CHAPTER 8

24 2 0
                                    

Just sorry.

Ranar a jiki hajia babba na kwana duk motsin da zanyi sai ta tambaye ni ko lafiya.

Karfe takwas na safe Dr Ahmad da matarsa suka iso, hannunsu rike da ledoji na gidan abinci sai wata yar kula ta abinci ita ma.

Hajia babba Asma ta bawa kular sannan ta ajiye min ledojin a gaba na.
Ki ce abinci mu fara jiya da kyar nayi bacci har mafarkin labarin nake deejah.
Dariya mukayi muka ci abinci zuwa karfe tara kowa ya zauna.

    Bayan na dawo gida da kwana uku ina zaune a daki kamar kullum naji wayata tana kara na duba naga papa ne ina amsawa yace na same shi a dakin sa.
Tun da na taho kirjina yake bugawa haka kawai hankali na ya kasa kwanciya da kiran da papa ya min Adua kawai nake duk wanda tazo min.

Zaune na same shi a kan kujera yana duba wani littafi, sallama nayi na shiga sai da na samu wuri ya zauna sannan nace masa papa gani.

Kiran da ya canza rayuwata kiran da ya kawo bacin rai, bakin ciki farin ciki da kuma nutuwa babu abinda kiran nan bai zama sanadin sa a rayuwata ba domin na tsinci komai cikin harda abun da nafi so a duniya 'ya'ya na.
Kiran da ta dalilinsa aka yi min laifi daya tak da ya canza rayuwata, ba don ba'a taba min laifin ba sai dai shi ya kunshi cin amana da tozarci.

Papa ne ya gama jawaban sa ya tabbatar min da ranar aure na yana bai canza ba ko da awa daya, na shirya Kabir zai zo anjima.

Daki na koma tun daga lokacin da papa ya sanar min da zuwan kabir na fara hawaye har yanzu da nake shirin fita domin kuwa papa ya aiko na je falon bakin sa Kabir ya iso.

Tun da na shiga naji alamar ido a kaina amma ban dago ba har na samu kujera ta nesa da shi na zauna a lokacin ne naje an min barka da zuwa, dagowa nayi ganin mutum uku yasa na tsaya ina binsu da kallo.

Ni suna na Ahmad babban abokin Kabir wannan kuma Idris dama muka ce bari muzo mu gaishe da gimbiya mu zamu tafi.
KB sai kazo.

Wanda aka kira da kb din na kalla ido muka hada nayi saurin dauke nawa idon.

Ina yini na gaishe shi
Kina lafia khadija ya karin hakuri.

Ji nake a lokacin kamar na shako wuyansa kawai amma na nutsu na amsa masa.
Shiru na dan lokacin ya biyo baya.

Uhmm khadija nasan abun ya zo miki a bazata ni kaina ban so ace lokacin ya zo a matse haka ba amma manya sunki yarda da fatan zakiyi hakuri muyi komai na shirin biki saboda raahin lokaci.

Insha Allah kawai na iya ce masa nan dai yayi ta surutun sa har karfe tara da rabi kafin ya tafi bayan ya karbi number na.

Shirye shiryen biki aka ci gaba da yi babu wanda ko sau daya ya tambaye ni halin da nake ciki.
Haka kabir ma tun ranar bai sake zuwa ba sai dai yakan kirani a waya lokaci lokaci.

Sati daya ya rage biki mai gyaran jiki tazo, naso naki amma hajia babba ta lallaba ni sai da aka min.

A wurin hajia babba kadai nake samun tattalin da nake so a wurinta kadai nake samun kafadun da zanyi kuka, ita kadai ta damu da halin da nake ciki, ita kadai tasan rudani da nake ciki.

Ranar asabar na watan shida shekarar dubu biyu da sha biyu aka daura aure na da Kabir Usman Bawa.

Message ne ya shigo waya ta lokacin ina zaune da dora kaina akan kafadun hajia babba tana min yan nasihohi yadda ya kamata.

Alhamdulillah an daura Allah ya bamu zaman lafia. KB

Bansan lokacin da hawaye ya fara zubowa a ido nan ba, a daidai lokacin mata suka shigo suka fara guda tare da sanya albarka.

Wuni nayi ina kuka don haka zuwa lokacin da aka zo kaini gidan su zazzabi ne mai zafi a jikina.

Papa da kansa ya shigo ya bani alkaybba na saka ya rike hannu na a motar sa daga ni sai shi.

Bai ce min komai ba har muka isa ya zagayo ya bude min kofa ya rike hannuna har falon gidan ina jin muryar maza amma ban san su waye ba.

Alhaji isa ga amana na kawo idan khadeejatu tayi ba daidai ba kaima uba ne a gareta ka mata fada sannan a rike min amana.

Tashi naga yayi da sauri na riko kafarsa ina kuka papa dan Allah kar ka tafi ka barni a nan.

Tsugunnowa yayi ya rungume ni Allah ya miki Albarka deejatu na Allab yasa gidan zamanki ne kiyi hakuri.

Wata yar jaka ya damka min a hannu na ya tashi ya tafi.

Kuka nake sosai hakan ya kara min zafin zazzabi ga kaina kamar ya rabe gida biyu tsabar ciwo a haka su aunty da hajia babba suka shigo su suka kaini daki.

Kwanciya nayi bayan na samu nayi sallah da kyar.

Farida ita ta kira kb ta fada masa bani da lafiya, da sauri ya ahigo dakin yaso muje asibiti amma ko kallonsa banyi ba balle na bashi amsa. Haka ya hakura ya tafi ba jimawa naga ta kawo min magani wai nasha.

Tabbas ba don azabar da nake ji ba da ba abunda zai sa nasha maganin nan amma haka na daure nasha.

Washegari da yamma akayi budan kai. Ana gamawa aka kaini gida na dake unguwar jahun.

Gida ne madaidaici daki biyu sai falo kitchen da store sai gareji na ajiye mota.
An shirya komai yayi das amma ni ba wannan ne ya dame ni ba.

Bayan an watse kabir ya shigo hanunsa da ledoji niki niki ya ajiye a kasa, ya zo gefen gadon ya zauna. Deejah ya jiki.

Kai kawai na daga masa, ki daure ki tashi kici abinci sai ki kwanta.
Kai na sake girgiza masa da naga yana shirin damuna da magana kawai na fara kuka.

Hakuri ya bani ya min sallama ya tafi bayan ya kwashe kayan da ya shigo dasu ya fitar.

Ranar kwana nayi ina kuka.

Vote
Share
Comment
AmminA3

LAIFI DAYAWhere stories live. Discover now