Happy independence day country.
I know i am not suppose to write cuz i have exams tomorrow. But i love you so much that i have to write for you.
Pray for me cuz i truly need it.Nasan hakan sai ta faru kabir. Na fada maka wannan ba game bane amma sam kaki yarda yanzu wa gari ya waya kabir.
Idanuwansa a kankan ce ua juyo ya kalli Ahmad me yasa ka kasa gane abun da nake fada maka ne ta tafi. Ba tone tone nake so ba kawai ku bani shawara.
Ilyas ne ya kalli kabir ka riga kabar shawarar ka a can baya. Tun a lokacin da kayi amfani da su da yanzu ba'a zo wannan gabar ba amma kayi watsi da m....
Shut up ilyas ya isa maganganun da kuke fada min haka idan baku da abinda zaku fada min gara na tafi. Key din sa ya dauka ya fita zuciuarsa yake ji kamar zata fito tsabar wani irin bugawa da take yi masa shin ina zaije ya samu saukin wannan abun da yake damunsa. Kansa ya kifa a jikin motar yana sauke wahallalun ajiyar zuciya.
Ahmad ne ya dafa shi yana bubbuga kafadar sa alamar ban hakuri. Kallon yadda idanunsa suke rine ya fita hayacci sa a lokacin kadan tabbas shi shaida akan irin soyayyar da kabir yakewa deejah tare suke kwana su tashi yasan komai nasa shin me yasa bazai tausaya masa ba yasan yayi babban kuskure wanda bazai taba kankaruwa ba amma ai dole akwai maslaha. Me zai hana kaje wurin papa.
Da sauri ya dagotare da bude rinannun idanuwansa wanda da gani kasan akwai abubuwa wanda bakin bazai iya furta su. Wayarsa kawai ya mika masa don yana kan sakon da papa ya turo masa tun jiya.
Inalillahi waina illaihi rajiun. Abunda bakin Ahmad yake iya furtawa kenan har ya samu shima ya jingida da motar kabir din. Shesheka kawai yaji ya dago a razane. Kafadunsa ya rike yana bubbugawa kayi hakuri kabir dole ka basu lokaci su huce. Shawara daya ce kayi yadda yace kawai a yanzu daga baya idan sun sauko in sha Allah komai zai dawo daidai.
Ahmad bazan iya ba na rubuta saki da hannuna na bawa deejah wallahi ka sani bazan iya ba. Idan na aikata hakan a ranan na zama mutum mutumi domin kuwa na rabu da ruhi na ka sani Ahmad she is the reflection of my self, taya kake tunanin zan rabu da ita. Bazan iya ba.
Rike shi yayi suka koma falon nan dai suka hadu suka dinga bashi baki tare da tausar sa akan yayi yadda papa yace tunda yafi kowa sanin papa mutum ne da kullum reputation dinsa yake duba amma tunda yanzu ya yadda mutuncin nasa ya zube a idon mutane to tabbas abun ya kure.
Papa yaushe ka shigo. Tashin ta daga bacci kenan wanda bata san lokacin da ya dauke ta ba.
Banfi minti biyar ba. Tashi ki zauna muyi magana. Yana kallo ta tashi ta zauna fuskarta a kumbure ido yayi luhu luhu tabbas ta kwana tana kuka kamar yadda ya kwana bai rintsa ba.
Nayi tunani akan maganar da kikayi jiya akan barin gari.
So na yanke shawara zaki tafi Jeddah kawai. A can zaki fi samun nutsuwa.Papa na gode sosai Allah ya kara nisan kwana Allah ya kara budi. Am so happy. And tashi tayi ta dauko wayar ta ta bude masa result dinta ta mika masa.
First class deejah. Congratulations dear Allah yasa Albarka yasa rai akayiwa. Sai kiyi applying masters a can kawai.
Papa Abdallah da Aisha fa?
Ki fara tafiya idan sun gama term sai a kawo miki su a sama musu makaranta a can suma.
Da sauri ta rungume shi tana kuka. Na gode papa Allah ya saka da alkhairi. A dan wannan lokacin ta manta da komai sai farin cikin da mahaifinta ya sata.
Ba komai deejah na i can do anything for you. Allah ya miki albarka.
Amin papa na gode.
Short chapter, i know i promise two chapters tomorrow. Don't forget to
Comment
Share
Vote
AmminA3
YOU ARE READING
LAIFI DAYA
Misterio / Suspensolabarin matashiya da ta samu matsala a gidan auren ta, a dalili cin amana , shin ya rayuwa zata kasance zata zauna ko kuma zata tafi. ku biyo ni don jin yadda labarin Deejah da Kabir zai kare a dalilin LAIFI DAYA TAK.