part 2

111 5 0
                                    

A Hankali take driving yayinda sautin karatun alqur'ani me girma yake tashi cikin qira'ar sheik shureim. Tafiyar da bata wuce 40 minutes ba ya kawota gidansu. Tundaga bakin gate din gidan zaka iya qissima samun me gidan. Gida ne matsakaici ba me girma can ba hakama ba qarami ba dae dae misali, amma fa ko iya gate din ka kalla zaka iya hasaso tsaruwar cikinsa. Horn tayi kusan sau biyu kafin wani matashi yazo y bude gate din sa kan motar tayi cikin gidan direct parking lot ta nufa sannan tayi parking din motar tareda kasheta. Cike da gajiya ta kwashi kayanta tareda fitowa daga motar ta kulle. Cikin gidan ta nufa inda suka hadu da wannan matashin da y bude mata gate, murmushi ya sakarmata tareda cewa Anty hamnah sannu da zuwa, yamutsa fuska tayi cikeda gajiya tace yauwa Affan. Kallanta yai yace da alama anty kin gaji, ssae ma kuwa tace a yayinda suke shiga falon. Kan kujera ta zube tareda furta wash Allah nah Affan Dan miko min ruwa , To yace yana nufar fridge din dake falon pure water ya dauko me sanyi ya miqa mata yauwa tace tareda karba bakinta ta kae tareda bulawa nan danan ta zuqe ruwan Alhmdllh ta fada kafin ta kalli Affan wai ina yaran gidan ne? Ta tambaya basu dawo daga makaranta ba ya bata amsa, Ammi fah ta sake tambaya, barci take ya fada mikewa tayi itama tana fadin nima bari naje na huta, a fito lpy yace yana cigaba da Kallan ball din da yakeyi. Direct dakinta ta nufa , kayan hannunta ta zube tareda tubewa ta daura towel, toilet ta shiga tayi wanka, sassaukan kayan shan iskah ta saka sannan tabi lafiyar gado. Se qarfe shida da mintuna ta farka da addua dauke a bakinta toilet ta shiga ta kuskure bakinta sannan ta fito parlour, a zaune ta tarar da Ammin tasu tareda ragowar qannenta ana ta wasa da dariya , gaesheda ammin tayi kamin ragowar qanan nata suka gaesheta sannan aka cigaba da hirar da ita, sallar magrib sukayi sannan as usual aka dasa sabon faifan hirar harda ammi, se wajejen takwas sannan sukayi dinner bawae Dan baa gama abincin bane aa sedan Haka al'adarsu take, nan ma suna kammalawa aka cigaba har zuwa lokacin da Alh.Abubakar wato mahaifin su hamnah ya dawo, bayan shima yayi refreshing yaci abinci se ya gayyaci hirar da ta dawo dakinsa, nan kuwa sukayi tayi harshi wanda hakan Ke kara kawo shaquwa cikin family din da bawa iyayen damar fahimtar 'ya'yan nasu ssae , halaiyya ,dabiu da kuma bukatunsu. Wannan kenan!!

Zafafan matasa ne da aqalla zasu kai shekaru 34-35 a duniya, dayan ya kasance fari mai matsakaicin haske haka kuma kallo daya zakai masa ka gane shidin kyakkyawa ne na gani a fada MAHMOUD knn! Yayinda na kusa dashi ya kasance shima fari ne amma farinsa yafi na Mahmoud haske tabbas a kallan farko in ka ganshi zaka iya kiran shi shugaban kyawawa na duniya , tako ina ya hadu abin baa cewa komai UMARUL FHAROUQ kenan Wanda iyayensa da jamaa kewalaqabi da yarima wasu kuma suce prince. Dukkan su Suna da qirar jarumai wato ya kasance su din dogaye ne masu ginannen miki, damtsensu dauke da 6packs Wanda me kallansu zeyi tunanin yawan Jim ya kawo su sedae Sam ba haka abin yake ba halittace daga khaliqu kulla sha'in. Fuskarsu takasance doguwa mai dauke da qananan lips Wanda har na fharouq yafi na Mahmoud qanqanta , idanuwansu manya ne masu matsakaicin girma, kwayar idan fharouq Kalan zaiba ne Wanda wasu kewa laqabi da idan mage hakana kuma oily and sexy Wanda yawan lushesu dayakeyi Ke qara qawatasu, yayinda Mahmoud qwayar idansa baka ce wuluk, kwantaccen sajen da ya zagaye fuskar su shi yadada futo da ainahin kyan nasu, kai me karatu duk yadda zan fadesu sun wuce haka kawae ka kiyasta Wanda yafi kowa kyau shine fharouq se me bimasa Mahmoud lol.
Muryarsau ce ta dawo dani nutsuwa ta daga shagalar danayi wajen kallansu, magana suke kaman wasu mata barema prince da har wani yamutsa fuska yake, saurarawa nayi ssae Dan naji me suke cewa, Mahmoud ne ya kalli fharouq " haba mana fharouq just 2 days nefa kamin in dawo, test din Nada muhimmanci shiyasa bazan jira se na dawo ba" gyada kai kawae fharouq din yayi kafin bayan shudewar wasu sakanni yace naji, yauwa ko kaifa inji Mahmoud tareda zaro wata file Mara yawa ya ajiye gaban fharouq din yana cewa yauwa ga record din se ka shigarmin, jinjina kae yayi be ce komai ba duo kuwa da yanayin gurin na masa dadi, rairayi ne wajen irin me ban shaawa din nan Wanda me fitar da sanyi yayinda furenni suka zagaye wajen Wanda hakan ba qaramin qawata wajen yayiba, Mahmoud ne y girgiza Kansa a ransa yana fadin muskilanci da mulkin sun motsa Dan haka tattare takardun daze tafi dasu yayi sannan yacewa fharouq " hey prince am gone see you later" dagowa yayi ya kalli mahmoud din yana cewa cikin muryarsa me taushi da dadin sauraro "jirani mana ni me zanyi anan" tsananin dadi , zaqi, taushi da amon muryarsa ya sanayi suman tsaye Wanda har ban San sanda Biro na y fadi ba Dan haka Ku biyoni in na siya sabo se muji su kuma suwaye wadannan matasa!!!

Your votes and comments are highly needed Dan kunsan su zasu qaramin karsashi da confidence din cigaba da rubutun

Ngde ssae my wattpadians

Momyn Ariff da Airah ce.............

                          AURENAH!Where stories live. Discover now