Assalamu alaikum my lovelies. Hope you all are doing good. Exams over i am now a free bird, and your girl is potentially in level 3.
So who is excited lets the story continues enjoy.Yusuf Yusuf!! YUSUF, a razane ya dago ya kalle ta.
Haba Alhaji wane irin dogon tunani kake yi haka tun dazu nake shige da fice a dakin nan amma baka san ina yi ba, yanzu nafi minti biyar akan ka ina magana amma baka san ina yi ba, kar fa wannan yawan damuwar da kake yi ya jawo maka wani ciwon da zai zama matsala a rayuwar mu baki daya.
Fatima ya kira sunan ta cikin tsananin kulawa da muryar sa na nuni da tarin bacin rai da yake ciki hannunta ya kama ya riko tare da zaunar da ita a gefrn sa.
Fatima ki yarda dani wallahi ban taba tunanin haka zai faru ba ban taba tunanin zasu wulakan ta min ya ba shin ta yaya zan fara bak.....
Shhhhhhh hannu ta dora akan labban sa na yarda da kai na amince da duk komai tun ba yau ba, nasan bazaka taba kaita wurin da zata samun matsala ba. Ko ka manta da kaddara ne me yasa kake wahalar da kanka akan abun da kasan bazai taba canzuwa ba.
Ina gani da na bata fuska tana fadar matsar da take ciki da haka bai faru ba, na hana su komai... anya fatima na cancanci zama uba
Ya isa yusuf kai uba ne na gari su kansu suna alfahari da kai wallahi dee tana da zurfin ciki wallahi ba komai ne zata fada ba.
Don haka ka bar maganar kawai Allah yasa hakan ne mafi alkairi.Fatimaaaa sunan ta ya kira tare da sake matse hannunta cikin nasa, idonsa yana kallon cikin nata.
Ina son idan ba damuwa hajia babba ta tafi wurinta su zauna tare tan dan debe mata kewa da sauran su.Idonsa ta kalla sosai akwai abu uwan da yake son fada amma ya kasa, abun da nake tunani ne ko wani abu daban.
Murmushi yayi ya kada mata kai, zata fara therapy na samu dan gidan Doctor Ahmad zai na zuwa gida insha Allah komai zai zo da sauki.
Therapy ta kalle shi idonta yana nuna almar tambaya, idan fa akwai matsala ni zan iya tafiya wurinta abar hajia babba.
Trust me it's nothing serious, kawai ina ga da session din zata fi saurin cire abun a ranta, damuwar zata ragu. Sai ki samu ki kira hajia anjima idan ta shirya zuwa jibi sai ta tafi.
Kwance take a falon idonta na kan tv amma tunani da duk ruhi na jikinta basa tare da ita. Yau kwananta uku kenan da dawowa gidan da Papa yasa aka sama mata. Daki biyu safe content sai falo kitchen da store.
Bugun kofar da ake hade da kararrawa ya dawo da ita duniyar da take, da sauri ta bude kofar ganin bakuwar fuska namiji yasa tayi saurin tura kofar.
Magana yake son yi amma tayi wuf ta rufe.Kara wayarta tayi ta duba PAPA ta gani a jikin wayar ta danna amsa sannan ta kara a kunne.
Papa barka da rana.Akwai bako da zai zo doc ne shine zai na duba ki da komai ma, give him a chance please dee. Ki cire komai a ranki ki sake da shi.
Kofar ta bude ta koma ta zauna suna magana da papa, ya samu dai ya shawo kanta da kyar ta amince. Ya sanar mata cewa dan gidan uncle Ahmad ne.
Tun da ya zauna bata ce masa komai ba haka shima, da yaga dai da gaske bazatayi magana ba yasa yayi gyaran murya.
Doctor Usman Ahmad, da fatan zaki bani hadin kai komai yazo da sauki.
Insha Allah, baka da mata ne?
Ina ta ida.
Next time kazo da ita ban yarda da maza ba idan kana so komai yazo mana yadda yake so kazo da matar ka then i will cooperate.
Daga haka bata kara komai ba ta tashi ta shiga daki.
Yafi minti ashirin yana jira ko zata fito amma shiru dole ya hakura ya tafi.A hanyar sa ta komawa asibiti ya kira papa ya fada masa duk yadda sukayi.
Hakuri papa ya bashi yace yaje da matar tasa ba komai tunda ita ta bukaci hakan don da gaske a yanzu kam bazata yarda da kowanne namiji ba.
Usman ranar wuni yayi yana tunanin shin me namiji ya yiwa dee da har ta hadu ta musu kudin goro har likita bazata yarda dashi ba, tabbas ya matsu gari ya waye yaje wurinta.
Matarsa Asma ita kanta abun ya daure mata kai tabbas zata so jin wannan labari itama.
Kwance take a daki taji bugun kofa ta fito tazo ta bude, ganin hajia babba yasa ta buga tsalle ta makale ta tana dariya. Hajia kaka ta oyoyo shine baki fada min zaki zo ba.
Ina fa zan fada miki babanki ya kade min hankali ko shirin kirki baa barni nayi ba, an tabo sha lelen sa.
Kai hajia ba wani sha lele kawai dai tausayi na papa yake ji, daga haka ido ta ya fara zubar hawaye nan ta shiga kuka ba wasa hajia babba na lallashinta har tayi mai isar ta.
Hajia ta mai kike so na dafa miki yanzun nan kiga aiki da cikawa.
Dariya ta mata ni nasaki aiki ubanki yazo ya daureni a kasar mutane, tafe nake da abinci kema ga naki nan ai yanzu kam sai dai na dafa na baki. Da fatan ma dai kina cin abincin.
Kararawa suka ji ta tashi da sauri taje ta bude, tsaye take shi kuma na bayanta.
Tare suka shigo suka gaisa nan yace zai je ya dawo hajia babba ma tace zata shiga daki ta kwanta.
Amra da dee suna taba hira har lokacin da usman ya dawo bayan sallar laasar.Deejah are you ready.
Yes!
Dan dan dan
Who can't wait also for the drama
Okey i am back dusted all the papers thank you for the prayers and you know i love you.See you
AmminA3
Comment
Share
Vote.
YOU ARE READING
LAIFI DAYA
Mystery / Thrillerlabarin matashiya da ta samu matsala a gidan auren ta, a dalili cin amana , shin ya rayuwa zata kasance zata zauna ko kuma zata tafi. ku biyo ni don jin yadda labarin Deejah da Kabir zai kare a dalilin LAIFI DAYA TAK.