*ZULFA*
@MHIZZPHYDO
A sweet and pitious Romantic love story
(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Page 117*
San da suka yi kwanaki uku kafin su ka koma Abuja daga nan kuma suka fara shirye shiryen zuwa honeymoon din su.
Sanye ta ke cikin doguwar riga da hula mai kyau sai tashin kamshi ta ke yi, wani cute bag ta ke zipping inda Mourad ya Kafe ta da idanuwan sa yana kallon backside din ta kaman zai cinye ta d'anya,juyowa ta yi saboda tana ji a jikin ta kaman ana kallon ta,
Gira daya ta d'age mai lokacin da idanuwan su ya sark'e irin ya dai dinnan, girgiza kai ya yi tare da sakin ma ta murmushi mai sanyaya zuciya, bag din ta sauk'e daga kan stool kafin ta ce
"Na gama fah!"
"Zauna abin ki mun fasa fita sai gobe! "Ya fad'a yana gyara kwanciyan sa akan gado, kaman za tayi kuka ta ce
"Please mana! "
Lumshe idanuwansa ya yi ya ce"Na gama magana fah! "
Cikin rashin jin dadi ta ajiye bag din a kasa sannan ta zauna abakin gado tare da cire takalmin kafar ta at the same time kuma tana share hawayen fuskar ta
Tashi ta yi ta sa takalmin ta wanda ta ke sawa a cikin d'aki sannan ta d'auki wayar ta had'e da ficewa daga d'akin, a hankali ya bud'e idanuwan sa yana kallon kofa kaman ta na wajen...
Cikin sanyin murya ta ke fad'in"Ohh babynzuly don't cry kin ji"
"Zulynah yanzu ba za ki zo bah kenan? "Babynzuly ta fad'a cikin rawar murya
"Erh kin ga ban jin dadi ne shiyasa amma in na samu sauki zanzo kinji? "
"Miye ke damunki Zulynah? Is it maleria? Kin sha magani kuwa?" Ta fad'a a rude ga kuma sautin tashin hankali da ke fitowa daga muryarta
Hawayen fuskar ta ta share ta ce "Ohh Babynzuly which one ki ke son na fara amsawa? "
"Mummyna please ki ce a kawo ni na gaishe ki! "Yarinyan ta fad'a cikin sigar rok'o
Cikin rarrashi ta ce"No zan zo kin ji! "
"Ohk Zulynah! Ina son ki kin ji!"
"Ina son ki ni ma babynah!"
"Na gode, please ki sha magani! "Ta fad'a kaman wata babba,, gyada kai Zuly ta yi tare da kashe wayan tana kuma sauk'e ajiyar zuciya
"Ki ta so muje! "Ta ji muryan Mourad da ke tsaye a bayan ta tin dazu ya fad'a, kallonsa ta yi cikin b'acin rai wanda hakan ya bayyana a muryar ta ta ce
"After na gama ma ta karyan bani da lafiya! Na fasa zuwa! In yaso kar ka sake bani izinin zuwa ganin 'yata I don't care! Kai in fact kar ka sake bari na na taka ko kofar gida nikuma zan nuna ma ka ni yar halak ce!"
Kallon ta ya yi da kyau sannan ya sake duba gefensa kaman mai neman mai magana nan ya ga ita din ce
" who talked?"Ya tambaya kaman mai koyon magana ya na Kafe ta da na mujiya, hawaye ne suka gangaro ma ta, lips din ta ta ciza ta ce