CHAPTER 10

27 3 1
                                    

Okey here i come insha Allah back fully till we finished the story.
#stayhome besafe may Allah see us through this hard time Ameen.
 

Bayan na idar da sallar asuba na fito nayi aiki na kamar yadda na saba no koma daki na kwanta don gudun haduwa da kabir kamar ko yaushe.

Karfe goma na safe na fito bayan na tabbatar ya fita amma abun mamakin sai banga takarda kamar yadda ya saba ajiye min ba ban kawo komai a raina ba illah ko yana sauri ya manta don haka na shiga kitchen na debo abinci bayan na fito ne naji karar fadowar abu daga dakin sa.

Ban damu ba don ba shiga dakin nake ba dan haka babu abun da zai sa na shiga na koma na zauna na fara cin abinci ban yi nisa da hakan ba naci faduwar abu wannan karan hade da kara wanda na tabbatar kabir ne.

Ban bata lokaci ba na shiga dakin ciki gaggawa don ganin me ke faruwa sai dai abun da na gani baiyi kyau ba, don kuwa kabir ne kwance rike da ciki yayi kaca kaca da komai na dakin wanda ya janyo masa jin ciwo jini yana fita a bangare da shashe na jikin sa daban daban.

Ban san lokacin da nayi tsalle naje gefen sa ina tambayar sa me yake faruwa, amma sam ban samu amsa daga wurin sa ba illah ci gaba da juye juyen da yake yi.

Wayar sa na dauka naci saa kuwa babu cord dan haka na bude na duba sunan Ahmad kira biyu ya daga tare da fadin kai angon karya ina ka tsaya ne kasan kai muke jira.

Kabir kabir jini shine kawai abunda nake iya fada masa ta cikin wayar, khadija lafiya, kabir kazo jini, nidai har lokacin abunda baki na yake iya fada kenan.

Bai tsaya sake jina ba ya kashe wayar, nidai durkushe nake na kasa aikata komai sai ruwan sannu kawai da nake masa tare da goge masa gumin da yake ta tsatsafowa a saman goshin sa.

Mintuna da bansan nawa ba naji bugun kofa, cikin hanzari hade da tashin hankali naje na bude kofar Ahmad ne tsaye tare da wani wanda ban tsaya duba ko wanene shi din ba.

Dakin muka koma cikin wannan halin muka same shi, salis tayani daga shi. Shine kawai abunda Ahmad ya fada suka daga shi ban tsaya bata lokaci ba na dauko hijabi na bi bayan su.

Ahmad shi ya rufe kofar sannan yaja motar muka tafi.
A asibiti muna isa aka shiga dashi emergency room.

Tabbas ranar itace rana ta farko da na ji haushin irin rayuwar da nake ko ba komai mijina ne ban san tun yaushe yake cikin wannan halin ba tabbas da ace ya mutu a ranar bazan taba yafewa kaina ba. Shi yasa nayi alkawarin canza tsarin zaman da nake dashu.

Wannan shine hukunci mafi alkairi wanda yazo tare da rashin sa, shine hukuncin da ya kawo min farin ciki rayuwata sannan ya bani bakin cikin da ban taba dandanashi a rayuwata ba.

Hukuncin da ya zamo min laifi daya tak a rayuwata.

See i told you, more is coming just push that botton and give some comment
Vote
Share.

LAIFI DAYAWhere stories live. Discover now