Wanka yayi ya shirya cikin shadda galila me uban tsada golden colour, ba karamin kyau ta masa ba se daukan ido takeyi.
Wankan sa knn aduk ranar jumaa wato manyan kaya. Part en ummi ya shiga lkcin tana hakimce kan cushion rikeda tasbaha tana ja amsa sallamar tayi tana me binsa da kallo, cikin ranta kuwa gdy da tasbihi takeyi ga sarki me kuwa me komai daya qagi wnn halittar kuma ya sanyashi ya zamo 'da a gareta.
Har ya iso ya zauna a can carpet din da ya mamaye duka dakin ba tasani ba se tsinkayo muryarsa tayi cikin taushi da amo yana fadin "mun tashi lpy ummy? Murmushin ta me 'kayatarwa tasaki kasancewar ta mace me yawan faraa ta amsa da fadin "lpy lau son fatan kaima haka" "same" ya amsa fuskarsa ba yalwatacciyar fara'a.
Ummy ta Riga tasaba da halinshi na miskillanci da rashin faraa Dan ko ita bakoda yaushe take ganin murmushin sa ba.
Sanin takamaiman halinsa Abu ne me matuqar wuya Dan murdadden mutum ne shi Wanda da wuya ka gane farincikin sa ko bakin cikinsa. Bambance abinda yakeso da Wanda baya so is another sort of work.
Magana kuwa ita tafi komai bashi wahala.Mikewa yayi yana kallonta "ummy zan wuce masjid" gyada kanta tayi tareda cewa "ok son in ka dawo ina so muyi magana".
Nodding kanshi yayi ba tareda yace uffan ba y juya ya fita. Bin bayanshi da kallo ummy tayi ranta ba dadi, duk cikin 'ya'yanta ta fisanshi kuma duk ciki shine me wuyar shaani.Shiru tayi tana tuno wasu moments da suka wuce, lkcin da fharouq dinta yake rayuwa kamar kowa, yake walwala kamar kowane mutum kafin tashi daya qaddara da masifar dangin uba suyi fata fata da duk wata walwala da jin dadin da yakedashi, Wanda har yakaishi ga rikidewa ya dawo sabon fharouq Wanda duniyarsa ta da da ta yanzu tasha bambam matuqa, lkcin da ya juye ya koma wani irin mutum da be damu da kowa da farin cikin kowa ba. Kafin asamu dakyar abubuwa suka Dan sassauta ta dalilin yawan addua da kuka da ummy keyi akan Allah y dawo mata da danta normal.
Nannauyar ajyar zuciya ummy ta sauke tana goge guntun kwallar da ya sauko mata na tausayin gudan jininta, a fili ta furta " ya Allah ka kare min Dana daga sharrin dukkan wani abin halitta a ko ina yake".
📖📖📖📖📖📖📖📖
Kai tsaye wata black Mercedes Benz, daya daga cikin motocinsa ya nufa, da gudu driver en shi yazo ya bude masa motar bayan ya shiga ya rufe sannan ya shiga driver's seat yaja. Direct masallacin sheik malam jafar (rahimahullah) dake gadon qaya ya nufa kasancewar yasan nan yake sallahr jumaa en shi indai yana gari. Suna qarasowa driver en (John) y bude masa ya fita, direct cikin masallacin ya shiga kasancewar 10:12 akwai gurare. Shikuwa john Cikin motar ya shiga ya zauna ya makala ear piece yana jin waqa.
Haka sukeyi, every Friday ze kawoshi masallacin kuma ya jirashi a idar da Sallah a gama huduba sannan su tafi.
Am sry for the short typing. Not feeling well that's why, manage with this please!!!
Mu hadu a next part insha Allah💑💑
YOU ARE READING
AURENAH!
RomanceA romantic love story, comedy together with tragedy of life. Ya taso cikin qiyayyar dangin uba tareda rangwamen kulawar iyaye.