*ZULFA*
@MHIZZPHYDO
A Sweet and pitious Romantic love story
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Page 56*
Cikin sauri Yusayrah takaraso wajenta tana zaro ido ganin yanda kammaninta ya chanza , kanta duk fashe jikinta ma kurjewa neh atako ina
"Na shiga uku Mai sona kardai mutuwa tayi?" Ta tambaya a tsorace, tsaki yaja tareda janta a kasa zuwa tsakiyar palour sannan yadauko ruwan gora mai Sanyi akan dining table Gabadaya Yusayrah tagama tsorata da ala'amarin Iqbal she never knew haka yake da saurin fushi bata hankara bah taji Zuly taja ajiyar zuciya mai karfi tareda fashewa da kuka dalilin ruwan daya sheka mata afuska Cikin sauri ta tashi daga kwance tareda yin kneel down tana hada hannayenta guri daya alaman roko, cikin muryan dayake nuna tana jin jiki tace
"DanAllah kana hakuri da hali na ,dukda bansan laifin danayi bah amma kayi hakuri, nasan bazaka so ka aurar da yarka mijinta yadinga mata yanda kake min bah,inma don abinda Yay Mou yamaka neh DanAllah kazamo mai yafiya wallahi yanzu na chanza DanAllah kadaina duka nah banaso pls
"Jikinsu neh yayi Sanyi Kuma sai yayi Dana Sanin abinda yamata amma kuma yana tuna abin da tayi zuciya taciyo shi cikin muryan bacin rai yace
"Heartbeat bring that rubbish" Jiki na bari Yusayrah tadauko abinci acikin plate, ajiye mata yayi yace
"oya fara ci yanxu" Kallon fuskan shi tayi cikin tsoro tace
"Ni banajin yunwa yanxu lokacin cin abinci na baiyi bah" Wani kallon daya hauna mata neh yasata yin saurin jawo plate din, Kaman ranan yau ma dakyar ta hadiye Loman farko, ajiye plate din tayi
"Baki na babu taste" tafada Sincerely cos haka Yay Mou yafada mata ranan, kallon kinma raina min hankali yake binta dashi , shi dayaji da kunnen shi ance ta iya girki sosai amma shine tsantsan rainin hankali take yi mai jagwalgwale soboda shine marainin wayanta Kuma tayi calming bakinta babu taste
"Wato irin ni neh mai kudin banza bari kiyi almubazzaranci da abinci nah? Kinsan Wani irin aiki nayi nasamu kudin Dana ke siyan abubuwa agida? In Ba so kike nayi miki zanen kuliya bah tin wuri ki je ki tuka irin tuwon dakika tuka a Azare har ake yabonki bah"
Hawaye neh suka zubo mata tace"Irin shine Wlhy kusake ci kugani"
Kallon ki haukace yajefe ta dashi ai batasan lokacin data mike bah amma bata kaiga yi taku uku bah suka jita akasa again soboda gabadaya bata da Wani karfi atattare daita , tagama gajiya . Mikewa tayi dakyar ta lallaba tashiga kitchen din , Wani tuwon tasake tukawa sannan ta fita dashi dining tsayawa tayi har suka karaso A plate yasa sannan yakai Loma daya baki tsantsan bacin rai baisan lokacin daya wurge ta da plate din zazzafan semovita bah, ai jitayi Wani azabebben zafi yaziyarce ta ai kuwa tayi yar karamar kara tareda zubewa akasa jinin goshin ta na karuwa, Kota kanta baibi bah yayi hanyan stairs cikin fushi cos gani yakeyi Zuly mugunta takeyi cos yasan bayanda za'ayi ace girman kauye bata iya tuwo bah, cikin tausayin ta Yusayrah tayi wajenta, tsugunawa tayi daidai wajenta tareda kiran sunanta amma ko motsawa batayi bah
"Heartbeat ki kyale ta" taji yafada daga sama, A tsorace tamike tareda nufan wajenshi, sanyin tiles neh yafarkar da Zuly daga suman datayi , dishi dishi take gani kafin idonta ya watsake, da rarrafe ta haura stairs din cos bata jin zata iya takawa soboda rikewa dasuka yi...
Shigowan shi kenan dakin ya hango ta akan sallaya tana bacci tabe baki yayi tareda karasawa wajenta ya tsugunna agabanta fuskanta dasuka kumbura zuwa bakinta yake kallo ,bacci takeyi amma bana Dadi bah Fuskanta ya taba Don jin temperature dinta so dasauri yadauke hannun shi tareda barin dakin dasauri Chan sai gashi yadawo da capsule din magani ahannun shi sake tsugunawa yayi tareda bugin kafarta, afirgice ta Mike ai tana ganin shi ta makure kanta ajikin bango cikin tsoro tace