafa sai ta dawo. Tana isa gida dakin su ta wuce, ta kwanta tana tunanin, yanda zata bar gidan, ta jawo wayar ta, ta kira num Hafis, still num baya zuwa damuwan bai fi miya samu wayar sa ba, kuma bai zo school yau ba, ko sun kare final exams din su, tasan shima bai yi submittin project din sa ba. A haka Ummi sister ta shigo dakin tace Umman su tace a fada mata, MD zai zo, zasuyi magana, don bayan fitar Na'iman makaranta, Shehu hassan ya kira Umman a cewa zasu don MD ya gana da Na'ima don bayan gaisuwa basu tafa haduwa sunyi magana ba, Na'ima shiru tayi batace wa ummin komai ba, da ummin taga shirun yayi yawa ta wuce abinta.

Taje ta fadawa Umman cewa ta fada mata, su kansu yaran gidan abin na damun su, ga rashin  abba ga rigimar da takuno na auren yayar su, ba wani shiri da Na'imar tayi don zatayi bako, Umman dai ce tasa akayi masu girkin abinci da abin sha.

Bayan sallar la'asar ne MD da Shehu sukayi parking a kofar gidan Dr,
Maigadin gidan ne ya fadawa Umma zuwan su,  bayan sun shiga falon Umma tasa an fitar masu da abinci da abin sha, ta leka dakin su Na'iman ta fada mata ga MD nen yazo in zata nuna masa bata tarbiya ne bismillah, ta wuce ta barta, tafi mintuna goma kafin ta tashi toilet ta wuce ta wanke fuskan da kukan da tayi idon ta duk yayi ja abinka da fara mace, powder ta shafa da kwalli , bakar jallabiyace jikin ta, mayafin rigar ta yafa ta wuce falon, da sallama ta shiga, MD sai da gaban sa ya fadi, Na'iman ma taji faduwar gaba da suka hada ido, shehu ne ya amsa sallama a hankali ta shiga cikin falon nesa dasu ta zauna, ta duka kanta kasa ta gaishe su ciki ciki, still shehun ne ya amsa ta din MD duk jikin shi rawar yake, ya rasa wane irin so ne yake ma Na'ima ko sunen ta yaji zai ji faduwar gaba.

Shehu ya kara yimata gaisuwan Dr, ya  dan jata da fira da tambayar ta, game da karatun ta, ta amsa ba yabo ba fallasa, shehun yace MD zai je ya dawo. Bayan shehun ya fita sun yi shiru dukkan su kowa da abinda yake sakawa, MD ganin shirun bazai yi ba, yayi gyaran murya kara yimata gaisuwan Dr da tambayar ta ya gida da fatar ba wani problem?ta yi shiru bata ce masa komai ba, ya kara tambayar ta karatu nen ma shiru bace komai ba, yayi ta magana ta ki cewa komai, cen shima yayi shiru da ma MD ba gwanin magana ne ba, a hankali Na'ima ta dago kanta tace masa ita fa tana wanda take so, bata son sa kuma bazata tafa son sa ba, kuma ba wata BIYAYYAR da zatayi BAYAN RAI don tasan mahaifinta bazai ce dole sai ta aureshi duk shirin Umman tane da gwaggonin ta.

MD da tunda tafara magana gabansa yaci gaba da faduwa ya tsura mata ido ya bala'in jin sonta cikin rasan, gashi gaba da gaba tace bata son sa, in ko har bata son sa gara ya hankura da nashi son, tana gama fadi ta fita falon. Ya bita da idanu  har ta bace ma ganinsa, ya mike da shirin barin falon, Ummi tayi sallama ta shigo tace Umman su tace a fada tanason magana da shi, ya koma ya zauna,  Umman ta shigo kenen Shehu ya dawo har zai fita tace ya shigo mana, ya shigo falon sun gaisa cikin girmamawa, ta ce ma MD tana son kwananen ya turo magabatansa, suje wajen yan uwan Dr tana son a tsayarda magana, MD yayi shiru na wani lokacin kamin yace ko zaa kara ba da lokaci su fahimci juna shida Na'ima don baya son a yi mata dole, Umma zainab tace ai ba maganar dole ne ba, maganar yiwa mahaifinta BIYAYYA ne ko BAYAN RANSA, kuma da yarda Allah yanda Dr ce haka zaa yi yaje ya tura magabatan sa wajen dangin mahaifin ta. Umma tayi masu sallama ta koma cikin gida a haka sunka fito gidan MD da duk jikin sa yayi sanyi, bayan sun shiga mota ne yake ma shehu bayanin yanda sukayi da Na'ima  yace ma shehu ya zaiyi, shehun yace ya kwantar da hankalin sa da yarda Allah komai zaiyi dai dai, duk kiyayar da zata nuna masa na wani lokacin ne yasan komai zai daidai ta shawara daya zai bashi yayi hankuri, shehun yace su wuce wajen kannen baban MD don suyi masu bayanin zuwa neman auren.

Na'ima kuwa dakin su ta wuce cikin bacin rai, ta tsanin mutumin tun farkon ganinta da shi, ashe da rabon zai zame mata matsala rayuwar ta,    ranta ya kara baci da jin umma ta aika su jira tayi magana da su, fahad ne ya shigo dakin yace yaya magana zamuyi don Allah ki kwantar da hankalin ki, kiyi abinda Umma keso nasa bazata cutar dake ba, ckin fada ta tasowa fahad ya wuce ya bata guri ko ta mare sa, cikin kuka ya fita dakin Umma zainab da ke jin duk abinda ke faruwa, cikin bacin rai ta shigo dakin ta fara Fada cikin bacin rai, tacewa ko mutuwa zatayi sai dai akai gawanta gidan MD. Ta fita dakin cikin bacin rai ranar duk yaran gidan kowa sai da yayi kuka.

Har dare gidan shiru abinci ma duk yaran basu ci ba, Umma zainab kuwa duk abin duniya ya taru yayi mata yawa ga rashim Dr ga bakin cikin da Na'ima ke sa mata, bata tafa tunanin akan son wani diyar da take ganin ko layi ta zana baza tsalaka. Ranar tayi kuka har kanta ya fara ciwo, ta kira baban yayansu akan tanason ganinsa, gara ayi ma Na'ima aure ta huta.

Na'ima kuwa ta sha alwashi yau zata gudu ta bar gidan, ta hada kayanta kala biyu a hand bag, Atm din dai ta dauka, don duk wata Dr na tura mata kudi don makaranta da wasu bukatun, ta kira num Hafis stil bata zuwa, ta yanke, ta kwanta da tunanin lokacin subahin zata gudu abinta, da kyar bacci barawo ya sace ta, 4:30 ta farka, daman ka'idan gidan Dr ne yaran na tashi kamin lokacin subahin suyi nafiloli da karatun qur'ani, akwai masallaci a kofar gidan, su fahad suna zuwa sallar subahin masallacin kofar gidan, tayi arwala ta dade tana nafilolin da suka saba yi, tayi subahin tun kamin masallacin su tadda sallah don tasan Umman su jam'ie take bi, bayan taji an tadda sallah a hanakali ta fita dakin su ummi duk suna dakin Umma sunbi jam'ie, ta kofar baya ta fita, ta lafe sai da akayi sujada sannen ta bude get din a hankali ta fice gidan.

Muje zuwa.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now