BIYAYYA BAYAN RAI

591 37 0
                                    

BIYAYYA BAYAN RAI 15-20

NAH

UMMU AS'MAU(SA'ADATU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LEADY), NAGODE TAWAN

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 15-20

Wannen pagen naku ne Diyar katibi, maman waleed, Allah ya bar zumunci.

Bayan MD ya koma gida
tunanin Na'ima ya tasoshi gaba, adaren sam kasa bacci yayi daya rufe idanuwansa ita yake gani.

Abu kamar wasa yana kwance yaji kiran sallar farko, da kyar yatashi yayo alwala ya fara sallah. Bayan yadawo daga masallaci yadan kwanta nan bacci ya daukeshi, acikin baccin ma mafarkinta yayi.

Zaune Hafiz da Na'ima suke asaman wasu kujeru bayan fitowarsu daga lectures. Hafiz yace dear kinga yanzu muna aji 3, yakamata ace zuwa yanzu agidanku asan da zamana, koba komai idana muka gama karatu bazamu sha wahalar sanar da Iyayenki maganar auren ku ba.

Na'ima kinsani babu wata mace da nakeso sama dake, duk wata rayuwata ta nan gaba na shiryata ne dake, idan har na rasaki ban san wane hali zan shiga ba. Dan Allah kada kibari wani yazo ya kwace mani ke.

Murmushi tayi tana fadin kaima kasan agidanmu ba'a barina kula kowa, taya kake tunanin wani zai zo ya kwace maka ni. Abbanmu baya zaba ma,mace abinda yakeso.

Shi mutum ne mai bama kowa 'yancinsa, hatta da biro idan zai saya maka sai wanda kakeso, sam baya tauye mana ra'ayinmu. Kada kayi tunanin Abba zai zaba mani wanda zanyi rayuwa dashi. Kawai ka kara bani lokaci mu shiga final year nasan Abba zai amshi maganata tunda yaga munzo karshe, nasan zai yarda da maganar mu, Hafis yace shikenen tunda kince haka, amman in wani lokacin sai nayi ta mafalkin wani yazo da jirgin sama ya dauke man ke. Na'ima tayi dariya tace haba, mafalki ai baya zama gaskiya, a haka Maryam ta taradda su, tana dariya tace romio an juliet, Na'ima ta tashi tsaye
tana fadin aike nake jira mu wuce gida, sukayi sallama da Hafis suka wuce.

Bayan wasu watanni shaquwa ce mai karfi ta shiga tsakain Dr da MD har ma da family both side, ko aure ake a family Dr zai gayyaci MD haka MD zai gayyaci Dr, suna waya sosai zuwa lokacin MD ya kare master programme dinsa dama 1yr ne,Dr kan shi yayi mamakin basira MD don result din shi yayi kyau sosai, haka son Na'ima ya yi yawa a zuciyar MD, basan ya zai tunkare ta ba, ko ya zaima Dr maganar, so dayawa in yaje gidan bai cika samun ta ba, wani zubin ko tananen da sun gaisa zata wuce ta barsa da kaninta, yayi sabo da su fahad sosai, duk zuwan da yayi gidan da kallar tsaraban da zai masu, Na'ima haka nen haushin MD take ji, sai tace ya cika shishigi shi ba danuwansu amman komai na family da shi ake, ko yaushe ta gansa sai taji gabanta na faduwa.

A gefe daya Dr kullun ayyana yake ina ma MD zai neme auren yar sa, har ga Allah MD ya kwanta masa, ya binciki family sa sosai, mahaifinsa dattijo ne, mutunin kirki,  sai dai yasan bazai yuyu shi ya fara yi masa maganar yar sa ba, haka rayuwa ta cigaba da tafiya, zumuncin su yayi karfi sosai, MD son Na'ima na ta cin sa yakasa neman mafita, rashin kunyar da Hindatu keyi masa sai abinda ya ci gaba, daman shi ba mutunin hayaniya bane. Abinci gidan ko yaushe yar aiki keyi, yaran komai mai aiki ke masu, har gefen mai gidan yar aikinta ke gyarawa, bata lokacin komai sai biki da yawon kawaye, mai gidan in ta je makwancin sa, tana bukata da shi, ko kudi ko tace tazo a bata hakkinta,  haka zaman yake duk hindatu tayi masa abin arziki, to akwai abinda take so a wajen sa har ya saba da hakan, yan uwansa ba wani dogon hulda tsakanin ta dasu.

