Hello dearie's i know its been a while. What can i say just sorry but now am back fully in sha Allah,so let go writing. And yes from this chapter on its all flash back of the story. Only few line will be present.
Khadija yusuf shine asalin suna na amma anfi kira na da deejah kamar yadda kuka sani, mahaifina Alhaji yusuf usman dan asalin garin ningi ne ta jihar Bauchi. Yana da mata na aure biyu mahaifiyata ita ce matar sa da fari sai mama balki.
Yana da yara goma sha daya amma mu tara ne a raye. Ni ce kuma ta bakwai.
Mahaifiyata haj zainab ta haife mu shida, ya sadiqa, ya amina, ya khalid, ya usman, ya Ali, sai ni ce kuma ta shida wato auta.A dakin mama balki ya faisal, sai yan biyun ta hasana da hussaina wanda kuma sune kadai kanne na sauran biyun da ta haifa sune suka rasu sai daya a dakin mu.
Tabbas mun taso cikin gata damin papa mutum ne mai son yayan shi kowa ya san da hakan amma matsalar sa daya ce mutane me zasu ce.
Wannan kullum itace matsalar papa ya tsaya akan yayan sa yana bamu kulawa yana mana duk abinda uba ya kamata ya yiwa yayan sa amma kullum idan bukata taka ce ta kanka sai ya ce anya hakan bazai jawo zubewar mutuncin sa ba.Nayi primary school dina a jibril aminu yadda daga can na shiga sky crest model school. Ina da kyau namu na hausawa ko kusa ni ba fara bace amma baki na mai kyau ne ina da oval face da karamin hanci wanda ya dace da fuska ta haka baki na shima karami ne ina da tsayi daidai gwargwado.
A lokacin da muke zana junior waec dina muka hadu da Ahmad.
Ahmad matashin saurayi ne dan asalin garin gombe ne, yazo service dinsa yana koyarwa a makarantar mu. Shakuwa da soyayya mai karfi hadi da yarinta sune suka rufe min ido bani da zancen kowa sai na ahmad har muka gama jarabawar mu. A ranar kuma na cewa Ahmad duk lokacin da na samu dama za mu dinga haduwa ko na kira shi da wayar wani a gidan mu.A lokacin da muka zo komawa makaranta ne papa ya canza mana makaranta zuwa International secondary school babu yadda na iya doke muka koma hakan baisa mun daina haduwa da Ahmad ba musamman da ya kasance makarantar a cikin university take toh ba matsi da yawa.
Hajia babba kakata mahaifiyar mama itace na fara bawa labarin Ahmad lokacin bikin ya sadiqa da ya amina.
Duka duka lokacin shekara na sha hudu ne a duniya hajia babba ta bani shawara sosai yadda zan bi komai a hankali, sannan kar na biye masa idan yazo min da wani abu na batanci ta kuma min fada akan haduwar da mukeyi a makaranta.
Lokacin da na shiga ss2 papa ya saya min waya tuni Ahmad ya koma gombe amma muna yin waya a wayar mama idan ta ajiye zan dauka na kira shi.
Shi na fara kira nan fa hanyar hira da chat suka bude ba dare ba rana.Rayuwa kenan kana naka Allah yana nasa, ban taba sanin kabir ba ban san ma yana rayuwa ba ko a hanya ban taba ganin mai kama dashi ba a daidai lokacin da muke WAEC a lokacin rayuwata ta zuya komai ya faru kamar a mafarki.
Muna sanun matsala da Ahmad akan lalle sai ya turo gidan mu nace ya bari har sai na gama exams idan yazo officially kowa ya ganshi kafin nan sai ayi maganar manya su shiga.
Ya amince da hakan har na kammala jarabawa da sati biyu Ahmad yasa ranar zuwa gidan mu.Hajia babba ita na nema na sanar mata, ita ta kira mama ta fada mata nasha fada kam a wurin kowa ma ranar ba don zan kawo saurayi ba aa sai don ba wanda yasan ina kula wani balle har ace nace yazo gidan mu.
Tabbas na kasance mutum mai zurfin ciki na tsananin boye damuwa ko farin ciki ko wani abu da ya shafe ni ba komai nake fada ba ina da boye sirri ba karamin abu nake fada ba ko abu nake da bukata lokuta da dama sai dai mama ta yi min kawai ba don na tambaya ko nace ayi min ba, a takaice ni mutum ce mai tsananin hakuri da zurfin ciki.Papa da kansa abun ya bashi mamaki don kuwa bai taba ji ko a hira ance ina kula wani ba amma hakan ya masa dadi kowa ya amince yazo.
Ya sadiqa da ya amina su suka tayani aiki ranar muka hada abinci kala kala da lemo.Fadar farin cikin da muke ciki ni da Ahmad a wannan radar baya misaltuwa duk da karancin shekaruna goma sha shida amma na yadda na kuma amince da tsananin son da Ahmad yake min tabbas na yarda na zama tasa har ranar da zanyi numfashi na karshe.
Ahmad yaje wurin papa sun gaisa ya masa tambayoyi ya kuma gamsu da bayanan sa don yace yasan kanin mahaifin sa. Don haka daga nan zuwa ko yaushe ya turo magabatan sa ayi magana.
Wanna furuci na papa shi yafi komai faranta zukatan mu tabbas na shirya na kuma yarda na amince.
Wata daya da komawar sa Ahmad ya turo da magabatan sa suka zo neman aure na papa kuma ya basu aka saka biki wata hudu.Ranar wata juma'a da bazan manta da ita ba lokacin saura wata daya bikin mu Ahmad yazo tun karfe goma na safe bai tashi tafiya ba sai bayan la'asar, kamar kullum har bakin mota na raka shi zoben hannunsa ya ciro ya saka min ga amana ta nan ki rike min, abun ya ban mamaki domin kuwa na jima ina tambayarsa ya bani zoben nan yaki ya tabbatar min mutuwa ce kawai zata raba shi da zoben.
Kallon sa kawai nake sai naga ya sake fari ya kara kyau sosai murmushi kawai na masa tare da fadin Allah kiyaye hanya.Tun da ya tafi na kasa samun nutsuwa har aka kira sallar maghrib nayi sallah ina ta gwada number dinsa amma taki shiga har bayan isha har karfe tara. Nan fa hankali na ya tashi na kira maryam kanwar sa amma itama bata dauka ba.
Can kusan karfe goma ne abba babban abokin sa ya kira ni, wani mummunan faduwar gaba naji nan na daure na dauki wayar.
Deeejaahhhh
Yadda ya kira suna na kawai naji hawaye ya fara sauka a idona.
Sai dai muyi hakuri deejah Ahmad ya rig....Inalillahi waina illahirajiun wannan shine kadai abun da nake fada, a daidai lokacin papa ya shigo falon ganin ina kuka yasan tabbas an fada min.
Wannan ranar itace rana ta farko a rayuwata da papa ya zauna ya bani kulawa ya rarrashe ni da kalamai masu sanyaya zuciya ya kwantar min da hankali na na samu nutsuwa a wannan lokacin.
Washegari tun asuba muka tafi gombe dasu papa aka kai ahmad makwancin sa. Zoben da ya bani kawai nake murzawa ina hawaye kwanan na uku a gombe papa yasa aka dauko ni dawowar da ta zama kaddarar rayuwata dawowar da tasa na fada cikin duk wata matsala ta rayuwata dawowa daga rashin masoyina na gaske na fada hanun masoyi na karya dawowar da bata kawo min komai ba sai akasarin bakin ciki da damuwa.
Kiran sallar magriba ne ya katse musu labarin da ake yi. Don haka Ahmad ya tashi ya tafi masallaci suma matan kowa ya tafi sauke farali.
Bayan sun idar da sallar ne hajia babba tace yanzu kam ki huta sai kuma gobe kukan da kikayi yanzu ma ya isa bana so ki kara wani.Asma tace kai hajia babba sai da labari yazo wurin dadi kuma
Ahmad yace nima ina da aiki don haka sai gobe kawai.
Okey how was it
DK is coming hope you enjoy it
See you tomorrow
Vote
Comment
Share
AmminA3
YOU ARE READING
LAIFI DAYA
Mystery / Thrillerlabarin matashiya da ta samu matsala a gidan auren ta, a dalili cin amana , shin ya rayuwa zata kasance zata zauna ko kuma zata tafi. ku biyo ni don jin yadda labarin Deejah da Kabir zai kare a dalilin LAIFI DAYA TAK.