BIYAYYA BAYAN RAI

463 31 0
                                    

🌸🌸🌸☘☘☘
BIYAYYA BAYAN RAI
☘☘☘🌸🌸🌸
NAH
☘☘🌸🌸

UMMU ASMA'U (SA'ADTU)

Dedicated to Nabeelat zango (lady)

Bismillahi rahamanir rahim.

55-60.

Da karfi Na'ima ke kwankwasa kofar bedroom din Md, lokacin yana kan sallaya ya kare sallah cike da mamakin me ke faru, ya je ya bude kofar, d Na'ima ce tsaye jikinta sai rawa yake yi
cikin kuka take cewa.
DonAllah kayi hakuri kada kace zaka sakeni, wallahi na yarda zanyi ma Abbah BIYAYYA, zan zauna da kai har kashen rayuwata, zan baka duk wata kulawa da kake bukata, wallahi yanzu ina sonka.

Runtse ido MD yayi wasu hawayen farin ciki suka gangaro masa, hannu yasa ya dagata yana fadin ya isa haka, kije daki ki kwanta zanyi tunani kafin safe, juyawa yayi ya rufe kofar tare da jingina yana hamdala ga Allah.

Yaso ace yashigo da ita ya lallasheta, amma yayi hakan ne dan yakara tsorata ta. Na'ima kuwa gaba daya hankalinta tashi yayi dajin abinda Md ya fada, ta dade awajen kafin ta koma daki. Alwala tayi ta fara sallah tana rokonAllah yasa kada Md ya saketa gobe.

Da safe Na'ima kicin ta shiga ta hada md hadaden breakfast, kamshi ne ta ko'ina ta gyara gidan ta saka turarunk wuta da na ruwa oily ones ko'ina gidan sai kamshi ke tashi, bayan ta kare aikin, wanka tayi ta dade tana kwaliyya don rabon tayi irin wannen kwaliyyar tun kan maganar auren ta da md ya tashi, ta shirya cikin dark purpule boyel jakad sikit an bulawus sun fito da sharp din ta sosai, falo ta wuce ta zauna don cike take da tsoron wane mataki md zai dauka a kanta, ko zai sake ta ne, don tasan iya rashin mutunci ba kallar da batayi misa ba, tabbas tayi kure rayuwar ta, amman zata gyara in har md bai yanke mata hukunci sallamar ta.

Cike da tunanin me zaije ya dawo take zaune falon, idanunta na kan kofar bedroom din sa, md kuwa cike da farin ciki yake shirin zuwa office, ya matsu ya fita dole zaije ya ba shehu labarin abinda ke faruwa.ya fito cikin shirin zuwa office yana fitowa suka hada ido da Na'ima da sauri ta mike tana ce masa ina kwana, ya amsa cikin dan daure fuska, bayason ya saurin sakin jiki da ita yana son ya fahinci da gaskiya ne ko akwai abinda take nufi, tace masa akwai abinci table, kamar yace aa sai dai yace ok, abin Na'ima batasani tun fitowar shi kwaliyyar ta, ta tafi da imanin shi, tayi mai kyau kamar ya hadiye ta sonta ko yaushe karuwa yake cikin zuciyar sa, ganin yake yi yafi kowa sa'a a duniya, table din ya wuce yanda ta tsara table ya birge shi, dan baka saba mijin Hindatu😀, ya bude hadadun warmers din fry patotos ne da kwai, farfesun kaza da kunun tsamiya, ya diba abincin kadan ya fara ci, wani test ya ziyarci bakin sa, abincin yayi masa dadi, ya kara hamdala wajen Allah. Na'ima gefensa ta zauna still a dare take, sunyi shiru shi yana aikin kallonta ita kuwa ta kasa hada idanuwanta dashi, ya kusa gama cin abinci yace mata bazata ci abincine ba, tace ta koshi, ya aje spoon din yana kallon, kuka ne ya kubce mata, tace masa tasan tayi kure but tana rokon sa da ya yafe mata, tayi alkawalin zatayi wa mahaifinta BIYAYYA BAYAN RAYUWAR SA. Md hamdala yake cikin ransa, yayi shiru yana sauraren ta, yana ayyana abubuwa da yawa a rayuwarsa tabbas maharkuci mawadaci, sai da ya kammala cin abinci, ya mike tsaye, yace zai je office ta sake tunani kamin ya dawo bayason ya tauye mata hakki, in har yanzun tana son Hafis shi zai iya sawaka mata ta auri zafinta, ya tsura mata ido ya ga reaction din ta, kuka ta kara ace tana son sa ya yafe mata, ya wuce yana cewa ta dai yi tunani,  har zai fita falon ya jita bayansa tana cewa ya kawo brifcase din, zata raka shi, ya mika mata suka fito side dinta, a harabar gidan suka hadu da Hindatu, zata fita, Na'ima mamaki ne ya kamata, ina zataje da safe haka lokacin taran safe ba ma'aikaciyar gwannati ba.

