*ZULFA*
@MHIZZPHYDO
A sweet and pitious Romantic love story
(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Page 121*
A tsorace ya ke kallon ta har yen dube-dube ya fara irin yana neman abin da ya sa ta kuka dinnan, volume din kukan ta ta kara cikin sauri ya zauna a gefen ta tare da jawo ta jikin sa cikin taushin murya ya ce
"DanAllah mine ki yi shiru! "
"Oho! "Ta fad'a a shagwabce har da make kafada tana mai cigaba da kukan ta, rasa abin yi ya yi aikuwa caraf ya chapki bakinta
Tirjewa ta fara yi saboda right away ba shi ta ke bukata ba, ganin yanda ta keyi ya sa shi sakin ta ba don ransa ya so ba!
K'awar da fuskarta ta yi saboda yanda ya kure ta da jajayen idanuwan sa, hannu ya sa ya juyo da fuskar ta nan ta runtse idanuwan
Dariya ya yi yana jan karan hancin ta "wayyo yunwa! "
Ta fad'a kaman zata yi kuka, ajiye ta ya yi a kan kujera tare da tsugunawa a gabanta ya ce"mine please na had'a miki wani abun daban? "
Mak'e kafada ta yi"toh muje ki taya ni! "
"Ni bacci na ke ji"ta fad'a tana kokarin kwanciya akan kujera, mikewa ya yi , cikin mutuwar jiki ya fara tafiya ganin ta rufe ido
Tana jin ya tashi ta bud'e idanuwan tana kallon bayansa, gani kawai ta yi ya tsaya, cikin sauri ta rufe idanuwan ta, karasowa wajen ta ya yi yasake tsugunawa, a hankali ya ce
"Fruity!" Dum gaban ta ya fad'i saboda tasan miye ya ke nufi in ya kira ta da hakan
"I miss you fa! Please in kin gama cin abinci ko round daya ki bari muyi! "Ya fad'a cikin sanyin murya yana shafa sliky fuskar ta
Wani tausayin sa ta ji ya kama ta saboda rabon su da suyi making love yanzu kwana hudu kenan ko rage zafi kuma bata bari ya yi saboda gabadaya yanzu bata son yana ko tab'a ta ne amma tasan abu ne mai wuya hakan ya yiyu barin ma da ta da ri ga ta saba mai da jikin ta, tana jin lokacin da ya mike a hankali ta sake bud'e idanuwan ta tare da raka sa dasu, ajiyar zuciya ta sauke tare da gyara kwanciyan ta lokacin da ya shige kitchen.
Da taimakon Google ya samu ya tuka ma ta tuwo din har da miyan kuka duk da ba karamin wuya ya sha ba amma ya ya iya tinda shi ya sata a condition din da ta ke
Yana tsaye ya hard'e hannayen sa a kirjinsa yana kallon yanda ta ke shan baccin ta, a cikin baccin ta ta ji kamshi ya cika ma ta hancin a hankali ta hau bud'e idanuwan ta, caraf ta sauke su a kan sa
Da sauri ta mik'e tana dada bude sleepy eyes na ta da kyau "kar dai baka gama dafawa ba? "
Ta tambaya tana Adduan Allah yasa ba mafarkin hadadden kamshin tuwo da miyan kuka ta keyi ba
"Kalli nan! "Ya fad'a yana nuna mata stool da ya ajiye abinci, wani irin yawu ta had'iye tana lashe labban ta cike da kwad'ayi
Jawo stool din ta yi gabanta sannan ta fara bud'e rufeffen plate din gaban ta, wani irin lumshe idanuwa ta yi saboda kamshin da ya bugi hancin ta