CHAPTER 5

28 4 1
                                    

I am so sorry lovelies, i know i made a promise but you all know how school can be hectic. And wedding also, happy married life sister pipi we love you so much.

Ok are you all ready for the bomb to explode, not now we have some chapters more before that anyways enjoy.

Kabir, ilyas tare da hamisu zaune a falon papa suna jiran shigowarsa. Sallama yayi ya zauna sannan suka gaishe shi babu komai a fuskar sa da zaka gane yanayin da yake ciki.

Ilyas ne ya fara magana, Papa dama munzo ne dan Allah idan da hali ka janye kudirinka na....

Dakata ilyas ba abunda zaku fada min dukkan ku, ya dago idanuwan sa da suka kada suka canza kala zuwa ja, babu  komai da nake so a yanzu banda a bani takardar 'ya ta.

Amma papa hamisu ya dora....

Lah na fada muku babu abinda nake son ji daga wurin ku domin duk kanku macuta ne maciya amana, kun mata rana irin wannan da kuka zo min da bukatar abokin ku na cika masa burinsa. Mai zai hana nima yau kusa ya cika min nawa burin.

Ahmad ne ya matso cikin tsananin bugun zuciya tashin hankali karar a kan fuskar sa idonsa shima jajayur, Papa dan Allah ka taimaka ka rufa min asiri kar ka rabamu.

Dariyar takaici ne ko bakin ciki ita ta kufcewa papa. Kabir gashi.
Biro da takarda ya mika masa. Wannan shine kawai zai kawo mana.

Hannunsa na rawa ya karba don bai taba ganin irin wannan bacin ran akan fuskar papa ba. Tabbas ya kai mtanen nan makura ina ma lokaci zai koma baya ya gyara wannan LAIFI DAYAN da ya aikata.
Haka ya karba ya rubuta saki daya ya mikawa papa.
Dishi dishi ya fara gani bayan ya mike kafin ya karasa kofa tuni ya yanki jiki ya fadi.

Ilyas tare da hamisu ne suka dauke shi sai asibiti. Ahmad suka fara kira sannan suka kira Baba a waya. Kai tsaye ya fada musu bazai zo ba. Hakuri hamisu yake bashi amma kit ya kashe wayar sa.
  Uncle ya kira ya fada masa. Tare da ahmad suka iso dakin suka wuce. Nan suka fada masu duk abinda ya faru.

Papa da kansa ya kaita Airport bayan taje makaranta taga su Abdallah.
Nasiha sosai papa ya mata kafin jirginsu ya tashi.

Saudi Arabia, Jeddah
Hyaat house a nan deejah ta sauka. Dakinta mai lamaba 236 nan ta shiga wanka ta fara yi sannan tayi sallolin da ake binta nan ta zauna tana ta karanta Qur'an har akayi isha. Papa ta kira ta sanar masa isowar ta suka yi hira. Nan yake fada mata cewa ta kira Mamin ta ya riga ya sanar musu komai.

Kabir kwanan sa biyu baisan yadda yake ba sai a na uku sannan ya farka. Dee kar ki tafi ki barni dan Allah kin san ina son ki ki yafe min.

Ahmad ne ya kira doctor yazo ya duba shi allurai ya sake masa. Ya tabbatar musu idan ya farka zai dawo normal.
Hankalin su baki daya a tashe yake ba wai rashin lafiyar Kabir ce tafi daminsu ba a'a kin magana da Baba ya musu yace ahi ba ruwansa a hidimar sa tunda bai dauke shi da mutunci ba. Wannan shi yafi komai daga musu hankali.

Papa zaune a falo ya hada dukkan 'yayansa sha biyu da matansa guda biyu. Cikin tsananin bacin rai da nuna damuwa da dana sanin abubuwan da ya aikata ya sanar musu komai har barin deejah kasar. Abu daya ne bai sanar musu ba shine kasar da take.

I know its short, but what do i do i typed a long chapter and my boy deleted everything.

Just show some love

Comment
Vote
Share
AmminA3

LAIFI DAYAWhere stories live. Discover now