Na'ima ce ta fara gaidata, ko kallon su Hindatu batayi ta wuce abinta, tana tsuki, abin yayiwa Na'ima ciyo, md kuwa bai yi mamaki don yafi kowa sanin halinta, har baki mota ta rakashi tare da yima sa a dawo lafiya, sai da ya fita get ta koma cikin side dinta tana mamakin halin Hindatu daman haka takeyi ma mijinta, lailai tayi kure wato su biyun ba inda yake jin dadi, wayar ta dauka ta kira num Ummanta, ring daya ana biyu ta dauka, sun gaisa Na'ima ta sa kuka tana rokon Umman ta yafe mata, ta tuba hamdala Umma zainab tayi tace ta yafema ta, tayima mijinta biyayya Allah yayi mata albarka sun dade suna magana kamin suyi sallama, ta nemo maryam cikin kuka take fada mata abinda ya faru da mafalkin abbanta da tayi, maryam tayi murna sosai da kawarta ta gane gaskiya, sun dade suna tataunawa yanda Na'imar zata jawo hankalin md, maryam tace ta kwantar da hankalinta tasan md bazai iya sakinta ko don abbanta, sunyi sallama, Na'ima ta kwanta tana tunanin yanda zata jawo md ko zatayi ma shehu magana ya roke shi? Batasan yanda zatayi ba, tana kwance tana nazarin me ma zata girka masa lunch, ga shi da yammah gefen Hindatu zai koma, a haka bacci ya dauke saboda rashin baccin jiya.

Md kuwa yana fita ya kira shehu, shehun cike da tsoro ya amsa wayar don yasan abokin shi bayada kwanciyar hankali gashi da safe, md ya labarta masa abinda kenen Shehu kuwa yayi yace na fada maka, Allah bazai bar ka haka ba, naji dadi abokina, nen ya masa bayanin me yace mata, shehu yace ya bata zuwa kwana biyu,yasan ta sauko ne, tunda ita ta same sa, a haka sukayi sallama da cewan zasu hadu anjima.

Na'ima kuwa sai kusan shabiyu na rana ta farka, ganin yanda lokaci ya tafi,  da hanzari ta wuce kichin da tunanin me zata girka, fried rice an cos low ta with chiken tara hadawa,  sai bayan karfe biyu ta kare aikin, ta sake wanka ta shirya cikin gwon din dark green  shadda tayi kyau sosai. Md kuwa da kyar yakai karfe biyu office ya ji duk zaman office din ya ishe sa, gida ya wuce, side din Hindatu yafara zuwa har lokacin bata dawo ba, har su Nuwaira yaranta an dauko su makaranta amman bata gida, abin yayi masa ciwo, yana tunanin in ya kare da matsalan Na'ima zai daukar Hindatu mataki ya gaji, ko bazai saketa don BIYAYYAR mahaifinsa, zai gyara mata zama ya gaji, a haka ya wuce side din Na'ima tun farkon kofar ya fara juyo kamshin turaren wuta, ya yi sallama ya shiga cikin falon tana zaune tana kallo ta amsa tare da mikewa ta amshi brifcase dinsa tana masa sanun da zuwa, kamar ya rugemeta, ya daure, dakinsa tavwuce da jikar, ya bita baya, yai mamakin gani dakin ko'ina a gyare an saka turaren wuta, toilet ta wuce ta hada masa ruwan wanka, ya shiga wanka ta koma falo, ya shirya cikin jalabiya ya fito da tunanin anya zai iya kwana biyun da Shehun yace, ko yanzun daurewa yake,  kamin ya zauna tace ga abinci, table ya wuce, ya fara cin abincin Shehu ya kira yana fada masa yazo, tare suka ci abincin suna fira, Na'ima kuwa bayan sun gaisa da shehu daki ta wuce duk jikinta yayi sanyi, ganin take kamar md bata gabansa, bata san mutunin daurewa kawai yake ba. Bayan sun kare cin abincin suka fita wajen gidan sun jima suna hira, Shehu yayi masa sallama ya wuce yana ta yaba girkin Na'imar, Md kuwa cikin gidan ya koma Na'ima tana daki kwance tana tunanin mafarkin da tayi da abbanta kuka take yi sosai, Md ganin bai jita ya wuce dakin yayi mamakin jin kukan ta, da sauri ya shiga dakin ya isa har saman gadon ya ce mata lafiya kike kuka, tayi shiru sai da ya kara maimaitawa tace masa ya yafe mata tayi kure, ya hau saman gadon sosai ya jayota zuwa jikinsa, ya rungumeta sosai jikinsa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya Na''ima ma wani sanyi taji a zuciyarta sun dade a haka, Md yace ta kwantar da hankalinta ba abinda zai rabasu yana sonta har gobe, jin abinda yace yasa ta kara shigewa jikinsa, ya kara rugumeta jikin shi.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now