10

634 36 3
                                    

*HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

 
     *SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*


2255398727zenith bank
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 07042277401

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

07042277401

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

                   *10*

********
"Ya zainul Wai menayi maka ne yau tunda Nazo kake shareni bakason kulanu?ta tunzuro Baki gaba idanuwanta cike da Yar kwalla tana kallonsa,...Shima idanuwansa akanta suke ko kiftawa bayayi yafi minti biyar a haka sanan ya kauda Kansa gefe batare da yace komiba,
Hawayen dake makale cikin idanuwanta ne suka sulalo a fuskarta zuciyarta na harbawa sauri da sauri tsoro falll zuciyarta,batasan laifin da tayi Masa ba tunda tazo yau yaki sakar Mata fuska suyi hira yadda suka saba,Kuma a iya saninta lafiya kalau suka rabu jiya hasalima bacci yakeyi batasan tafiyarsa ba,shin kodai Mai martaba yayi fada akan abinda tasa mishi a kunne ne na karatun kur'ani?har Shima bayaso yasa yake Sha Mata kamshi yau,dikda cewar tasan halinsa Sarai be cika son magana ba miskili ne ajin farko sanan dikda ciwon da yakeyi baya hanasa sarautarsa ta motsa ya rinka magana sama sama kamar bayasonyi,...idan har laifin da tayi jiya ne to tabbas zata daina kunna Masa Kuma insha allahu zata dauke mp3 din ma ta wuce gida da ita.

Murya na rawa ta Kara dubansa "ya zainul kafadamun menayi maka yau kaki kulani wallahi hankalina ya matukar tashi ya zainul kaji?na Bata maka Raine?idan na Mata maka Rai kayi hakuri bazan sake ba"Tai maganar tana shasshekar kuka,kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa a dishe
"Ummaty babu abinda na tsana a rayuwata sama da injuya gefen dama da haguna bangankiba,banji motsinki ba sanan Banga ko inuwarki a kusa Dani ba,tun bayan tashina jiya da yamma bangankiba zuciyata bataimun Dadi ba,naso ace Naga tafiyarki munyi sallama dake shine zaisamun salama da kwanciyar hankali"share hawayenta tayi ta sauke sassanyar ajiyar zuciya,
"Kayi hakuri ya zainul kasan yanayin tafiyar tawa,da yamma tayi nake haramar tafiya gida kafin magriba ta riskeni Akan hanya,da Naga kana bacci shine kawai banyi yunkurin tashinka ba na kimtsa natafi kawai kayi hakuri daga yanzun ko dare zankai inhar kana bacci bazan tafi inbarkaba batare da munyi sallama ba"

"Yanzun wanan hawayen na menene kikeyi?umm?

Turo Baki tayi "ba Kai bane tunda Nazo kaki kulani sai dauremun fuska kakeyi?Kuma fa da har naji tsoro nafara tunanin kila kadaina kula ni ne"

"Komi girman laifin da zakiyi ummaty baxaki tabayin laifin da ni zainul abideen zan kasa bude Baki inyi Miki magana ba,bazan jure ba bazan iyaba,bana tunanin akwai wanan ranar a rayuwata Koda kuwa kinyimun babban zunubin da ya dace ingujeki infita hanyarki,Amma bazan iyaba....shin tayaya ma zaayi nakasasshe kamar ni ingujeki ummaty?dik fadin duniyar Nan bayan iyayena yanzun Kam banida tamkarki ummaty...babban tashin hankali bai wuce idan na tuna watarana Zaki aure kibarni ba a cikin wanan halin ,nakan tsinci kaina cikin tsananin takaici da bakin ciki,duniyata takanyi mun duhu komi bana iya gani bana iyaji,dikda nasan wanan ranan tana zuwa,Amma burina be wuce inhar ban warkeba zuwa lokacin to Allah yasa in mutu in huta..."

"Shhhhh ya zainul banason Jin wanan kalmar daga bakinka karkasake fadamun irinta idan ba hakan ba Zanyi fushi Kuma Zanyi kuka"Tai maganar tana shagwabe fuska,

Murmushi yayi "banason hawayenki ya diga ko kadan ta dakililina Dan ban cancanci hawayen kyakkyawar budurwar yarinya kamarki ya zuba akan nakasasshe kamata ba,Niba kowa bane yanzun a wanan duniyar,dani da babu dik daya ne tunda babu wani Abu na amfani da nake amfanawa alummah sai ma wahala da nake Basu"sosai tausayinsa ya kamata ta matso daff dashi tasa bakinta daidai fuskarsa ta hura Masa iska ya lumshe idanuwansa ya budesu lokaci daya Yana kallonta,

ZAINUL ABIDEENWhere stories live. Discover now