BIYAYYA BAYAN RAI

460 14 0
                                    

☘☘☘🌸🌸🌸

BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸🌸☘☘☘

NAH

☘☘🌸🌸🌸

UMMU ASMA'U (SA'ADATU)

dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi Rahamanir Rahim.

Page 65-70

Last page.

Koda Md ya dawo

Hindatu bata dawo ba, haka yshiga yaci abinci shida Na'ima, suna zaune a falo suna fira

yaji karar motar ta, ya tashi yayi yace ma Na'ima yana zuwa. Bakin kofar gida yaje ya tsaya.

Haka tafito tana ya mutsa, ta gefensa tazo wucewa ko,kallonsa batayi ba ta rabe zata wuce. Da karfiya fisgota sosai ta tsorata ganin yanda ta kusa faduwa. Daure fuska tayi tana fadin meye haka? Fuska adaure Md yace ina tunanin nan gidan beyi maki kama da gidanku ba.

Duk duniya agidan Iyayenki ne kawai zakiyi abinda kija ga dama domin can ne kike da iko dashi. Saboda haka kamar yanda kika fita ina so ki juya ki tafi gidanku, sai na neme ki, tayi shewa tace ai ka kasan in ka isa ka sake in mana, gidan kuma na barsa har abada, md kuwa taikaici kamar ya kashe sa, badon BIYAYYAR mahaifinsa tabas da yau zai saki Hindatu, but ko yanzun zai kyaleta sai gidan su sun nema mata sakin da kansu, cikin bacin rai yace.

Kuma idan zaki shiga ki dauki kayanki na baki mintuna biyar ki bar mani gida.

Nagode Allah duk cikin yarana babu wanda ba'a yaye ba, dan haka bana son ki daukar mani yaro ko daya saboda anan kika samesu. Cike da masifa tace sai me. Dama taya za'a kawoni ni daya sannan ka koreni na tafi da nauyi gidanmu.

Allah nagode maka da ba'a daji ka dauko ni ba, kai kanka kasan muna da gida. Kuma mintuna biyar sunyi mani yawa. Butulu kawai. Rabasa tayi ta wuce. Na'ima da side dinta sama sama take jin hayaniya, jin abin yayi yawa yasa ta bude tagar falon ta, ganin yanda Hindatu ke cin mutunci Md gaban maigadi da masu hindimar gidan kasa motsi tayi, Na'imar fitowa tayi da niyar ta basu hankuri.

Haka Hindatu da kwashi kayanta na sawa tarika fitarwa har ta gama, ko,kallon Na'ima batayi ba ta wuce. Rufo kofar Md yayi ransa abace ya kama Na'ima suka shige side din dama Yara suna makaranta. Bata hanasa kanta ba saboda tasan ransa abace yake, sosai ta dage wajen faranta masa rai har sai da ya manta da wani bacin rai.

Kasancewar Na'ima Ummanta ta koya mata yanayin zaman gidan miji musamman idan kana da mata yasa sam bata tambayi Md abinda ya faru ba, domin Ummanta tace idan kana da kishiya dan kaji sunyi fada da mijinku kada kace zaka ria zakewa kana tambayar abinda yafaru.

Matukar ba shine yayi maki maganar ba to kada ki tambayesa, kiyi kokarin kyautata masa, idan kuma yayi maki maganar kada ki sake ki fada masa muguwar shawara domin alokacin zai kara gwada kyawun halinki.

Wannan dalilin ne yasa Na'ima batayi masa maganar ba, ita dai tana kokarin faranta masa rai. Lokacin da Yaran suka dawo haka suka zauna ta sa masu abinci sukaci tayi ma kananan wanka sukayi ta wasa, ko takan Mamarsu basu bi ba.

Da Md ya dawo sosai yaji dadin yanda yaga Na'ima taja Yaran ajiki, hakan yasa hankalinsa ya kara kwanciya dan yasan ko ya rabu da Hindatu har abada Yaransa bazasuyi kuka ba.

Mahaifiyar Hindatu tasan kome yake faruwa na zaman aurenta, hakan yasa datazo ta fadi karya da gaskiya tacce

Allah ya kyauta sai taje ta share dakinta ta zauna, Allah ka zaba abinda yafi alkhairi.

Mamanta tace in dai gidan ne gaki gashi ita Hindatun taji dadi, hakan yasa tashige daki hankalinta kwance ta cigaba da hidimarta, dan tace bazata koma gidan Md ba.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now