7

535 27 1
                                    

*HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

 
     *SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*

2255398727 zenith Bank
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 07042277401

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

07042277401

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

                   *7*
Kwance take idanuwanta a lumshe tamkar wadda take bacci Amma ba baccin takeyi ba ,minti minti takan juya kwanciyarta saboda gajiya da takeyi kwanciya gefe daya ga bacci yaki daukanta ko kadan,hakan Nan ta bude lumsassun idanuwanta kurriii a kan fankar dakin dake juyawa a hankali,meke damunta yau ne?bacci yayi kaura a idanuwanta?...ko wani Hali ya zainul abideen ke ciki oho?dikda yau ne Rana ta farko da ta kwana a cikin gidan nasu Amma tanada bukatar sanin halin da yake ciki yanzun,dago kanta tayi ta dubi agogo karfe daya da minti goma Sha biyar na dare sai kawai ta maida kanta pillow ta tsunduma cikin kogin tunani,dik tunaninta be wuce akan yadda zainul abideen zai samu lafiya bane?ta auna ta juya dik yadda tai tunanin sai taga babu mafita, mafita guda daya ce shine iyayensa su amince su nema Masa maganin gargajiya ko zai samu lafiya Amma abun ya faskara,kwata kwata basuda raayi akan hakan babu ma maganar zuwa gun Mai magani sai maganar likita,kullum narkar da naira akeyi Amma kullum jiya iyau,hakan besa sunyi tunani akam lamarin su kamo bakin zaren ba,to ita ta Yaya zata tunkari wanan ciwon na zainul gashi tana bashi magani a boye Amma kullum jiya iyau,....sauke numfashi tayi ta gyara kwanciyarta Dole ta nemi mafita akansa Dan tabbas tana tsananin tausayin sa tanaso Shima ya samu lafiya kamar kowa...tayi nisa a cikin kogin tunani ta dau tsawon lokaci Mai yawa tana tunani har bacci barawo ya saceta batare da ta tsaida shawara a zuciyarta ba....

*******
Washe gari ta shirya tsaf ta maida kayan jikinta da hijjabinta tana zaune a parlor dik ta takura ta kosa ta Shiga inda zainul yake taga ya ya kwana,...dago Kai gimbiya bilkisu tayi ta dubi ummaty "ah ah ummaty ya kika maida kayan jiya?bayan nace fiyya tabaki kayanta kala daya kisanya tunda jikinku daya ko Baki Bata bane fiyya?ta juyo da dubanta inda fiyya ke zaune tana kaeyawa da karamar kanwarsu afee,

"Na ajiye Mata a kan gado ammiey Kuma na fada mata ga kaya Nan,kawai dai kinsan ummaty Bata sakin jiki da mutane batada sabo"

"Tashi ki canja kayan jikinki ummaty"..babu musu ummaty ta Mike ta nufi dakin da suka kwana jiya dam ta canja kayan jikinta,...jimm kadan baafi minti goma ba ta fito sanye da kayan Amma ta maida hijabin jikinta,kallonta kawai ammiey tayi ta girgiza kanta tana murmushi yarinyar dabiunta masu kyau ne tun tana kankanuwarta ba karamin burgeta takeyi ba...

*********
"Wadanan sune files din zainul abideen na asibitin Nan gabaki daya Kuma dukka sun kunshi dik wani treatment da akeyi Masa Kama daga ranan daya fara zuwa har yanzun da muke magana ranka ya Dade,Kuma dik wani treatment Yana ciki na  magungunansa da testes da akeyi Masa da gwaje gwaje komi da komi ranka ya Dade babu inda bamu gwada ba a jikin yarima,dik wata gaba ta sadarwa mun bimciketa Amma sakamakon guda da'ya ne komi lafiya Lau yake sawa"numfashi Mai martaba ya sauke hade da gyaran murya,

"Yanzun likita babu abinda zaa iya yi mishi bayan haka?bincike nakeso sosai ayi mishi likita ko zamu gano ciwon dake damun d'ana shine kadai da namiji da Allah ya bani ya Sanya mun soyayyarsa a cikin zuciyarta nakeji zan iya salwantar da duka dukiyar Dana mallaka inhar zainul abideen zai warke ya hau gadon sarauta"

ZAINUL ABIDEENOnde histórias criam vida. Descubra agora