BIYAYYA BAYAN RAI

423 29 0
                                    

🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI
Unedited

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU ASMA'U(SA'ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango leady

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 50-55

Haka  Na'ima ta cigaba
da gasa ma MD aya a hannu, ta ko ina baya samun sauki. A haka suka koma kaduna inda yake aiki, kadunar ma sai da shehu ya mata magana ta yarda zata tafi, a kadunar zaman ba dadi shida ake aure ayi kiba amma shi rama yakeyi, sam beda kwanciyar hankali, ko aiki yaje baya da nutsuwa, Hindatu kishin hauka, Na'ima kuwa ba kallar kiyayar da bata nuna masa ba,  har hakan yaso ya shafi aikinsa. Kullum addu'arsa idan Na'ima ba alkhairi bace agaresa Allah ya basa karfin guiwar rabuwa da ita.

Sai dai duk lokacin da yayi sallah ya roki Allah bayan ya kwanta banda soyayyar Ni'ma babu abinda yake karuwa azuciyarsa, ganin zai zefa kansa cikin halaka yasa kawai ya fara azumi. Sam ya fita harkar matansa, Shehu ne ya bashi shawarar yin hakan , ya yi MD ya bari ya samu Ummu zainab ya fada mata abinda ke faruwa yaki.

Duk wani hakkinsu na abinci da abubuwan bukata yana kokarin sauke masu, amma ya dena shiga dakin kowa, abinci ma awaje yake ci, idan yadawo gidan sai da dare, kuma idan yayi sallar asuba daki yake shigewa har sai lokacin fitarsa office yayi yake fitowa.

Ko Yaransa yanzu ba sosai yake haduwa dasu ba, duk lokacin da ya hadu dasu sai dai yajasu dakinsa suyita fira, wani lokacin kuma ya daukesu sutafi yawo. Sosai wannan abun ya fara damun matarsa, domin tana matukar sonsa kawai kishi ne yasa take masa wulakanci.

Na'ima halin ko in kula da MD yake mata ya fara damunta, sam bata ganinsa bare tayi masa rashin mutunci harya saketa, gashi Maryam na zariabare tazo su tattauna, kuma idan takira wayarta kullum maganarta dayace tayi hakuri tunda anyi auren ta zauna da mijinta lafiya hakan shine zai nuna tayi BIYAYYA ga Mahaifinta.

Wannan dalilin ne yasa ta rage kiran Maryam. Wata rana bayan ta gama shirin kwanciya ta kulle dakinta kamar yanda ta saba, wayarta ta dauko sai taji tana son jin muryar Hafiz, lambarsa ta nemo tana mai addu'ar Allah yasa yau ta samesa.

Cikin sa'a tana kira tashiga, sai da kiran ya katse sannan ta kara kira, kamar baza'a dauka ba sai kuma taji an dauka, shiru tayi tana hawayen farin ciki. Kamar daga sama taji muryar mace tana fadin Salamu Alaikum.

Saurin cire wayar tayi daga kunnanta ta kara duba lambar data kira, tabbas ba kuskure tayi ba, sake maida wayar tayi a kunne tana fadin hello ina mai wayar? Daga dayan bangaren akace ke wacece da zaki kira lambar mijina kuma kirika kiran ina mai wayar? Na'ima ta maimaita mijinta? Na'ima tace baiwar Allah Hafiz fa nake nufi.

Tsaki taji anja ana fadin shegiya karuwar banza mai bin mijin mutane, banda jaraba yanzu karfe 9:00 na dare zaki kira mani miji, abin haushin ma baki sani ba ko sunanki be rubuta ajikin wayarsa ba. Kitt taji an kashe wayar.

Wasu irin hawayen bakin ciki da kishi mai tsanani Na'ima taji suna zubo mata. Shin da gaske Hafiz yayi aure? Ya goge sunanta daga wayarsa? Lallai Maza basu da amana, ni ina nan ina kokarin kashe aurena sabodashi, na hana mijina hakkinsa duk sabodashi ashe yana can yana rayuwarsa cikin farin ciki da iyalinsa.

Karar wayar ta taji hakan yasa ta dauka batare data tsaya dubawa ba. Muryar dataji ne yasa saurin tashi zaune tana fadin Hafiz. Ajiyar zuciya Hafiz ya saki tare dajin wani abu ya sokesa azuciya, tun bayan da akayi masa rokin Allah ya hakura da tunanin Na'ima, amma ayau dayaji muryarta sai yaji wani yanayi yana shigarsa.

Biyayya bayan rai completedWhere stories live. Discover now