CHAPTER 3

49 5 0
                                    

Papa ta kira sunan sa lokacin da yakai bakin kofa zai fita.
A hankali ta karasa wurin da yake papa wani abu nake ji a cikin zuciya ta ya rike min ina jin kamar zan mutu.
Numfashi na yana sarkewa (i feel suffocated here).

Deejatu kiyi hakuri ki nutsu kiyi ta addua dukkan tsanani yana tare da sauki.
In sha Allah kamar yau zaki ga komai ya wuce kiyi ta kai kukan ki wurin Al Aleem.

Kwana deejah tayi batayi bacci ba a kan darduma tayi tsayuwar har sai ka kafafuwanta suka fara rawa, haka wurin sujood sai na numfashinta ya fara daukewa kafin.
Zaune akan abin sallah har aka kira asuba.

Kabir zaune a gaban mahaifinsa Baba usman kamar yadda kowa yaje kiran sa.
Kabir baba usman ya kira sunan sa da tarin bacin rai a muryar sa idanuwansa sun canza kala sunyi jajir saboda bacin rai.
Mutumin banza shashasha wand bai san hallaci ba na sha fada maka biyayyar da kake yi wa baffanka ita zata jawo maka kowacce irin matsala a rayuwar ka. Kanina ne uwar mu uban mu daya dashi amma ni da na haife ka baka mutun ta ni kamar sa. Saboda shi yayi arziki ko ya daukaka a cikin dangi, ina arzikin yake yanzu tunda baa je ko ina ba ya salwanta saboda Allah yasan babu alkairi a barin sa da dukiya in bada auri saki babu abunda yasa a gaba wai shi mai arziki.
Kai idan kaki bin maganar sa kana gani kamar baka masa adalci ba zaiga don yanzu bashi da komai ne ka guje shi, ko ba maganar ka a kullum ba kenan.

Baba kayi hakuri duk wannan maganar ta wuce dan Allah kaje gidan su kuyi magana da papa kuyi.....

Kabir tashe ka bace min da gani.
Wallahi ko ni ne abunda zanyi kenan kaci sa'a ma da bai maka ka a kotu ba. Kaje wurin wanda ya isa da kai din yaje ya bashi hakuri. Uban kishiya da zuwa biko.

Kabir tun da alamarin nan ya faru gaba daya ya rasa nutsuwar sa. Hankalin sa bai sake tashi ba sai da ya koma gidan ya tarar da ba komai na daga kayan sawarta da na yara. Sannan karfe goma na dare yaga message din papa cewa ya bashi kwana biyu ya kawo masa takardar dee.
Anya kuwa zai iya rayuwa babu dee matar da ta gama shiga rayuwarsa tayi yadda take so da hankali tunani da nutsuwar sa. Shin ina zai kai tarin so da kaunar da yake mata. Uncle why.
      
                Flashback
Dk kasan da cewa uncle yana yin yadda yaso da kai ina jin tsoron biyayyar da kake masa wata rana zatayi sanadiyyar da zaka rasa abunda yafi komai muhimmaci a rayuwar ka.
Me yasa baka iya ce masa a'a ba komai ne zai zama kana amsa masa ba. Musamman abun da ya shafe ni da kai gaskiya hakuri na ya fara karewa.

Kallon ta yayi cikin kulawa dee ba haka bane wallahi uncle bazai taba cutar dani ba ina so ki gane haka. Sannan na miki alkawari daga yau uncle bazai sake shiga hidimar gidan ki ba In sha Allah.

Dk" uhmm uhmm dee dan Allah mubar wannan maganar bakya tunani wata ran maria taji irin wadan nan maganar daga bakin ki kin san bazata ji dadi ba.

Shikenan bazan sake ba kayi hakuri kuma idan ranka ya baci.

                  Present
Uncle barka da rana.
Barka dai kabir.  Me yake faruwa ne tun jiya naga maria a gida na tambaye ta kuma sai kuka kawai take yi me yake faruwa.

Eh haka ne uncle na fada mata ta zauna har sai mun sasanta da deejah kafin nan ita ma na mayar ta.

Wani irin kallo ya watsa masa mai nuni da kana da hankali kuwa.
Yanzu akan wannan marar mutuncin yarinyar ne dama ka dawo min da maria gida. Toh tun kafin raina ya baci ya shiga ka fito da matarka ku tafi banza sakaran yaro kawai.

Kabir ransa a bace ya tashi uncle idan ta gama ta koma kawai ni ina da abubuwan yi a cikin gari gaskiy.
  Yana ji yana ta kiran sa amma bai koma ba ya shiga mota ya tafi gidan Ahmad ya wuce yana shiga yaga motarsa tare da ta ilyas da hamisu.

Kan kujera ya fada ya kwanta kawai.

Ya dai Dk na dee ahmad ya tambay.

She find out and she is gone.

Hey another chapter is here
Don't forget to show some love

Comment
Share
Vote
AmminA3

LAIFI DAYAWhere stories live. Discover now