4

637 38 0
                                    

*HASKE WRITERS ASSO....💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*

   *SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

                   *4*

Gefe ta nema ta raku'be zuciyarta Babu Dadi,kwata kwata batajin dadin yadda warisat takeyi Mata dik lokacin da zasu hadu sai ta bi ta da wanan kallon na wulakanci da kyama Amma hakanan take jurewa,

   Hajiya ce ke kallon zainul abideen Wanda shima idon Nasa akanta yake kallo daya zakayi mishi tausayinsa ya kamaka duba da yanayin nasa Amma hakan be hanashi murmushi ba dikda murmushin ba fita sosai yakeyi,ba itama murmushin ta maida Masa takai hannu ta shafa sumar kansa "ikon Allah sai kallo sannnu zainul Allah ya kawo karshen wanan rashin lafiyar taka ya baka lafiya magajin baba"

  Jinjina Mata Kai yayi "ameeen hajiya... Kaka"yadda yayi maganar bakinsa na furzar da miyau sai ya baka tausayi,...jin dadin maganar tasa yasa kakarsa sakin kayataccen murmushi Tana shafa sumar kansa,

  Daya bayan daya suke karasawa kusa dashi suna duba jikin nasa yayyinsa manya Mata guda uku sai kannin mahaifinsa Mata da iyalansu Suma suna dubashi cike da tausayawa,

  Hajiya ce ta dubi warisat da zahira dake gefe suna yatsina fuska tamkar sunji wari ta daure fuskarta "ku kunfi karfin kuzo ku duba jikin yayan naku ne kuna raku'be gefe daya?"

Tura Baki zahira tayi sanin halin kakar su Bata daukar raini yasa ita takaraso gaban gadon Tana magana Tana yatsina fuska ta gaisheshi Banda warisat da ko kallon gefen da suke batayiba ta maida kanta gefe,

A fusace mahaifiyarta ta dubeta "me kike nufi ne warisat?ke kinfi karfin ace kiyi Abu kiyi ko?hajiya Bata isa tace kiyi Abu kiyi ba kenan to karyarki yarinya kafin in bude idanuwana kinzo kin cika umarninta kafin in tattakaki"

  Murmushin takaici gimbiya rumana tayi tana karewa warisat kallo Sanan ta dubi mahaifiyarta tace"hajiya kubra kibita a hankali yarinya ce"...

  Dakyar warisat ta Tako gaban gadon Tana Harare Harare ta tsaya ta wani bishi da mugun kallo ta kauda kai Tai Masa ya jiki sama sama ta juya Tana wani irin taku,kallo zainul ya bita dashi ya rufe idanuwansa gammn....

  Sun dauki lokaci a sashin na zainul sanan suka fito a waje sukai Karo da ummaty tsugunne,

  "Allah sarki yarinyar kirki Allah yayi Miki albarka yasa ki Gama da duniya lafiya yadda kike kokari da zainul kinji?"cewar hajiya kakar zainul,
Murmushi ummaty tayi ta sadda kanta kasa,
.
  Tabe baki warisat tayi "kwadayi ne kawai irin na yaran talakawa shiyasa ta manne"...kowa yaji abinda tace Amma suka basar sukai gaba ummaty tabi bayansu da kallo,ta Dade tsugunne sanan ta Mike jiki a sanyaye tayi hanyar Shiga wajen zainul

*********
"Banji dadin abinda kikayi ba warisa,wanan abun da kikayi kika nuna kyamar dan uwanki a cikin mutane kin Saida mutuncinki ne a idon kowa kina tunanin iyayensa zasuji dadin abinda kikayi?koko Mai martaba idan yaji labari zaiji dadin abinda kikayi warisah?"

  Turo baki tayi batare da tace komiba yadda uwar ke zazzaga Mata masifa tamkar zata daketa,

  "Haba momy nifa ba kyamarsa nakeyi ba"

  "Ubanki kikeyi ba kyamarsa ba?Ina ganin take taken ki kema bakifi karfin Allah ya maidake haka yadda kika ganshiba, wanan yaron da kike gani yafiki gata a wajen kowa a dangi Dan dai Allah yayoshi Haka ne Dan Haka kibi a hankali shashasha kawai"

  Tana gama fadin haka ta wuce tabarta Nan zaune Tana ture turen Baki,

  Wata baiwace hannunta dauke da tray tazo wucewa ta karamin parlorn ta Dan durkusa ta gaida warisa wadda ke zaune kafarta daya Kan daya harta wuce ta Kira sunanta a wulakance "ke sadiya zo Nan"da sauri ta zube a gabanta

ZAINUL ABIDEENTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang