*HASKE WRITERS ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33**3*
Nisawa yayi ya sauke ajiyar zuciya ya dubeta a karaye, "kina ganin raba ummaty da zainul shi zaisa kisamu cikar burinki na ganin cewa zainul abideen bashida sauran amfani a masarautar Nan da doron kasa?idan har kikace sai na raba ummaty da zainul abideen zanyi hakan Domin cika umarninki Amma kisani boyayyen kudirinki da nufinki bazai cika yadda kikeso ba Domin ita yarinyar itace jigon tafiyar Nan da mukeyi,rabata da zainul abideen zai kawo cikas a wanan tafiyar da muka dauko muna gab da samun nasara"
Kallonsa tayi na dan wani lokaci Sanan da kauda idonta kamar bazatace wani abuba sai ya tsinkayi muryarta "ta Yaya kake ganin tafiyar bazata yuwuba sarkin dawaki?"
"Idan muka Raba yaran Nan babu hanyar da zamuyi amfani da ita wajen bashi magungunan da muke bashi,ko kin manta cewa ummaty ce take bashi magani idan ankarbo?ko kece Zaki bashi idan anrabasu?kisani idan na rabasu to wallahi baki isa ni kisani kice nine zan cigaba da wanan aikin na hatsari ba don itanma dabara nayi Mata yasa kikaga komi Yana tafiya daidai yadda mukeso"
Juyowa tayi wanan karon Tana fuskantarsa fuskarta Babu annuri tamkar Bata taba dariya ba a duniya cikin kakkausar murya wanan karon ta Soma magana,"naji na amince da dik bayaninka na fahimceka Amma kasani wallahi tallahi bazan taba amincewa soyayya ta kullu tsakanin yaran Nan ba,idan har hakan ta kasance to har Yar taka zan batar da ita a doron kasa"
Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa Nan da Nan jikinsa yayi sanyi Jin abinda tace"Babu soyayya a tsakanin me lafiya da nakasasshe,sanan babu soyayya ko aure tsakanin me hankali da Wanda bashida hankali Wanda bashida sauran amfani a wanan duniyar,bazan taba lamunta diyar Dana Haifa a cikina me cikakken koshin lafiya ta auri wanan nakasasshen kotayi soyayya dashi ba,Dana fahimci hakan nidakaina zanyi amfani da almakashi in datse alakarsu Dan Haka ki kwantar da hankalinki ummaty batakai shekarun da zata kulla soyayya yanzun ba dududu kwaya nawa take?inaji yanzun ne zatayi shekara goma Sha bakwai shi kansa zainul din Ina ashirin da biyu yake?Babu Hadi"
Ajiyar zuciya ta sauke Ta tsugunna ta dauke hand bag dinta dake gefenta ta zuge zip din Jakarta ta ciri wrappers din kudi Yan dubu dubu guda biyu dubu dari biyu kenan ta Mika Masa "ga sadakin ka Nan buri na be wuce in bude Ido Inga gawar zainul abideen ba dikda boka ya sanarmun da cewa mutuwarsa tanada wahala,to tunda bazai mutuba ya dawwama a kwance har karshen rayuwarsa"....Tana Gama magana ta juya Tai hanyar fita abinta,
Kudin da ta Mika Masa yake bi da kallo zuciyarsa cike da fargaba
**********
"Ya zainul kagafa yamma tayi Kuma munyi karatu gobe Insha Allahu zan Kara maka a inda na tsaya yanzun zanyi Shirin tafiya gida sai idan Allah ya kaimu gobe ko?"Canja fuskarsa yayi Nan da Nan ganin tanata Shirin tafiya gida ta barshi kusan dik lokacin da ummaty zata tafi gida to Nan da Nan fuskarsa takan nuna damuwa a kwayar idonsa,Tana Shirin daukar Jakarta ta waigo ta dubi inda yake kwance miyau na gudu a bakinsa suka hada Ido taga kamar hawaye a makale a Ramin idanuwansa,...tausayinsa ne ya lullubeta taji jikinta yayi sanyi ta janyo kujerar gaban gadonsa ta zauna dafdashi Tana Kara kallonsa cikin tausayawa, "ya zainul kardai kacemin abinda nake gani a kwayar idonka hawaye ne na tafiya da zanyi inbarka?Koda na tafi akwai masu kula dakai ya zainul Kuma gobe zanzo kaji?"ta karashe maganar idanuwanta cike da kwalla saboda tausayinsa,...ga mamakinta sai ya Shiga girgiza kansa alamar be yarda ba,
Numfashi ta sauke tasan zaayi haka musamman yau da suka wuni ita dashi batare da ciwonsa ya motsaba tasan inhar zata tafi sai sunyi drama gashi kuwa,ganin ya kafeta da Ido yasa ta boye kwallar dake makale a idanuwanta,"kaga kayi hakuri ya zainul bazai yuwu in kwana a wajenka ba kaji?Amma Ina Mai tabbatar maka da insha allahu da kaina zan tasheka a bacci gobe saidai ka tashi ka ganni nayi maka alkawari kaji ya zainul?umm?ka yarda?