Bayan shekara daya lokacin su Na'ima sun shiga level four, soyyarsu da Hafis yayi nisa, har daya na gani baya iya rayuwa batare da yan ba. Haka son Na'ima na Azalzalan MD ya kasa fada mata. Akwai watarana ya shiga zaria da yammah, kai tsaye gidan Dr ya wuce, yayi parking wajen gidan ya shiga cikin harabar gidan yana shiga da Na'ima ya far haduwa tana wajen kan kujeren dake harabar gidan tana rubuta project dinta, tunda ta dago taga mai sallama yana shigowa ta hade fuska, ciki ciki ta gayar da shi, ya amsa cikin sakin fuska, gabansa na faduwa don bai zaci da ita zai fara haduwa ba, kai tsaye falon gidan ya shiga da sallama, su ummi kanen Na'ima na zaune, da fara'a suka tarbe sa, ummu zainab tace muhammadu ne sannu da zuwa ya duka har kasa ya gaida ta, sun tafa fira yace Dr fa tace yana evening lecture yaje makaranta, amman nasan bayana nesa zai dawo, yace daman na shigo gari ne nace bari inzo mu gaisa, ya tashi yana cewa a gaida shi zan wuce, ya kira fahad ya basa kudi ya bawa umman su, ya na fitowa sukayi karo da Na'ima zata shiga falon, da sauri taja baya, shiko ya tsura mata ido, ya yi seconds yana kallonta, gabansa na faduwa, a fito falon a hanakali ta wuce ciki.

Fahad ne ya dawo da kudi yace umma tace bata karfa mata, MD yace ka maida mata, kace albarka ta nake nema matsayinta na uwa, yace fahad level nawa yayar ka take fahad yace final year take, su zasu kare wannen shekara, MD yace to in Dr yazo ka gaida shi zan wuce. Bayan ya bar kofar gidan ya fara tunanin mafita kamin garin kallon ruwa, yarasata, babban abokin shine ya fado masa a rai, Shehu hassan zai ne me shawaran shi.
Abinda MD yaje yi a zarian bai yi haka ya dauki hanyar kaduna cikin mintuna arba'in da biyar ya isa kaduna kai tsaye, gidan Shehu hassan ya wuce, friend dinsa ne tun a secondry school shi ma shehun dan zaria ne, kaduna yake aiki banker ne. In akwai wanda yasan halin MD bayan shehu yake, so dayawa wayanda suka san su, suna mamakin abotan su, don Shehu ba raini yana da zafi sosai in an tabo sa tun a makaranta, so dayawa shi ke shige MD fada lokacin suna secondry school, ko ya yake neman MD baya zuwa gidansa, ya tsanin halayen Hindatu, yana mamakin wane irin rayuwa ke ga MD da bazai daukar mata mataki ba, Hindatun haushe Shehu take ji, tana ce masa munafiki, basa shiri ko kadan, matar Shehu bata hulda da Hindatu.

Ya isa cabalar road unguwar gidan shehu, yayi hon maigadin ya leko, ganin motar MD jiki na rawa ya fito don MD ba dai Alhairi ba, ya rusuna yana kwasar gaisuwa, MD yace maigidan na nen ko, kamin mai gadin ya yi magana. Suka ji hon waje alamun mai gidan ya dawo, bayan shehun ya shigo ciki da fari'a ya tarbi MD yana cewa ya baka shiga ciki ba, MD yace isowa na kenen ka dawo, yace to bismillah, suka kara sa cikin compound din gidan, MD yace mu tsaya a waje maganar da nada muhimmanci, su ka karasa wajen round hot din dake cikin compound din suka zauna, MD yayi shehu bayanin halin da yake ciki na son Na'ima amman bai san yanda zai tunkari Dr da maganar ba,  Shehu yayi hamdala yana cewa wallahi naji dadi abokina kuma nasan Dr zaiyi farincikin haka, don Shehu ya san Dr saboda M,   kuma atlist ko bazaka iya rabuwa da Hindatu ba, don BIYAYYA BAYAN RAN Alhajinku, zaka ji saukin matsalolin ta, Shehu yace mafita daya ce muyi magana da Dr kamin mu yi ma yarinyar magana, in zanje  zaria goben, don ko yau ba dan dare yayi da yau zan je. Amman gobe da yarda Allah zanje nayi masa bayanin abinda kenen, kuma ka kwantar da hankalinka har na hango Na'imar ta zama taka MD yayi dariya, Shehu yace naso ganin yarinyar ta cira tutu tun muna secondry ban tafa jin kace kana son mace sai kanta, kiran sallar da aka fara ne, yasa mikewa don zuwa masallaci.

Bayan sunyi sallah sun dawo, suka shiga falon gidan,  Shehu ya wuce ciki yana ce ma matar Samira tazo ga MD, ta fito suka gaisa da tambayar su Nuwaira da maman su, yace duk lafiya suke, bayan sun kare fira MD ya wuce gida da alkawalin Shehu zai je wajen Dr goben.

Muje zuwa

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now