OK kawae Mahmoud ya furta tareda Qarasaw wajen motarsa budewa yayi ya shiga sannan fharouq daya qaraso shima ya shiga side din me zaman banza, tafiya suke yi tamkar kurame Sam ba jin dadin tafiyar Mahmoud yakeyi ba amma sanin ko ya kawo topic of discussion ba kulasa prince zeyi ba se shima yayi shiru. Tafiya me dan nisa sukayi kafin su shiga wannan shahararriyar unguwar wato G.R.A (nasarawa) wani kankararren tamfatsetsen gida suka nufa Wanda ko a unguwarta nasarawa babu gidaje dayawa masu irin girma kyau da fasalinsa. Horn daya me gadi ya bude musu gate suka shiga. Daidaita parking prince yayi sannan ya kashe motar tare da fitowa, shima Mahmoud fitowa yayi sannan fharouq ya rufe motar. Direct cikin gidan sukayi heading, main falour din suka shiga Wanda tsaruwarsa kadai ya isa tabbatar da Gidan na manya ne Wanda suka kama kasa. Tafiya suka cigaba da yi inda suka nufi wata qofa cikin kofofi hudu dake falon, Masha Allah na fada saboda ganin tsari da haduwar parlourn duk da cewa na farko ya fishi girma amma wajen kyau da tsari Sam ba hadi. Komai na cikin parlourn light green ne se ratsin golden Wanda ya hadu y haske parlourn. Kujeru suka samu suka zauna batareda jiran umarni ba Suka mimmike kafafuwa suna fadin "wash" wai irin sun gaji dinnan amma fa injisu ni kuwa nace samun guri 👨lolz.
Mintuna kadan da zaman nasu se ga takun takalmi kwas kwas Wanda yake fitowa ta saitin stairs din dake parlourn Wanda akeyinsa cikeda nutsuwa, ko baa fada ba kasan me yinshi ta kasance babba, classy kuma hamshakiyar mace. Dukkansu attention dinsu suka maida stairs din lokacin da wata kyakkyawar mace ta bayyana fuskarta dauke da motherly smile. Kyakkyawa CE ajin farko Wanda kallo daya zakamata ka gano asalin kamannin da sukeyi da prince, ba tareda an fadamin ba nayi concluding cewa mamansa ce. Cikeda kyakkyawan murmushi ta qaraso ta zauna a kujerar dake tsakiyarsu tareda cewa" marhababikum ya aulad" gaba dayansu murmushi sukayi me kyau da maana tareda cewa "kaifa ant ya ummy?" Tun kafin ta kai ga amsawa prince ya tashi ya zauna a gabanta, Dada fadada murmushinta tayi tasa hannu akansa tana shafawa sannan ta amsa da cewa " ana bi khair, wa antuum?" Dada lafewa prince yayi acinyarta batareda yace komai ba se Mahmoud ne ya bata amsa da " nahnu bi khair" kallan prince tayi ssae tace" are you ok son? Yamutsa fuska yayi tareda cewa" am so exhausted ummy" message ta fara yi masa ahankali tana cewa" I think if you refresh it will soon get away" " i hope so " yace batareda ya tashi daga laps dinta ba. Murmushi kawae tayi ta dago tana duban Mahmoud tace" ya aiki son? "Aiki se a hnkli ummy" ya bata amsa " to Allah yayi jagoranci" tafada yayinda Mahmoud ya amsa da "Amen". Nan suka cigaba da hirarsu ita da Mahmoud batareda fharouq yasake cewa komai ba, kafin sukayi sallama da Mahmoud din cewar ze qarasa gida, "k gaida mom din taku" ummy ta cewa Mahmoud "toh ummyn mu zata ji" ya amsata Kefin ya kalli fharouq" hey prince ni na wuce" "okay" yace "my regards to my mom" ya dada fada "insha Allah" Mahmoud y amsashi yana fita daga parlourn. Ba wani nisa ne tsakanin gidan su Mahmoud Dana su fharouq ba Dan gida uku ne a tsakaninsu kawae.
