6

668 36 1
                                    

*HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

 
     *SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*

2255398727 zenith Bank
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 07042277401

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

07042277401

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

                   *6*

Idan har na bari matar Nan taci galaba Akaina nayi babbar asara,idan har ban amsa mata bukatar ta ba to tabbas abinda tace zatayi nasan zatayishi dan ba cikakken imani gareta ba zata iyayin komi Dan ganin ta tarwatsamum sauran farin cikina,

  Nisawa yayi ya sauke ajiyar zuciya ya Dan dubeta,..."ka shiryawa bukatata ko har yanzun kana ko kwanto akan hakan?"ta jefa Masa tambaya tare da kafesa da idanuwanta Babu annuri a fuskarta,

  Kad'a kansa ya shigayi Yana murmushin takaici "Dole in amsa dik wata bukata taki tunda tun farko kin rigada kin jefani cikin masidar da fitarta yanada matukar wuya a gareni,zan aikata dik abinda kikeso Amma kisani badan zuciyata naso ba sai Dan kin tursasani da yin haka,Fadi bukatarki Ina sauraronki"

Kayataccen murmushi ta sauke hade da yin kasa da murya cikin lallashi ta soma magana,"sarkin dawaki abubuwan da nakeso ya zamana zainul abideen ya kasance cikinsu har yanzun burina bai Gama cika ba sarkin dawaki,naso ace zainul abideen bayaji,baya gani sanan baya iya magana ganobin jikinsa da yake motsa su lokaci lokaci ya zamana Suma basa motsawa ya zamto ga Rai Amma Babu amfani bana bukatar ganin farin ciki wajen iyayen zainul ko kadan nafiso ganin dansu a wanan halin su dawwama cikin bakin ciki na harabada"

  Tunda ta soma magana yake bin ta da kallo da tsananin mamaki da rashin imani irin nata,tunawa da yadda zainul abideen yake Amma dikda hakan beyi mataba tafiso ta gansa a nakastat da tafi haka,dakyatya hadiye wani mugun miyau ya kalleta idanuwansa jajir yaga itama shi take kallo,karantar yanayinta yasashi fasa fadin abinda yayi niyya sai kawai ya furzar da iska mai zafin gaske yace "Fadi bukatarki daidai nake da inyi yadda kika umarceni Dan a halin yanzun banida maraba da Zama bawanki"

  Can kasa ta sassauta muryarta Babu Wanda ke iyajin abinda take fada sai shi da ya ke sauraronta har ta Kai Aya a zancenta,a firgice ya dago Yana dubanta da tsananin mamaki da tsoro sai kawai ta gyada Masa Kai Tana fadin "zaa kawo aikin Kuma ummaty nakeso ta aiwatar da komi yadda ya dace yadda na fada maka mistake daya zaai wajen aiwatarwa komi zai lalace Zanyi asarar makudan kudin Dana kashe wajen yin wanan abun Dan haka ka kiyaye sanan ayi yadda nakeso rashin biyan bukatata tamkar rasa farin cikinka ne sarkin dawaki"...a gadarance ta karasa maganar,zufa ce take karyo Masa ta ko Ina Babu abinda yake ambata a ransa sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun....hakan yanaji Yana gani tai ficewarta ta barshi Nan zaune kamar mutum mutumi hotiho...

********
Zaune take a parlor hannunta rike da remote kanta Babu Dan kwali gashin kanta ya Sha gyara tayi matukar kyau,hankalinta gabaki daya Yana kan tv lokacin da taji sallama a parlorn da kyar ta maida dubanta ga bakin kofa sukai Ido biyu da zahira sai Kuma ta dauke Kai kamar bazatayi magana ba,

"Nifa tsiyata dake mugun Jin Kai tamkar wata sarauniya haka kikejin kamki warisat,yanzun idan ba iskamci ba ki juyo ki kallemu nida Yaya musaddik ki wani juyar da kanki gefe kamar Kinga Kashi"ta karasa maganar suna shigowa cikin parlorn,

ZAINUL ABIDEENOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz