Bismillahir Rahmanur Raheem
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah S.W.T Wanda ya bani iko da damar rubuta wannan littafi, INA rokan Allah da ya bani damar rubuta kyakkyawa acikinsa y haneni da rubuta mummuna. Ameen summa ameen.Zuwa ga yan uwa na wattpadians da kuma writers ina rokan Ku da aduk Inda akaga gyara ko kuskure kar agaji da fadamin domin kuwa sabuwar writer ce ni Dan wannan shine novel dina na biyu ngde
PART ONE!
Iska ce me dadi gaske Ke kadawa a Hankali yayin da ganyen bishiyu Ke kadawa a Hankali cike da Burgewa da ban shaawa, garin KANO kenan ko dame kazo an fika. Tafe take cikeda nutsuwa tana takawa a sannu kamar yadda tasaba littattafae ne rungume a kirjinta yayinda side bag dinta Ke rataye a kafadarta. Kamar kowace rana yau ma sanye take da hijjab daedae gwiwarta yayinda atamfarta me ruwan pink and yellow ya sami damar bullowa ta kasan hijjab din Wanda ya kasance me hannu. Zagayayyiyar fuskarta ta bayyana cikin hijjab din wadda babu ko digon powder akai balle ayi maganan lip glows akan kananan lips dinta. Haka take zuwa skul dinsu kullum wato B.U.K batareda tashafe komi akan fuskarta ba, gareta tace karatu tajeyi ba fashion ba. HAMNAH kenan!!!!
Daliba a bayero university kano department of medicine. A yanxu HK tana level 700 ne Wanda ya saura one year ta gama. As usual inda tasaba zama ta heading Wanda wani palace ne can bayan parking space din malamai, gurin ya kasance shiru a koda yaushe Dan dalibai basu fiya zuwa wajen ba shiyasa yakeda rangwamen hayaniya. Ko da ta isa pray mat ta Ciro daga Jakarta ta shimfida sannan ta zauna . mike kafarta tayi ko taji dadi Dan ba Kadan ba ta gaji, handout din dasuka gama lecture akai ta dauko ta Shiga dubawa a nutse. Kusan one hour sannan ta mayar jaka tareda zaro wayarta kiran tecno spark 3. Security dinta bude nan da nan hotan wasu yara biyu mace da namiji ya cika screen din, masha Allah nace saboda tsantsan baiwar kyau da na hanga wajen yaran. Murmushi naga tayi tareda shafa fuskan Hoton kamin ta shiga contact, ban ga number dinda ta kira ba kawae dae nga ta kanga wayar a kunnenta shiru nadan wani lokaci kamin a Hankali cikin daddadar muryar data tafi da tunanina naji tana cewa "Ae min gama lecture yau ko? Banji abin da aka ce ba daga daya bangaren ba kawae dae naga ta gigiza kae tareda cewa " okay na gode. Wayar ta sauke a kunnenta tareda tattare takardunta tahada ajaka Wanda zata riqe kuma ta riqe a hannu. Motarta qirar vibe naga ta nufa ta bude tareda shigewa sannan a Hankali ta yimata key tareda Barin gurin cikin tukinta na nutsuwa..
YOU ARE READING
AURENAH!
RomanceA romantic love story, comedy together with tragedy of life. Ya taso cikin qiyayyar dangin uba tareda rangwamen kulawar iyaye.