*HASKE WRITERS* *ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33**1*
Daga zaunen dayake saman wheel chair ya d'ago ido yana kallon ta yana saukar mata da murmushi me sanyaya zuciya, Tabare masa fuskar nan tayi wane zatae kuka
"Amma ni Yaa zain banace wai idan kanajin wannan abin ba ka dinga adu'a dan Allah" kanshi dayake a karkace ya k'ara juyarwa yawun bakin nashi suka k'ara gangarowa zuwa saman kirjin sa, da sauri ta sanya tissure ta share masa su ta wurga a kwando, lokaci d'aya k'wallan datake k'ok'ari tarewa ya silalo mata da sauri ta sanya bayan hannunta ta d'auke shi tana me kawar da kanta karya gani, wani azababben bak'in ciki ne ya taso mata ya tokare mata k'irjin ta zuwa wuya, da k'yar ta had'iyi wani yawu me d'acin gaske sannan ta furta
"Sannu yaa Zain, yanzu inane yake maka ciwo?" Kasa magana yae sabida abinda yakejin yana taso masa yana danne masa mak'oshinsa da k'yar yake numfashi ma, hannunsa yakai yana shirin mak'ure wuyansa da sauri ta rik'eshi ta soma karanto masa adu'o'in tsari tun yana k'ok'arin qwacewa harya hakura ya lafe tayi ta masa adu'a kusan 15mns ko ita gumi takeyi, seda taga ya lafe alamun yashiga duniyar bacci sannan ta sakeshi tasoma kuka wiwi tamkar wata zararriya, tausayi sosai yaa Zain yake bata d'an sarki guda d'aya, lamarinsa kullum sekace me ciwon iska, tayi wa Sarauniya maganar amasa na gargajiya amma ta kafe akan haka Allah ya haliccesa, wane ciwon ne bashida magani?" Jansa tayi zuwa cikin b'angaren sa har tsakiyar d'akinsa sannan ta kira fadawan sa suka kwantar mata dashi, kallon bafade d'aya tae tace dashi
"Nasan halin baccin sa baze wuce 1 houf ba bari zanje na dawo, idan ya farka kafin 1 hour ka aika akirani" tana gama fad'ar haka ta juya ya bita da harara, an baiwa yarinyar nan dama da yawa, harsu take commanding irin haka?.....
********
Hararar sa ta keyi sosai, yanayin kallon dake idanta kurin ya isa ya sanya kasha jinin jininka, sadda kanshi yae a k'asa cikeda rotso, besan kose yaushe ze dena tsoron ta ba, besan kose yaushe zata dena shiga rayuwar sa ba, meya mata ne wai? Aduk fad'in masarautar nan bashida abinda ya tsana da gani sama da ita, gata sekace aljana duk inda yae idonta na kasan"Idan abinda nake fahimta daidai ne kana nufin bazaka sab'awa waccem jakar ba kenan?, so kake ka nunamun kai kanada taurin kai da kafiya ko? Dacen dawa kake amfani bada 'yar taka ba! Se yanzu danka gama rainan hankali zaka ce wai baka san yan da zaka datse alak'ar tasu ba" D'agowa yae ranshi ba dad'i, xuciyarsa tamkar zata fasa k'irjinsa tayo waje yace
"Kece kike amfani da ita bani ba, tun faruwar al'amarin nan roqon meye ban miki ba akan ki sake kuruwar yaron nan? Ya kamata kisani nifa ba yaronki bane ba, banida kuma almakashin datse wannan alak'ar kece kike dashi, keda kima dasa alak'ar tasu tun suna jinjiraye"
Cikin baqin ciki tabishi da kallo
"Amma ba haka mukai dakai ba, wannan aikin tare muka faroshi kuma da sanya hanmun 'yarka da ita akayi komai ko kanaso ko bakaso, idan ma so kake lallai seka had'a aure a tsakaninsu ka sani zan fasa k'wai kowama ya huta" Yanzukam idan shi yayi ja jajir
"Bazan miki uzuri ba kika sako Ummaty acikin maganar nan, kece kika turata kece zaki warware komai, yanzu yara sunyi shak'uwar dabazasu iya rabuwa ba shine zaki tayarmun da hankali" A yamutse ta kallesa
"Da gasken kake mafarkin had'asu aure kake kenan, kasan Allah wlhy tsaf zan b'atar da Ummatyn inga k'arshen iskancinka" Mik'ewa yae daga zaman dayake ya bugi babbar rigarsa
"Ga fili gamai doki, wacce bata tsoron Allah kawai" yae ficewar sa,Koda ya fito hanyar fita yayi gidan gabaki daya saboda tsananin bacin ran da ya tsinci kansa....

ESTÁS LEYENDO
ZAINUL ABIDEEN
EspiritualBanida wani burin daya wuce Inga gawar zainul abideen akwance babban kudirina a duniya shine in bude idona Inga zainul abideen akwance baya numfashi inhar be mutuba kuwa bazan taba daina bibiyarsaba har saina tabbatar da na maidashi ga Rai babu amfa...