CHAPTER 9

12 1 0
                                    

Sorry guys.

Ranar kwana nayi banyi bacci ba tsabar zafin zazzabi da tsannin sarawar da kaina yake yi.

Da kyar na mike naje nayi alwala na dawo kasa tsayawa nayi  sai a zaune nayi sallah saboda jiri da yake diba na.

Ban san ya akayi ba na bude ido na kawai na ganni a gadon asibiti hajia babba na gefe na.

Kwana na uku a asibiti aka sallame ni naso hajia babba ta zo mu tafi tare amma sam taji ta tabbatar min ma a ranar ma zata tafi.
Babu yadda na iya haka na dawo gidan na samu koina tsaf a gyare kamshin turaren wuta sai tashi yake.

Kayana da suke a akwati duk an jera min su a cikin drower, abun ya bani mamaki amma haka dai nayi shiru tunda ba iya tambayar sa zanyi ba.

Bandaki na shiga nayi wanka da ruwa dan daidai kafin na fito na shirya cikin riga marar nauyi.

Abinci ya shigo dashi a jere akan tray ya ajiye akan table din gaba na, da kansa ya zuba min dan daidai sannan ya miko min amma ban iya ko kallon yadda ya ajiye ba da kyar ya lallaba ni ya hada min ruwan tea ya ajiye sai bayan ya fita na dauka na sha.

A haka muka ci gaba da rayuwa har tsawon wata daya kullum idan zai fita zai bar min dan rubutu na cewar ya fita hade da kudi a cikin takardar. 

Zan yi kokari na kammala duk aikin da zanyi kafin ya dawo don bana son haduwa dashi amma duk da haka idan ya dawo sai ya shigo ya duba ni ya tanbaya ko akwai abinda nake bukata amma kullum amsar daya ce babu.

Lokaci yana tafiya abubuwa suna yadda suke daga gaisuwa ba abunda yake hada ni dashi har sai ranar wata jumua bazan manta ba ita tayi sanadin da na fara kula shi har komai ya canza.

Okey i dont know what to say.
Just
Comment
Vote
Share

LAIFI DAYAWhere stories live. Discover now