*HASKE WRITERS ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33**Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*
2255398727 zenith Bank
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 07042277401Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number
07042277401
Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.
*9*
********
Kwance suke su biyu kan makeken gadon dakin zahira da warisah gefe fiyya ce zaune kan kujerar hannunta rike da wayarta tana latse latse hankalinta na kan wayar,...shiru dakin babu me yiwa Dan uwansa magana kusan dama fiyya da warisah ba shiri sukeyi sosai ba ko wacce ji da kanta takeyi da sarauta musamman warisah da idan bakasaniba sai ka dauka cewa itace Yar sarki,Dan tsaki warisah taja tai jifa da story book din dake hannunta ganin wayarta na haske,."lafiya dai kikejan tsaki haka?"
"Wanan Dan anacen ne yayanki zai dameni da Kira,yakira yakira ban daukaba Yana Kara kirana nifa ban fiyeson damuwa ba zahira kinsani ki fada mishi"mtsww taja dogon tsaki,"nikam warisah Wai me kike takama dashi ne haka?kikewa ya musaddik wulakanci?ba kyau kika fishi ba fa ballantana kice Zaki wulakantasa ba Kuma asali kika fishiba Dan asalinku daya yadda kike takama da mulki haka Shima hakan ,kawai dai soyayya gamon jini ce yasa ya nacce Miki ai ga Yan Mata Nan a family da yawa da be nemesu ba?ni ya fiyya ma naso ya nema"ta karashe maganar cike da haushin warisah,
"Kanki akeji,da kinsani kice ya nemi fiyyar Mana ya daina nacemun haka,ni dik ya takurani wallahi so yakeyi yazo Amma Wai beson zuwa Nan Dan kada Mai martaba ya fahimci akwai soyayya tsakaninmu ace ai Mana aure da wuri Wai ya kosa in dawo gidanmu,besan Nima a takure nake da Nan din ba kamar nazo prison wallahi,gashi bacci ya gagari mutum saboda numfashin wancen mutumin na daki ya isheni"
A hassale fiyya ta dago kanta wadda tunda suka soma hirarsu Bata bi ta kansu ba sai yanzun da warisah Tai wanan furucin "karki kuskura idan kina rashin kunyarki kice Zaki sako ya zainul ciki Dan shi ba saanki bane Kuma karki fara kice Zaki aibantashi Dan zan wulakantaki"
"Ni kike cewa Zaki wulakanta saboda yayanki nakasasshe?"a hassale safiyya ta Mike ta sharara Mata Mari Karo na farko tana nunata da yatsa "ki Shiga taitayinki warisah dik take takenki Ina kallonki ne Ina kyaleki tunda kikazo gidan Nan Amma kada kice Zaki Shiga gonar Dan uwana nafada Miki tunda bakida mutunci ko wanine kikaji Yana zaginsa ke ba me tare Masa bace?Amma har ki iya bude Baki ki aibantasa to kulll ya tsaya daganan ai Shima ba yin Kansa bane,Kuma insha allahu sai kinyi danasanin abinda kika fada sai kinzo da Kanki kina Neman ya kalli inda kike ma balle ya kulaki da izinin Allah"
"Saidai in a mafarki ne zanzo in nemi kulawar tasa ko kuwa warkewar tasa Kuma wallahi sai kinsan kin mare ni"
"Idan kece ke bada lafiyar saiki hanasa lafiyar Mara mutunci kawai,kizo har gidansu kina ci Masa fuska ko da yake gado kikai indai rashin tarbiyya ce da rashin mutunci"zuwa yanzun warisah ranta ya Gama baci wato ita fiyya ta kalla ta kirata da dangin marasa mutunci?su waye Mara mutuncin kenan?uwarta data kasance jinin Mai martaba kanwarsa uwa daya uba daya ko kuwa mahaifinta da ya kasance attajirin gaske Shima Kuma jinin sarauta?,Bata Gama tunani ba afnan ta shigo dakin tana binsu da kallo daya bayan daya sanan ta dubi safiyya tace "anty fiyya kizo Wai su ya Zahra sunzo Kuma ammiey taji Kuna hayaniya"tana Gama fadin haka ta juya Tai waje abinta cike da natsuwa,

YOU ARE READING
ZAINUL ABIDEEN
SpiritualBanida wani burin daya wuce Inga gawar zainul abideen akwance babban kudirina a duniya shine in bude idona Inga zainul abideen akwance baya numfashi inhar be mutuba kuwa bazan taba daina bibiyarsaba har saina tabbatar da na maidashi ga Rai babu amfa...