part 11

956 65 0
                                    

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*ASHWAAN*

      STORY & WRITTEN

               BY

       _Neeshar_jay_


Happy sallah jama'a Allah ya maimaita mana Ameen
   Ina jiran naman sallah na har yanzu shiru

Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu kun san abubuwa sae a hankali

Love u all ❤❤

*HAPPY TWO YEARS ANNIVERSARY KAINUWA*

united we stand and succeed our ambition is to entertain &motivate the mind of readers

  2⃣0⃣ to2⃣5⃣

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun ranar da sir farouq ya karba assignment dinsa kullum hnkln sa na kan safa wani irin sonta na fisgarsa amma bae San taya zae gaya mata duk da ya samu no wayar ta sae dae yyi ta kallo amma ya kasa kira  har akayi Hutu

******************
Safwaan ma ya dawo gda sbd sallah da za'ayi

Shirye2 ake sosae kowa naso yyi kyau

Rafeeq da Tasleem ba a barsu a baya bah hudima suke sosae

Alhmdllh anyi sallah lpy gdan Alh. Mas'ud a cike da mutane masu zuwa barka da sallah da kuma mutanen gdan twins ma ba'a barsu a baya bah suma sunzo cika taro.

Da misalin karfe 8:30pm bayan sallahr isha gaba dayan su suna zaune a parlourn domin yin dinner gaba daya sae farin ciki suke ita dae safa tana daurewa ne dan zazzabi taji alamun zae rufe ta a haka suka ci abinci har suka gama.
Fira suka dora cin jindadi ita dae jin su kawae take dan zuwa yanzu gaba daya zazzabin ya saukar mata lafewa tayi jikin kujeran da take sosae daddy ne dake kallonta ya kula da kamar bata jindadi yace" Safa lpy kuwa na ga tun dazu kinyi shiru kamar baki da lpy"

Ta dafe kae tana fadin"wlhi daddy tun dazu zazzabi nake ji"

Yace"subhanallahi sannu"

Ya kalla Rafeeq yace"likita kana ji tashi ka du ba ta"

Yace"toh daddy"

Safwaan ya tabe baki yace"su yaran nan abu kadan su ce basu da lpy koda ciwon kan stress ne sae su wani langwabe ajjebotars kawae"

Daddy yace"kae kama min bakin ka kasan ya take ji ne"

Yyi shiru bae kara mgn bah

Ina kuma safa ta watsa mishi harara kafib tabi bayan Rafeeq da ya fita

Bayan Rafeeq ya bata drugs ya dawo shi kadae ita kuma ta koma daki ta kwanta

Haka suka cigaba da firar har kusan 10pm kafin sukayi sae da safe kowa ya tafi part dinsa

          *******
Bayan safa ta kwanta da niyar bacci taji wayar ta na ringing ta sa hannu ta jawo wayar ganin new no yasa bata daga ba har ta tsinke sae da aka koma kira jiki a sanyaye ta dauka tare da yin shiru     dayan ban garen aka ce"Aslm Alkm"

Shiru tayi dan jin muryar namiji sae da ya kara mata sallama cikin sanyin murya tace "wslm"

Shiru ne ya biyo baya da taga alamun ba mgn za'ayi ba tace"dawa nake mgn"

Boyyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"sir farouq ne"

Wani irin razana tayi tana mai2ta Sir farouq

A hankali yace"nasan kina mamakine koh safa"

Tace "sosae ma kuwa"

Ya kara kwantar da murya yace"wato bazan boye miki bah Aysha tun ranar da na ganki zuciyata ta kamu da sonki kullum ina attempting gaya miki amma ban San ya zaki dauki zancen nawa bah dan Allah ki tausaya wa zuciya ya kar ta buga"

Shiru kawae safa tayi gaban ta sae faduwa yake kalma ko daya ta kasa furtawa

Bata ankara taji muryarsa ta canza zuwa muryar mae kuka  da sauri ta kashe wayar har yanzu gaban ta sae dukan tara2 yake Kalmar innalillihi kadae take fita daga bakinta