Gyada Mata Kai yayi Yana murmushi,itama murmushin ta maida Masa ta Mike ta dauki Jakarta tabi hanyar kofa ya bita da kallo harta bace sanan ya rufe idanuwansa shikadai a daki Dan fadawan dake kula dashi wani lokaci sukan fice su barshi dagashi sai ummaty
*******
"Meya hanaki bacci har wanan lokacin rumana?"Mai martaba ya jefo Mata wanan tambayar Yana karasa shigowa cikin dakin Yana sanye da Yar shara irinta sarakai ya nemi gefen gadonta ya zauna,
",Ki duba kigani yanzun kusan karfe goma Sha biyu da rabi na dare har yanzun Baki bacci ba ko akwai wani Abu ne?"..
Fuskarta Babu walwala ta dago idanuwanta ta dubesa a raunane sanan ta maida kanta kasa ta dukar "Haka kawai na rasa samun sukuni cikin Daren Nan,tunanin yaron Nan zainul ya hanani sukuni inaso ingansa Inga halin da yake ciki yanzun"....murmushi yayi irin na manya ya rungumota jikinsa Yana shafa kanta a hankali "haba rumana zuwa yanzun ya kamata kisaba da rashin lafiyarsa tunda ya dauki shekaru Yana wanan ciwon kusan tun bayan haihuwarsa,nikam Banga sabon abuba a wajen ciwon Dan naki"
Kwantar da kanta ta karayi a kirjinsa Tana sauke numfashi "muje ki ga Dan naki kinaso?"...da sauri ta daga Masa Kai alamar ehh ,girgiza kansa yayi yana murmushi rumana Bata girma dikda ta girma ta haifi yara Amma kullum jinta take kamar karamar yarinya,Haka ya tasata a gaba suka nufi sashin yarima zainul,
Rike suke su biyu da zainul dukkansu bacci ne a idanuwansu Amma Babu damar yi saboda yadda zainul abideen ya Bata jikinsa gabaki daya da amai da yayi Wanda sukansu basusan dalilin Aman NASA ba,su kansu sun gaji dashi,suna Shiga dakin fadawan suka zube a kasa suna kwasar gaisuwa,
Ganin halin da zainul ke ciki yasata saurin karasawa ta rukosa jikinta ta Shiga share Masa jiki da kanta da Dan karamin towel din dake wajen ,Mai martaba Yana tsaye Yana kallon yadda take rungume da zainul abideen ko kazantar jikinsa bataji batadamuba ta tsaftace Masa jiki kawai takeyi ita,Saida ta kammala gyara Masa jikinsa ta juyo ta dubi inda Mai martaba ke tsaye hannunsa rungume a kirjinsa ta dubesa a raunane ya sakar Mata murmushi kawai ta sadda kanta kasa hawayen da take boyewa suna sauka a kuncinta,
Kallonta sosai zainul abideen yakeyi Yana girgiza kansa alamar tayi shiru ta Kara rungumesa sosai tanajin soyayyarsa na ratsa sassan jikinta.....
********
Yau ta kasance jumaa yaune mahaifiyar me martaba da ahalin gidan sarki suke zuwa fadar sarki kawo gaisuwa Dan Haka dik ranan jumaa zakaga cikin gidan tamkar Ana wani shaani,Zazzaune suke a babban parlorn gidan kowa ya hallara anata ciye ciye,
Yatsina fuska tayi kadan "nikam banajin zan Shiga duba zainul yau ko zakuje ni boyewa zanyi Dan banjin zan iya Kai kaina ganin wanan kazantar dake cikin wanan dakin"ta karasa maganar hade da yatsina fuska,
"Kai warisat kada ki manta ya zainul fa Dan uwanki ne be kamata ki kyamace sa ba kiduba halin da yake ciki"
Dan tsaki tayi tana dubanta cike da tsiwa"banson iyayi zahira Zaki fara Koh?kinji nace dama ba Dan uwana bane?kawaidai banida raayin zuwa dubasa ne"ta kauda kanta gefe,
Tabe bakinta zahira tayi "kedai kikasani mu zamuje mu dubashi idanke bazakije ba Kuma ya zainul a tsaftace yake masu kula dashi suna iya bakin kokarinsu sanan ummaty ma Tana tare dashi ai Yar sarkin dawaki"
"Kwadayi ne kawai yasa take makale a gidan sarauta da son asani"
Wani dogon tsaki fiyya tayi daga gefe dik hirar da cousins din nata sukeyi a kunnenta tsananin takaicin kalaman warisah ne yasa ta tabar parlorn Dan ji take tamkar ta shaketa,
*********
Karatun alkurani takeyi da muryarta Mai dadin saurare ya kafeta da idanuwa da alamar yanajin dadin yadda take karatun,....shigowarsu tawagarsu yasata zumbur ta Mike tsaye jikinta na rawa ta zube a kasa Tana kwasar gaisuwa wajen dattijuwar matar da aka shigo da ita wadda ta kasance kakar zainul abideen ta wajen uba.....wani irin kallon kyama da wulakanci warisat da zahira suke bin ummaty dashi Wanda yasata kasa tsayuwa a wajen tayi hanyar fita.....*SLIMZY😍*

YOU ARE READING
ZAINUL ABIDEEN
SpiritualBanida wani burin daya wuce Inga gawar zainul abideen akwance babban kudirina a duniya shine in bude idona Inga zainul abideen akwance baya numfashi inhar be mutuba kuwa bazan taba daina bibiyarsaba har saina tabbatar da na maidashi ga Rai babu amfa...