Bayan fitar Mahmoud ummy ta dawo da kallanta kan fharouq a hankali take shafa kansa yayinda shikuma y lumshe ido cikeda jin dadin hakan " khooyaa" ta kirashi da sunan da yafiso daga gareta which means beloved, Murmushi ya saki me taushi Wanda ya Dada fito da ainahin kyaunsa na gaban kwatance tareda 2sides dinsa(dimples) masu kara kawata fuskarsa da karamata haiba da kwarjini "na'am life" ya amsa mata ita ma murmushin tayi sannan tace " kaje ka huta akwae muhimmiyar maganar da zamuyi dakae" dagowa yayi ya kalleta ssae kana ya tabe bakinsa Dan yasa baya tantama maganar dasukayi da abbynsa ne Dan haka y gyara zama yace "life in dae akan Maganar da mukayi ne da abby ,Dan Allah kar kisa baki wallahy bazan auri wannan abar ba , I like a good mother to my children and I will definitely find her buh dat girl isn't my type, kwata kwata batada tarbiyya so don't even stress your mouth, suma iyayenta are after something that's why suka nace in aureta ni kuma I will surely surprise them Dan ko me zaayi I won't accept this" ya kai karshe yana faman sauke numfarfashi kaman Wanda yayi tsere Dan magana me tsawo irin haka ba halinshi bane Dan haka be saba ba, kallanshi ummy keyi cikeda so da tausayi "khoyaa kana ganin hakan ze yiwu ? Kafasan umarnin ammuh ne ". "Kar ki damu just pray for your son kinji ummyna buh kome zaayi bazan yarda da wannan ba, ai umarnin NATA ba na Allah bane, manzon Allah da Kansa yace mu zabawa 'ya'yayen mu uwaye nagari saboda tarbiyya, toh life itaa wnn tarbiyyar gareta balle ta bawa wasu? "Hakane son buh bana San abinda ze saka a matsala kuma zasu CE nina zugaka" "kyalesu suce koma miye ummy all I know shine da da yanxu da banbanci Dan haka ba Wanda ya isa ya cimin mutncinki ban dauresa ba ko waye kuwa" murmushi ummy yayi tasa hannu ta tsiyayo swan din dake ajiye kan center table acikin wani farin tumbler ta sawa fharouq a baki tana cewa "open and drink water son karka damu na fahimceka" ta fada tana San cooling temper dinshi ganin yadda eyes nasa suka fara sauya kala. Sha yayi ba musu , shiyasa yakesan ummynsa saboda tasanshi in and out. Mikewa yayi bayan ya gama sha ya kalleta yana murmushi Wanda hakan ke nufin ze Shiga side dinshi Dan gabadaya kanshi juya masa yakeyi kasancewar yayi abinda be saba ba wato doguwar magana "okay see you soon" ummy tafada tana me kallan dannata , juyawa yayi ya fita daga parlourn sannan ya bude wata da ga cikin kofofin dake main parlourn Wanda nanne corridor in daze sada ka da part dinshi. Binshi da kallo ummy tayi har ya fice sannan ta sauke numfashi me karfi " Allah ka tsaremin yarona" ta fada cikeda damuwa.
WANE NE FHAROUQ?
Ku biyoni next part danjin wanene shi? , wacece yake cewa baze aura ba? , su waye kesan se ya aureta? , mene ne alakarsu da it's? Duka yana cikin next part,
Nagode ssae my fans, kar Ku gaji da voting da comments, likes da sharesNagode ssae really appreciate your effort
Gdy ta musamman ga Sis Anty Ayusher muhd, Anty Mamuhgee, Sis suryhams, Dadai sauran wattpad writers .

YOU ARE READING
AURENAH!
RomanceA romantic love story, comedy together with tragedy of life. Ya taso cikin qiyayyar dangin uba tareda rangwamen kulawar iyaye.