A haka  Tasleem ta shigo ta same ta "lpy kuwa sis na ganki haka ko duk ciwon ne" tasleem ta tambaya tana taba wuyan safa

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Tasleem na rasa mae ke damun mutane Tasleem ban San ya zanyi da rayuwa ta bah kowa ya ganni yace yana so ni kadae ce mace a duniya Ku Mae yasa basa maku haka sae ni"

Cikin rashin fahimta Tasleem tace" ki gaya min Mae ya faru ne kin Sani a duhu"

Safa ta goge hawayen da ya zubo mata tace"Tasleem yanzu fah sir farouq ya kirani"

Da mamaki Tasleem tace"sir farouq kuma toh ina ya samu no dinki da har zae kira ki tunna ma Mae yace miki"

Safa tace"shima din wae sona yake"

Tasleem ta gyara zama tace"tirkashi lallai ko akwae matsala ga ya kabeer ya ma'aruf snn kuma ga sir farouq"

Safa tace"shawara nake nema ba cewa nayi kitsaya kirgasu ba"

Tasleem tace"toh gobe ki gaya ma ya feeq mana yasan halin da ake ciki kinga idan yaso sae ya baki shawara koh ya kika gani"

Tace"toh Allah kae mu goben sae in fada masa"

Tasleem ta amsa da ameen

Suna cikin fira sae ga texy message ya shigo wayar safa jawo wa tayi tare da karanta wa text ne kamar haka"_y dd u hang d call anyway we talk gobe good nyt and don't forget to dream of me my Angel bye💋❤"_

Tsaki tayi tare da ajiye wayar Tasleem ta dakko ta karanta dariya tayi sosae tace" Matar sir farouq harda wani kiss da heart kice bayan kunyi aure zaki sha love " ta fada tana kara dariya

Pillow safa ta cilla mata ita kuma ta kauce ganin haka taja blanket ta kwanta ita kuma Talseem ringing din da phone dinta tayi ne yasa tsagaita dariyan ta dauka koma wa tayi ta lafe kan pillow tare da yin kasa da murya waya sukayi sosae da Rafeeq Kafin sukayi sae da safe.

Washe gari da safe su Hasfa suka shirya koma wa gda gaba dayan su safa da tasleem suka saka daru zasu bi aunty Haleema dan itace da ciki haihuwa wani wata da kyar daddy ya yarda suka hada kan kayan su da zasuyi amfani dashi.

A parking space suka hadu dasu ya ma'aruf da yanzu ne shigowar su shida Nabila (sistern shi)  bayan yyi parking suka nufi inda mutanen gdan ke tsaye gaba daya Safwaan na ganin Nabeela ya hade fuska kamar bae taba dariya bah (a haukan ta wae son shi take hmmm lallai Nabeela kina da aiki) hk ma safa ganin yanda ya ma'aruf ke kallonta yasa ta hade fuska tare da kauda kanta gefe

Bayan sun gama ban kwana safa tayi gaba dan kar ma ya ma'aruf ya tsaidata ita kuma Tasleem hawaye ne ya cika idonta na rabuwa dasu mommy ne koh Rafeeq oho  Nabeela ta matsa kusa da safa tace"gudun yayan nawa kike ne"

Dariyan yake safa tayi tace" haba dae"

Nabeela tayi dariya har hakorin ta ya bayyana tace"toh ki kula mana da soyayyar mu karki je can wani ya kwace"

Itadae safa smiling kadae tayi ta matsa kusa da Ummi tayi hugging dinta ta fadin"gonna miss u mom"

Ummi tayo dariya tace"same angel"

Karaf ta tuna da sir farouq gabanta ya fadi a samule ta janye jikin ta daga na ummi Rafeeq ma haka sukayi dashi kafin suka shiga mota suka wuce

Sae mu raka su safa da addu'an Allah ya kaesu lpy


Yawan comments yawan typing


Yours

Neeshar_jay💞

ASHWAAN (Love Saga)✔️Where stories live. Discover now