8

517 30 2
                                    

*HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

 
     *SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*

2255398727 zenith Bank
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 07042277401

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

07042277401

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

                   *8*

Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da gamsuwa da shawarar da zuciyarta ke Bata dikda Bata bada karfi akan hakan ba Amma tabbas akwai haske ga wanan shawarar,
   Kallon gefensa tayi sai sharar baccinsa yakeyi Yana sauke numfashi a hankali dik ya fada a fuskarsa cikin Yan awanni ya canja gabaki daya,fuskar Nan ta Kara fari tasss hancinsa ya fito zir tamkar balarabe gashin girarsa kwance lufff,lumshe idanuwanta tayi ta bude "Allah ya baka lafiya ya zainul ya kawo karshen wahalar Nan...

********
  Washe gari yau jiki da jini ummaty ta tashi da ciwon Kai tun dare take fama dashi irin ciwon kan Nan na gefe daya har safiya ko kanta Bata iya dagawa,shiru shiru innah bataga fitowar ummaty tunda suka hadu da asuba a wajen alwala tayi tashiga daki Bata ganta ba har karfe Tara da wani Abu na safiya,mikewa tayi daga zaunen da take a kofar daki inda suka Saba Zama suyi Karin safe ta nufi kofar dakin ummaty,labulen dakin ta da'ga da sallamarta ta Shiga kasantuwar ko Ina a rufe sai dakin yayi duhu Amma tana iya hangenta lullube akan katifarta,a hankali ta karasa ta xauna gefen katifar ta Kira sunanta,"ummaty lafiya dai ko?tun safe Banga fitowarki ba balle ki karya kitafi gidan Mai martaba"

"Kai na ke ciwo gefe daya innah tun Daren jiya haka na kwana yanzun ma na tashi dashi ko iya daga kaina banayi"

"Assha subhanalillahi,shine kikai shiru kika kasa fadamin ummaty?kika kwanta a daki?a haka Zaki samu lafiya?ai Dole sai da magani ko?yanzun tashi Kisha kunu ga kosai can malam ya siyo kafin ya fita,ni Bari inje chemist din bawa insiyo Miki magani ko?"dakyar ta yunkura ta xauna ta bude idanuwanta da sukai jajir daka kalleta kasan batada lafiya tace "toh innah"

"Yau a hakura da zuwa gidan Mai martaba tunda Kinga bakida lafiya ko?komi sai da lafiya akeyi"gyada Mata Kai kawai tayi batare da tace komiba ta Mike ta je jikin drawer ta dau brush dinta Tai hanyar fita...itama innah mikewa tayi ta zura hijjabinta ta fice,

*******
  Mai martaba na saman kujerarsa a zaune gefe da gefensa matansa ne sunsha ado da kwalliya da tsadaddun laces irin na alfarma ko wacce sanye take da Dan kunne da abun wuya na zinari da kambu na zinari a hannayensu sunyi matukar kyau Dan dukkansu ba baya bane wajen iyau musamman gimbiya bilkisu da ta kasance amarya Kuma Mai kananan shekaru sanan ga kyau irin na usulin hausa Fulani idanuwan Nan farare tassss da jerarrun hakora farare,itama gimbiya rumana ba bayaba wajen kyau,katton plate ne da fruits cike a ciki danginsu apple,ayaba,kankana,da abarba dik an yayyankasu .gyaran murya Mai martaba yayi,

"Na taraku ne a Nan wajen Dan in tattauna daku dangane da ciwon yaron Nan zainul abideen,abun kullum gaba yakeyi,sanan mutane sunata maganganu akan cewar tunda har yakai wanan shekarun ciwonsa ba na asibiti bane na gargajiya ne shine nakeso inji shawarar iyayensa "murmushi kadan gimbiya bilkisu tayi ta dubi rumana tace "kece uwarsa ai ke yakamata kice wani Abu ni banida abin cewa dangane da ciwon Nan na zainul"

Ajiyar zuciya gimbiya rumana tayi "ya kamata muyi hakuri da kaddarar data fadowa magajin sarki mu fawwalawa Allah lamarin ba zancen mutane ko shawarar mutane zamubi ba,yawanci mutane da kuke gani macuta ne,abinda yasa suke wadanan maganganun be wuci Dan sunji ubansa sarki bane akeso ayi amfani da wanan damar a cucemu,bama kudin da zamu kashe bane damuwa face tsoron garin nema Masa magani a janyo Masa wani cutar,ni gaskiya ban amince a Mika d'ana wajen wani me magani ba,idan hakan akeji me zai Hana a canja mishi wani asibitin Mai martaba?idan wadanan sun kasa aikinsu"ta karashe  maganar cike da damuwa idanuwanta na kawo ruwa,....tausayi sosai tabawa Mai martaba yadda ta dauki son duniya ta dorawa zainul abideen tamkar ita ta haifeshi,"shikenan uwar maganin sarki dik yadda kikeso hakan zaayi insha allahu zansa a bimcikamun asibitin da yafi wanan din sai mu kaishi mu gwada muga abinda Allah zaiyi koh?"jinjina Kai gimbiya bilkisu tayi batare da tace komiba Banda murmushi da tayi Dan ita dama akwai sarauta..

ZAINUL ABIDEENOù les histoires vivent. Découvrez maintenant